Sashe 288
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da bakinta . ammi mike tana yi mata sallama , ak ya rufa mata baya ya shiga mota itama tashiga ta zauna direba yajasu suka bar gidan. kai tsaye gidan'su ammi suka zarce , d'akin ammi suka wuce ya nemi guri ya zauna yana fidda numfashi shi kad'ai yasan yadda yake jin zuciyarsa alokacin daya daura idanunsa akanta ji yayi kmr ya tashi ya rungumeta ajikinsa. dubansa ammi tayi a kaikaice sannan tace "ko zaka koma ne ka d'auko ya'yanka, naga duk kayi wani iri? " wani irin harababben son yayane hk? "inda Allah bai baka yaran ba yaya zakayi? "hakuri ammi zanyi nasan Allah bai bani amman yanzu danasan dadinsu bana kaunar abinda zai nisanta ni dasu ,duk da wallahi ba akansu bane kikagani haka. "kai kasani wallahi idan kasake jajjabowa kanka wata maseefar babu ruwana sai dai takare akanka, bazan sake zuwa maka bikon mata wannan shine na farko da karshe "ammi kiyi hkr Inshaallahu babu abinda zai sake faruwa atsakaninmu, naga kun gama komai but banji kunyi mgnr yaushe zata dawo .. "ok shima nice zan maka yakin dawowarta ? ya d'age mata girasa yana kashe mata idonsa daya yana murmushin. "aiko zaka zauna hka bata dawo gareka ba. "dan ammi nah karki min hk pl ..ki taimaka kikarasa ladanki ki dawo min daita da kanki nasan kina mata mgn zata dawo plz. "abinda kuwa bazanyi ba kenan ka ajiye girman kai kaje ka rarraso abarka shine magana, idan kace girman kai zakayi wallahi babu hanu kaga dai yadda dadynka yaki zuwa. "naji zanje " karmakaje ruwanka nagama me wuyar ,sannan shima taufeek ka shirya idan ya dawo kaje kabashi hakuri idan kagadama.. tana karasa fadar hk tayi gaba abinta, ya runtse mayatattun idanunsa yana sauraron zuciyarsa dake bugawa akan matarsa gbdy yayi sorronder sai yadda tayi dashi . bayan zuwansu ammi da kwana uku prof taufeek ya dawo daga tafiyar dayayi zuwa Thailand shi da madam shema inda ya barota zata wuce koria. umma ta tarbeshi cike da matsanancin kulawa sannan ta amshi jakar daya shigo daita xuwa d'akinsa ta had'a masa ruwan wanka sannan tabashir yayi wanka. byn kmr minti talatin ta sake dawo wa tana daga labulen d'akin ta hangoshi zaune akan gado sanye da jallabiya coffe colour ,da alamun har yayi wanka takarasa shiga cikin d'akin da sauri ta ajiye tiren data shigo dashi tasoma tsiyaya masa coffee cikin cup dan tasan shi zai fara bukata, ta mika masa ya dubeta kafin ya amsa yana murmushi yace "nagode sannu da kokari sannan ya amsa ya kur'bi coffee yayi masa kur'ba uku ya mika mata ta ajiye "abinci fa? "sai zuwa anjima ganin hk yasa , ta fara masa magana cikin laulausar lafazi "yakamata zuwa yanzu ace yarinyar nan takoma d'akinta duba ga yanayin yaron ,yashiga damuwa dayawa akoda yaushe hakuri shine jigon komai a rayuwar duniya . "duk naji bayaninki yabaki hakuri? "eh yabani kuma da ala'mun yayi nadama " "yabaki hakuri yayi nadama kin hakura, duk bashi ba saboda ni ban hakura ba ,sai ya tako da kansa yabani hakuri ai yatace dana yi silar zuwan duniya ba a caca na cuyota ba, sannan kai tsaye baza meida masa ita batare sun fuskanci juna ba ,sabod yin hkn akwai hatsari . "kai dai kace kana goyon bayan diyarka ne kawai "duk abinda zakice daidai ne muddin akan wannan matsalar ce, tayi murmushi tana kokarin bude masa kular abinci.. bayan kwana biyu da dawowar taufeek ak ya shirya domin bawa sirinkisa hakuri, bakinsa d'auke da sallama ya isa parlour'n da aka yi masa izinin shigaz prof na zaune yana shan coffe gefe guda kuma farhan da ihsan ne zaune suna zuba masa surutu ya amsa masa sallama yaran naganinsa suka kwasa aguje sukayi gurinsa suna murna "granpa dadynmu yazo ..." ya d'auki ihsan ya rungumeta, ahankali yakarasa ya durkusa har kasa "ya gida... yayi shiru ya kasa karasa saboda bai san da wani suna zai kirasa ba matsayin me gidansa ko surikinsa ko kuwa babansa, yana wanan tunani zuciyarsa tayi saurin furta "ya gida dady ?karo na farko daya kira wani da wannan sunan bayan mahaifinsa cikin fara'a prof ya amsa "a a son kaine yau agidanmu? sunkuyar da kansa yayi k'asa ala'mun jin kunya da rashin gsky yana tsosa keyarsa byn yace "eh wallahi dady nine "prof yayi murmushi saboda yasan abinda ke tafe dashi arana kuwa cewa yayi " yaga uwar bari . shiru ya ratsa parlour bakajin motsin komai sai na hayaniyar ihsan da farhan da suke guje guje basu gurin kankansu barsu gurin ubansa, can dady ya d'ago ya tsura masa ido sannan yace "son ina fatan dai lfy ko akwai abinda kake bukata daga gareni? ak shafa keyarsa ya cikin yanayin kunya sannan ya fara magana "uhm dady nace ba. sai kuma yayi shiru "relaxe my son kwantar da hankalinka ka min bayani ta yadda zan fahimce ina sauraronka "da kyar yasanyawa zuciyarsa natsuwa dan gbdy yagama daburcewa agaban sirikin nasa dan wani kwarjin na musamman yayi masa, duk wata rashin kunyarsa ya nemata yarasa ahalin dayake yanxu agabansa yana jin kmr k'asa ta tsage yashige tsabar kunya, kusan minti goma sannan ya fara magana atsanake "daman dady nazo ne nabaka hakuri akan abinda ya faru wallahi nayi nadama dan Allah kabawa su'ad hakuri har ummanta a sake bata hakuri ina bukatar matata ta dawo gareni yakarasa mgnr cikin yanayi na damuwa yana goge hawaye . prof ya sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ya fara magana "hakika abdul ka aikata kuskure babba laifi wanda nima sai da raina yabaci sosai amman babu komai komai ya wuce ka daina kuka Inshaallahu matarka zata dawo gareka wani irin dadi yaji ya mamaye zuciyarsa ya rungume yaransa yana jin dumin uwarsu atare dasu hatta sihirtaccen kamshi jikinta yana jiyowa daga jikinsu . bangaren su'ad ce dai sai ahankali dan ta hau dokin naki, anyi yin duniya daita ta komai taki ,babu wanda bai yi mata mgn ba amman tace "sam bata koma gidan abdulkabir ya sawake mata kawai, zaman da sukayi abaya Allah yasanya masa albarka ,rabuwarsu kuma Allah yasa hk shine mafi alkhari lokacin da musty yaje masa da zance hankalinsa yayi mugu mugun tashi saboda bai ta'ba expecting din zata iya hakura dashi ba. prof taufeek yayi kiranta zuwa parlour'n sa nasiha me ratsa jiki yayi da kwantar da hankali "kiyi hkr ki koma d'akinki ,duk wani mutunci d'iya mace bai wuce tana zaune d'akin mijinta ba,"mijikin yayi nadamar abinda yayi "ni kaina na sheida nadamarsa,ni mahaifinki ne ina baki umarni idan mijinki yazo gareki kiyi hkr ki rungume aurenki kuka take sosai lokacin daya mahaifinta yasoma magana har ya dasa aya hawaye bai bar zubo mata "ya ta iya da rayuwarta akansu ne take wannan fushin gashi gbdynsu sun sallama sun hakura dole itama tayi hakuri ta rungume kadddaran mijin da Allah ya had'ata dashi .. ya shirya da kansa zuwa bikon matarsa dan duk wannan abinda ya faru basu had'u da junansu ba tun ganin dayayi mata lokacin da sukaje tare da ammi bata sake kuskuren had'uwarsu ba ,ko yaje gidan ganin yaransa bata yarda suga juna har yagama abinda ya kawosa ya wuce . tana jin sautin hayaniyarsa da yaransa a a harabar gidan tayi saurin shigewa d'akinta daga inda take tana jin duk wainar da suke toyawa kusan awa daya yana tare dasu har ya mike zai wuce saboda rasa yadda zai yi yaganta ammaan yaji bazai iya tafiya ba batare da ya sanyata acikin idanunsa ba, ihsan ya tmby dan tafi farhan wayo "mamana ina momy'nminku take? "momy'n mu ta fad'i hk tana me kamo hannusa" muje na kai ka d'akinta zaune ya sameta abakin gado ta tallafi fuskarta da hannayenta duka gabansa ya bada wani sauti dam... da hanzarinsa ya karasa isa gurin datake zaune ta bala'in d'auke kanta kmr batasan da tsayuwarsa ba ya juyo yana kallon fuskar kyakkyawar diyarsa ,yarinyar a zuciarsa take bai sani ba kodan tafi kama da uwarta ne akan sauran yaran ,ya ja numfashi ahankali ya sauke ya tsugunan agaban yarinya "mamana jiki cigaba da wasanki kinji gani nan zuwa.. yarinyar tayi murmshi daya bayyana hakoronta da basu gama kwari ba tayi hanyar fita tana tsalle tsalle. ya juyo gareta yana kare mata kallo tayi wani azababben kyau wanda bai san yadda zai misaltawa masu karatu ba ,aransa yace "bata damu da nisantar juna da mukayi , ya dad'e akanta yana kallonta sannan ya bude bakinsa da kyar ya kira sunanta "hrt beat " tayi shiru batare da tace masa komai ba ya kuma maimata kiran sunanta nan bata tanka masa ba,hankalinsa ya sake kololuwar tashi tsam su'ad ta mike daga gurin datake zaune dan kusancinsu yayi yawa kuma tasan halinsa da wannan kusancin yake cin duk wata nasara akanta, tayi taku daya biyu zuwa uku taja ta tsaya game da juya masa baya. ak ya tsaya bayanta yana yi mata magana ahankali tamkar yana yi mata rad'a. "hrt beat kada kice zaki juya min baya ,dame kike son naji, da zuciyata koda me? ya birkitota gabansa gami da ware mata hannuwansa duka "kizo gareni dan Allah rayuwata bazata ta'ba kasancewa daidai ba sai dake ,tacigaba da kallonsa batare da ta motsa koda dan yatsan kafarta ba. ya kuma langwabe kai "haba hrt beat kizo na rungumeki konaji sanyi acikin kokon raina, zuciyata tana matukar yi min kuna rashinki bari na durkusa bis gwiwowina plz am very sorry for what I did wad'an kalaman nasa sunyi matukar ratsa zuciyarta hkn yasanya takowa tmkr wacce k'wai ya fashewa aciki ta fad'a kirjinsa tana kuka. ya mayar da hannunwasa duka ya rungumeta tsam akirjinsa tmkr wani zai kwace masa ita, wata doguwar ajiyar zuciya yayi. "ko ke fa? baki ji yadda nake jin wani sanyi yana ratsa min zuciya ba" ya dago fuskarta yana share mata hawaye. "ya isa kuka banason yawon kuka kina min hasarar hawayenki " kuka take sosai ,ta wani narke ajikinsa ta jima rungume a kirjinsa tana kuka da kyar yasamu ta daina kukan. "meyasa kayi kokarin son rabumu abdul ?ka daina wa ummata wani kallon dabashine ba, ka tayani mutunta mahaifiyata ina sonta sosai, ban had'a soyayyarta da kowa ba. murmushi yayi yana cizan lip's dinsa na kasa "am sorry baza mu ta'ba rabuwa