Sashe 225
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH YA MUSAWWIR THE FASHIONER OF SHAPES. page 73 suna gama fitowa daga cikin jirgi yayi gaba abunsa yabarta abaya ,tabiyo bayansa cikin hanzari har suka karaso inda motocin kafaninsa ke zaman jiran karasowarsu bai juya yaga a wani hali take ciki ba. direbansa na hangosa yayi saurin bude masa gidan baya yashiga ya zauna yana jin kmr ana zuba masa wuta ne agabadaya ilahirin ajikinsa Allah Allah yake ya isa yaga zeey dinsa, wannan shine Karo na sau ba adadi dayake ja tsaki yana shirin bawa direba umarni tada mota takaraso cikin sauri tashiga motar direba ya meida murfin mota ya rufe, yana ganin tashigowarta yayi saurin kawar da fuskarsa gefe dan baya kaunar kallon fuskarta, ta juyo ahankali ta saci kallon inda yake duk da bataga fuskarsa ba ,tasan ran nan nasa a hade yake tmkr wanda aka aikowa da sakon mutuwa har suka dauki express din da zai kaisu ikeja a long tsaki ya dinga ja yana jijiga kafarsa daya, hannusa daya km na saman cinyarsa yana shafawa ahankali . kai tsaye yabawa direba umarnin ya nufi gidansu zeey dashi ,su'ad ta juyo a firgice ta kalleshi zuciyarta na wani irin harbawa da karfi amman babu fuskar dazatayi magana haka yasa takoma ta kwanta jikin kujerar motar tana sauke numfashi sama sama take tashiga karanto addu'oin samun natsuwa cikin ranta. gudu direban yake sosai amman gbdy ak ganin yake tmkr ba gudu yakeyi ba ,dan haka yace"kule ka sake taka mota sosai , "sir ai karshe gudun motar kenan. minti goma kacal ta kawo su unguwarsu zeey, koda suka isa kofar gidansu zeey direba yayi parking a kofar gidan , ya fito cikin sauri ya nufi karamin get din gidan batare daya jira direban ya bude masa jikinsa na tsuma yashiga buga get da iyakacin karfinsa, me gadi yataso ya bude yana gaidashi cike da girmamawa, zai shiga cikin me gadi "yace ai babu kowa acikin gidan gabansa yaba rasssssss tare da zaro ido waje muryarsa na rawa yace "ina sukaje? me gadi yace "sun d'an jima basa gidan suna gidan alhaji Adam lumshe mayatattun idanunsa yayi bai sake cewa komai ba ya juya cikin sauri. ******** suna isa gidan ammi dake zaune a parlour ita da mahaifiyar zeey da eiman sai hannutu me aiki ta mike cike da murna ta tarbesu cikin farinciki ganinsu ta rungume su'ad ajikinta, jiki a sanyaye su'ad ta rumgumeta itama tana murnar sake ganinta . cikin tsananin farinciki ammi tace "shiyasa na dinga jina cikin yanayi biyu ashe diyata ce tafe sannu da zuwa . dumin jikin su'ad yasa ammi zareta daga jikinta tare da tsura mata ido sannan tace "Bakida lafiya ne naki jikinki kamar garwashin wuta? kai kawai su'ad ta iya daga mata batare da tace daita komai ba dan koda tace zatayi magana kuka ne zai biyo baya . kusan eiman tafi kowa murna dawowarsu ta janyo hannu su'ad suka shiga dakin ammi suna rungume da juna. shi kuwa ak sai baza idanu yake yaga ta inda zai ga zeey kawai yake amman bai ganta ba , ita kuwa zeey tunda taji dawowarsu tashige kuryar dakin da suke zaune da mahaifiyarta ta kulle kanta ta dinga tikar rawa tana dariya da murnar burinta zai cika, wahalarta tazo karshe zata samu abinda takeso muradin ranta ya dawo ta aiyana aranta bazata bari yasanyata acikin idanunsa ba har wahala gurin nemanta . takira kawarta bolaji tana gaya mata zance dawowar ak murna tayi sosai "gsky dole kiyi murna kawata wannan daukar hutu da kikayi batare da an yi miki savices me kyau ba, nasan gurin na can yayi giress ina nan zuwa gobe da lemun tsamina na wanke miki gurin tsab dan ak yaji dadin caccakarki, suka saka dariya atare . "wallahi bolaji bakida kirki to waya gaya miki tun wannan lokacin zaune nake ba harka? bolaji tace "wai da haka nayi tinani ganin mama bata barinki fita koina. "tab ai in gaya tunda muka dawo gidan na koma ruwa tsumdum nida akil dina muke cin duniyarmu babu tsinke . "allah kawata" "wallahi ke ko sherajiya mun hadu dashi a citedal hotel dake nan underbridge din dake kusa da gidan nan ai bazan iya zama babu harka ba ,ai naga kokarina ma danayi cikkaken wata uku babu harka . "gsky kinyi kokari sosai dan banyi tunanin zaki iya hakurin hakan ba a yadda nasanki kmr kura inji cewar bolaji tana kwashe mata dariya daga karshe suka zarce da hira batsa . shiru2 ak baiga fitowar zeey ba tun yana dauriya har yashiga bulayin nemanta, yashiga wannnan dainin ya fito yashiga wacan dakin ya fito yana hauka kiran sunanta wanda hakan yabawa duk wani wanda ke cikin gidan mamaki, kusan awani goma kenan da dawowarsu amman har zuwa wannan lokacin bai sanya zeey acikin kwayar idanunsa ba , wannan dalilin dayasa ya haukace musu agidan tausayinsa ne yakama maman zeey ta tashi da kanta tashiga daki inda zeey ke kwance cikin kuryar daki, ta kwankwasa kofar tana kiran sunanta "zainab zainab !! "waye? "nice dan Allah malama kixo ki bude min keda waye zaune a dakin dazakice waye mama takarasa mgnr tana jan tsaki. zeey dake kwance ta tashi ta bude mata kofar takoma ta kwanta abunta mama takaraso ta zauna kusa daita "ki tashi kije tun safe abdulkabir ke bulayin nemanki acikin gidan nan banga dalilin wannan wulakanci ba alhalin nasan abukace kike da ki koma gidansa "ni dai shawara zan baki wannan itace damarki ta karshe, kin dai san halinsa sarai ba sai nagaya miki ba. "nifa mama babu inda zani, wata nawa ni nayi ina hauka akansa amman yayi burus dani wallahi sai nima na gasa masa aya a hannu "nidai tashi kije kada uwarsa taji babu dadi aranta dan bakiga yadda hankalinta ya tashi ba. "naji mama zanje amman kafin na zan roki wata alfarma guda daya duk abinda zai biyo baya atsakanina da abdulkabir bana son kice komai matawar ba bayana zaki bi ba. mama ta tabe baki tana dubanta a dan atsorace saboda batasan dalilinta na fadar haka ba sannan tace "kinji shirmen banza ni dan Allah tashi kije karki karasa zautar min da yaro yana ya kusan haukacewa takarasa mgnr tana murmushi . "aikuwa yanzu muka fara wasan dan wallahi sai gidan nan sai yayi masa zafi ba dai takamarsa zafin kai ba sai na karya weekpoint dinsa sai na meidashi abin tausayi. "idan baki meidashi abun tausayi ba shi ya meidake zeey ta bude bakinta zatayi mgn kenan mama ta katseta "ni jeki dan Allah magangunki sun fara sani jin ciwon kai. zeey tashigo parlour'n tana yatsina fuska kamar taga kashi , shi kuwa yana ganinta ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da mikewa tsaye ya nufiota yana kokarin rungumarta ta tokare kirjinsa da yatsunta tana furta "lafiyarka malam daga ganin mutun zakayi cikinsa? ya marairaice murya " plz kiyi hkr karki hanani taba jikinki kefa matata ce. "may be ka fara hauka ko kuma kasha wani abu wanda yake kokarin taba k'walk'kaunarka ,idan ka manta na tuna maka ka dade da sakina har nayi idda nagama dan haka ka matsa min a hanya in sha iskar duniya. ta nufi kujera ta zauna tare da d'aura kafarta daya kan daya tana girgza jiki, shima yabiyo bayanta ya zauna kusa daita har cinyoyinsu na gugan juna ya riko tafin hannuta ciki nasa "dan Allah kiyi hakuri da abinda ya faru abaya yanzu ashirye nake danayi komai akanki ciki kuwa har meidake gidana. " kai kai dan allah malam rabani da wad'an nan zantuttukan naka masu sakani jin wani iri, ko ka meidani gidanka ko karka meidani daman dole zan koma gidanka tunda har karigada ka dawo kasar. ak yashiga girgiza mata kai sannan yace "what ever you want me to do i will do, gbdy ji nake idan bana tare dake kmr mutuwa zanyi, ki taimaka ki dawo gareni ayanzu . ammi da eiman dake zaune suna dan tautaunawa akan lamarinsa sukayi sakatoto suna kallonsu tmkr TV cike da matsanancin mamakin abinda ke faruwa agabansu. abun bai sake dagawa ammi hankali ba sai sanda taji yakamo hannun zeey "kinga tashi mu wuce gidanmu na meida aurenmu . zeey ta fixege hannuta cikin nasa a fusace tana mikewa tsaye tare da cewa "kana hauka ne abdul a wani garin mahaukatan ka tab'a ganin an yi haka? " kataba ganin idan miji ya sake matarsa har tsawon wata hudu ya meidata haka kai tsaye batare da an daura sabon aure ba? yayi saurin girgiza mata kai tare da cewa "gaskiya ba'ayin haka . "ok to idan ma ka soma hauka ne kayi saurin dawo da tinaninka ,sai an d'aura sabon auren zan iya komawa gidanka da sunan matarka ta juya tabarshi tsaye tana buga masa bombom dinta da suke baje a wa faratin batare da ta kalli inda ammi take zaune ba dan gabadaya yi tayi kmr batasan da wata halitta zaune agurin ba. yayi sauri biyo bayanta yana kiran sunanta tare da kokarin kamo hannuta taja ta tsaya tare da dakatar dashi "ina km zaka bini? "zan biki ciki ne mu kwana tare bazan iya kwana ni kadai batare da ke ba ,ta tabe baki "duk watanin nan da uwar wa kake kwana? yayi shiru yana kallonta batare da yace mata komai ba sai idanunsa daya tsura mata , "kaje ga matarka can ku kwana tare . "ina aibazan iya ba ko ra'bar inda take ma bazan yi ba asalima ni yanzu na tsani ganinta bana son d'aura idanuna akanta.. "wannan km matsalarka ce batawa ba idan ka gadama ka kasheta duk ba matsalata bace.. inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi ammi take furtawa acikin zuciyarta tana sake maimaitawa take km gefen kanta yayi wani irin mugun sara ta mike tsaye da kyar tashiga dakin dan eiman tuni ta rigata barin parlour'n bazata iya ganin takaici ba . tana shiga dakin taji sound din kukan su'ad sama sama bata tsaya tambayarta dalilin kukanta ba dan ta lura akwai babbar matsala dake shirin kunno kai cikin rayuwarta da mijinta, tunda gashi idanunta sunga komai, abubuwan da abdul ya dingayi da yanayin yadda su'ad din tashigo mata gidan yashiga dawo mata, kai tsaye ammi ta nufi bayi