Sashe 153
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa? dan ya gano dalilin abinda yasa ammi take son korar masa yaro. "bakaga yadda ya tsare min yarinya da wadan mayun idanun nasa ba kmr zai cinyeta,? AK ya tabe baki yana sake watsawa su'ad idanunsa sannan yace "ta zauna ta ci abincinta babu ruwana daita dan banga abin kallo agunta ba. "nidai ka tashi ka wuce kawai ,bakayi kaura daga gidan nan bane me ke yawon kawoka yanzu? AK yayi murmushin takaici yana sakarwa su'ad harara sannan ya bude bakinsa da kyar "ta ya mutun da gidan ubansa bazai zo ba? dady kana jin fa abinda ammi take cewa kaima ka yarda kar naxo? "ina ai hkn ma ba me yiwu bane dole kullun yarona yakawo mana ziyara idan ke bakya so ganinsa ,ni ina kaunar ganinsa kullun . ganin da su'ad tayi mgnr ta dawo muhawara a tsakaninsu yasa ta sulale ta gudu daki . byn sun gama cin abinci ammi ta iske su'ad a dakinta zaune ta zabga tagumi dan batama san tashigo dakin ba ,har sai da ammi ta isa gareta ta cire hannunta data tokare habarta daita "banason yawon tunani mamana ....su'ad tayi firgigib ta dawo hayacinta tare da kallon ammi tana murmushin yake wanda yafi kuka ciwo. "banason wayon tunani, yawon tunani na haifar da cututttuka dayawa masu saurin na kasa jikin dan adam "idan wani abu yasameki bansan yadda zanyi ba? ke kadai kika rage min arayuwa ahalin yanzu ganinki ke dabemin kewar mahaifiyata da dan'uwana dana rasa ...murya cike da rauni su'ad tace "kiyi hkr ammi na daina nima hk kawai nake tsintar kaina cikin wannan tunanin. Allah yasa kin daina dan kullun hk kike cewa takarasa mgnr tare da shigewa bayi. kullun ammi sai ta jaraba kiran number malam me bada maganin farfadiya bata samu kasanceawar yana ghana ,duk da ance mata sai byn sati biyu zai dawo amman ta kasa hakuri kmr kullun data sabawa gwada kiran number bata shiga, hk ce ta faru yau cikin ikon Allah tana gwada kiran wayar taji yashiga cike da matsanancin murna ta zaku bai dauki kiran ba. kiran ya katse batare da an dauka ba ta sake gwada kiran a karo na biyu aka dauka "assalamu alaikum " daga dayan bangaren aka amsa mata da "wa'alaikimu salam" muryar malamin ce ta doki dodon kunneta wani irin murna da faricinki ya sake ruf ammi kmr anbata maganin farfajiyar ne. "malam nice wace nazo kan zance yarinyata me fama da cutar farfadiya kace lallai sai anxo daita sai km akayi rashin sa'a mun zo baka nan . "eh wlh tafiyar gaugauwa ce tasani zuwa ghana amman dazu da asuba na dawowa zaku iya xuwa .. wani sanyin dadi ya sake rufe ammi "nagode sosai malami gamu nan zuwa "Allah yabada iko karasowa inji cewar malamin. katse kiran ammi tayi tare da duban inda su'ad ke zaune ita da eiman suna hira wace rabin hirar eiman ce ke yi akan yadda aurensu zai kasance . "ammi tace mamana maza tashi ki shirya zamuje gurin malamin nan ya dawo tun ammi batakarasa mgnr ba su'ad ta mike tsaye tare da kwance mayafi jallabiyar dake sanye ajikinta wanda ta daurashi akanta ,ta warware tare da nade kanta dashi ta dauki daya daga cikin turarukan ammi ta fashe ilahirin jikinta dashi wajen ajiye takalma ta nufa ta dauki takalmi flat tasanyawa kafafunta ta juyo daidai ammi tagama shirinta sukayiwa eiman sallama suka wuce. ***** zaune suke gaban malami me tsoron Allah da son taimakawa bayin Allah, wannan malamin kowa ya sheidaishi akan cewar malami ne nagari me tsananin tsoron allah duk abinda wannan malamin za'i maka daga cikin alqurni me girma zai duba. " ko maganin gargajiya wanda alqurni yayi mgn akansu,bai dogara da komai ba sai da ayar Allah ya dagora . tunda akayi musu iso ga wannan malamin gaban su'ad ke faduwa banda kallonsa babu abinda take, alahakikanin gsky tana ganin kmr tasan fuskar dan fuskar malamin bazata taba bace mata ba a iya tsawon rayuwata. malamin ya numfasa byn yagama hada wasu magunguna cikin bakar leda ya mikawa wani mutu, kana ya meida hankalinsa sosai kansu ammi, ammi ta sake gaidashi ya amsa cike da sakin fuska "malam wannan itace diyar tawa me dauke da cutar farfadiya . malam ya sake numfasawa sannan yasoma mgn cikin hausarshi da batagama kwarewa ba "sannu yarinya ,su'ad ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta "tace yauwa ina yini .. " lfy ina son ki bani labarin abinda ya faru dake tun daga farko sbd ji yanayin labarinki yasa nace azo dake ,saboda mahaifiyarki ta min bayanin komai agame da yadda akayi ciwon ya dawo jikinki, amman nafi son naji daga bakinki kasancewar lokacin da mahaifiyarki tazo min da labarin yadda akayi ciwon yasameki yayi min tuni da wani labari wanda yazo daidai da irin naki . "dan hk bismilla ina sauraronki su'ad ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da sake sunkuyar da kanta kasa sosai sannan ta fara bawa malamin barinta tunda daga farko har karshe. lokacin da su'ad ta kai karshen labarin malamin yayi murmushi yana sake fuskantarta da kyau sbd tabbatarwar kansa babanshi ne yabata wannan maganin . numfasawa malamin yayi sannan "yace kinga wanda yabaki maganin farfadiyar nan da kikawa abdulkabir mahaifina ....... a matukar tsorace ammi ke dubansa wanda ita su'ad bataji wani tsoron komai ba , daman ita tun shigowarsu ta sanya ayar tmby akansa sbd tsantsar makanin dataga yayi mata da alhj tapa. "malamin yacigaba daman mahaifina yabani labarinki kafin ya rasu yace komai daren dadewa ko ke baki dawo ba wani naki zai dawo gareshi . "sannan mahaifina kafin ya rasu sai daya Shiryu yakoma zuwa ga Allah ya koma cikakken malamin addinin muslinci duk ya daina aikin shirka da tsubuce tsubuce sai da yayi tuba sosai tuba km irin wanda Allah yake so. mahaifina sai dayazama mutumin arziki sannan Allah ya dauki rayuwarsa " kafin ya rasu shi yagayamin duk abinda zanyi nayi sbd da Allah mahaifina ya bar mana wasiyyaha sosai domin kuwa sai daya tara duka ya'yansa yayi mana huduba gbdynyamu "yace Duk Wanda yayi shirka byn ransa Allah ya isa bai yafe masa ba . "yace mu shiga duniya muyita hajahadi mahaifinmu ya raba dukkanin ya'yansa zuwa garuruwa kasashe kasashe muje muyiwa muslinci da alummar annabi hidima sannan ya rasu. " mahaifina yace duk lokacin kuka dawo yabani sakon cewa makarin maganin tunda kema alokacin yace baki taba sanin da namiji ba wanda bansani ba ko zuwa yanzu kinsani cewar wanda bai taba kusantar ya mace arayuwarsa shi zai kwanta dake ta hanyar sunan ma'aiki saw. abinda ake nufi zayi auratayya aure dake sau bakwai acikin halin cutar farfadiyar ajikinki ,shine makarin wannan cuta ta farfadiya . take gaban ammi yashiga dukan tara tara da mgnr mlm sannan km jikinta ya dauki rawa babu abinda tasoma furtawa cikin ranta kmr kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi kadai take karantawa tana maimaitawa sbd tashin hankali dataji ya shigeta... ita kuwa su'ad kusan har tafi ammi shiga damuwa da tashin hankali wani abu taji ya gilma ta cikin idanunta jiri ne ko kuwa buguwar zuciya ne ta sameta daga zaune da take ita dai batasani ba sbd ji tayi kanta da gangar jikinta suna juyawa gbdy idanunta sun soma rufewa . malamin yacigaba km daman mahaifina yace wani mummunar bala'i sai ya fadawa yarinyar sbd tayi shirka tasabawa mahalincinta km duk wanda yayi shirka ya sabawa allah daman arayuwa sai yaga badaidai ba, idan yaci banza a duniya har yagama rayuwarsa ta duniya batare da ya tuba ba km allah baiyi masa komai ba, definitely idan yaje lahira sai ya hadu da mummunar sakamakon abinda ya aikata arayuwarsa ta duniya. sosai malamin yayi musu nasiha inda yake cewa su'ad wadan nan yan fashin da makamin da kika hadu dasu a wance ranar dazaki kai tukunyar tsafi har suka yi miki sharrin cewar da ke sukeyi fashi. bala'i da mahaifina yace zai sameki shine wannan haduwar da kika yi da yan fashin suka miki wannan sharri har kika fada bala'in da har kikaje kikayi gidan yari. idan zaki hankalta Allah yana sonki da rahma ne a lahira wanda yasa tun aranar farko da kika aikata shirka yasoma hukantaki tun a gidan duniya bisa ga laifinki . "yanzu abinda za'a yi hjy ki soma da tuntubar yarinyar idan har zuwa wannan lokacin bata taba kusantar "da" namiji ba arayuwarta . sai a nemo wanda shima bai san ya mace ba a daura musu aure... hankali ammi a idan yayi dubu to ya kai kololuwar gurin tashi, a matukar tsorace take agaban malam sai dai duk bayaninsa na shiga cikin kunnuwanta ," cike da raunin muryar "tace na saurari dukkanin bayanika na km gode kwarai da gaske malam Allah ya bar girma sai dai wani hanzarin ba gudu ba yanzu hk ita yarinyar jibi ne daurin aurenta sai dai daga ita yarinyar har mijin bani da tabbaci akansu "yanzu dole sai hkn ta faru sannan zata rabu da ciwon? " a'a wannan al'amari ne na ubangaji idan Allah yagadama zai iya warkar daita a duk sanda yaso ni dai abibda mahaifina yace nasanarmuku kenan duk randa yarinyar ta dawo. "ammi ta sake marairaice murya" allah gafarta mlm mijin da ita yarinyar zata su biyu zai aura arana "zai iya jinkirtawa har zuwa sanda zai aiwatar da komai akan ita wannan yarinyar ...." shikenan mlm nagode sosai yanzu nawa zamu bada kudin sadaka? "bana bukatar ko sisin ku ga wannan itacen maganin sassaken dinya ne, kinsa ciwon farfadiya lamarin iska ne , km iska basa kusantar sassaken dinya zata dinga wanka da wannan sassaken dinyar kullun har sai randa ya kare kuje Allah yabata lfy. "ameen mlm nagode nagode sosai . "ki godewa Allah domin kuwa shine abin godiya bisa ga dukkan komai zuwa wannan lokacin ammi ta jima da mikewa tsaye ,amman su'ad na nan zaune cikin wata duniyar tunanin me cike da sarkakiya jin bayanan mlm tun mgbrsa ta farko jin ya dauke ta daina jin komai sai bugun zuciyarta daya tsananta. da taimakon ammi su'ad tasamu ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa rawa suka bar gidan mlm suka nufo hanyar dawowarsu gidan tun akan hanya ammi takira layin ak "tace maza maza duk abinda