← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 261 OF 289

Sashe 261

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* Dedicated To Hauwa A Usman Jiddar YA RAFI'U THE EXALTER page 82 .............tsoro da matsanancin firgici Ammi ta hango bayyane akan fuskar Umman Su'ad dake tsaye a gefenta jikinta na kirrrma, yayinda madam Shema ke tsugunne akan gangar jikin Taufeek tana girgizashi tana ihun kiran sunansa zuciyarta na tsananta bugawa kan abinda taga ya faru da mijinta. cike da matsanancin tashin hankali Umman Su'ad tashiga nunashi da yatsan hannuta zuciyarta na wani irin bugawa da k'arfi bakinta na rawa da illahirin gangar jikinta ta furta complete name dinsa cikin wani irin sark'akk'iyar muryar da ita kanta batasan tana da ita ba, "Tau...Taufeeq Abubakar Tafeeda gulun ........ "sai kuma numfashinta ya tsaya cak, yasoma barazanar d'aukewa cikin wani irin sanyin jiki tayi luuuuuuuu zata fad'i 'k'asa, cikin zafin nama Ammi tayi saurin tarota jikinta tana kiran sunanta Saleema Salema!!" " ki tashi dan Allah karku sa zuciyata ta buga.. amman ina Umman Su'ad ko ala'mun motsi batayi ba.. Gaba d'aya mafi kusancin' 'yan uwa ne suka taru akansu suna kallon Sir Mahbub wanda sukaji Salema takira da Taufeek a yanzu, da ita kanta Salemar dake zube jikin Ammi babu ala'mun numfashi atare da ita. kafin kace me take gaba d'aya hall din ya hargitse da hayaniyyar mutane kowa da abinda yake fad'a akan abinda ya faru ahalin yanzu, Musty ne ya duba yaga itama Umman Su'ad din suma tayi, dan haka cikin sauri ya fito da wayarsa cikin rawar jiki yashiga kiran number minister Mubarak wanda bai rigada yak'araso ba tukun. Cikin tashin hankali ya sanar dashi komai daya faru "cewa Minister yayi a yayyafa musu ruwa yanzu, yana kan hanya k'arasowa babu musu Musty ya fad'a musu abinda Minister ya fad'a masa, aka kawo ruwan roba aka shiga tsiyaya musu an dai yi sa'ar Salema ta farfad'o amman shi Taufeek ko ala'mun farfad'owa bai yi ba. Nan fa hankalin Shemah da Salema da ma Ammi gaba daya ya sake kololuwar tashi, inda Madam Shema ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta tana kurma ihu da kururuwa kiran sunansa" dan Allah mahbub ka tashi, ka tashi karka mutu kabarni kasan bani da kowa sai kai, "duk duniya kai kad'ai nake da, " dan Allah ka tashi karka mutu kabarni ..... yadda Madam Shemah ke ihun kuka haka salema ke rike da hannunsa tana wani irin marayan kuka me tab'a zuciya tare da kiran sunansa "Taufeek d'ina, ka tashi karka mutu karka sake barina a karo na biyu har sanda aka tattara gangar jikin Taufeek aka sakashi cikin mota direbansa ya fige motar aguje escort dinsa suka biyo bayan motar dayake ciki gudu kawai suke sharara kan titi. Kai tsaye Shemah tace "ayi babban asibinti dashi fadar haka keda wuya taji saukar murya Ammi cikin kunnenta inda take bawa direban umarnin yawuce dashi gidanta, haka kawai Shemah ta tsinci kanta da kasa mutsawa umarnin Ammi, dan haka kawai take jin zuciyarta na rawa tun sanda ta d'aura idanunta akanta ta tabbatarwa kanta lallai akwai wata alak'a me k'arfi atsakaninsu dan kamartasu ya baci .. "meyasa Mahbub ya firgita tare da suma akan yaga fuskar matar da batasan ko wacece ba, asalima yau ce rana ta farko data soma ganinta arayuwarta..? "to ko Mahbub d'inta ya dawo cikin duniyar tuninsa ne sakamakon ganin fuskar matar ? tashiga yiwa kanta tambaya kirjinta na cigaba da bugawa da k'arfi. "idan takasance ya dawo cikin tunaninsa kuma wannan, matar takasance matarsa ce alokacin ganinyar tunanisa, ya nata makomar rayuwar auren zai kasance..... ? ta sake jehowa 'kwakwalwar ta tambaya zuciyarta na sake dokawa da sauri sauri, "Allah kasa halakar yan'uwan takace kawai atsakaninsu ba aure ba ta tsinci kanta da fadar haka cikin k'asan ranta. yadda Madam Shemah take tunani da zance zuci haka Umman Su'ad ke zurfafa tunaninta wanda ya zarta na madam shema sau ninkin ba ninkin tare da kisma matsayin Madam Shemah ga Taufeeq d'inta. "yakayi Taufeek d'inta ya tsira daga mammunar hatsarin daya faru dasu har yayi aure a wata duniyar ya manta da ita arayuwarsa ? "Ai kuwa idan haka ya kasance gaskiya data sake tafka babban kuskuren arayuwata, na 'bata tsawon rayuwarta datayi akan kaunarsa .... cike da tashin hankali shemah ta juyo a firgice tana fuskantar gefen da Ammi ke zaune tana zubda hawaye tasoma magana cikin harshen turanci, "dan Allah kiyi hak'uri akai shi hospital domin tsiratar da rayuwarsa banason na rasashi, wallahi shine komai na rayuwata, "rayuwar da babu Mahbub cikinta kango ne babu majingini...... takarasa maganar tana sake bawa direban umarnin zuwa hospital. "Ammi dan Allah ki bari akaishi hoapital kar murasashi zuwa dashi gida bashi da wani amfani a wuce dashi hospital d'in Doctor rak "Ammi kinsa komai akaina kinsan halin k'angin rayuwar dana shiga akansa "dan Allah ammi karki bari na sake rasashi a karo na biyu arayuwata .. kuka suke sosai suna rokonta tamkar wasu yara k'anana, wanda haka yasa Ammi kasa cewa komai d'an kusan tafi kowa shiga tashin hankali sai dai murnar faruwar wannan alamari ya d'an natsar da zuciyarta, d'an batasan yadda zata misalta tarin farincikinta ba. " yau tazo mata da abubuwa dayawa na rud'ani, farinciki da akasin haka .. "abubuwan farinciki sun sha faruwa daita arayuwa amman wannan farincikin ya zarta kowani irin farinciki gareta ,ayanzu fatanta Allah ya farkar da d'an'uwanta ya dawo tamkar yadda take son ganinsa .. "A she dai gaskiya Abdul ya fad'a mata lokacin baya a farkon had'uwarsa dashi har yazo mata da zance amman ta karyata yuwar haka ? "ashe gaskay ne ba karya bane zata sake rayuwa da d'anuwanta mafi kusancin d'an uwa arayuwata, har su cigaba da rayuwarsu tamkar yadda suka ginata a can baya? "wannan farincikin da me yayi kama?" idan aka barta da wannan farincikin kawai ya isheta karasa sauran rayuwarta datayi saura cikin salama da kwanciyar hankali mara misaltuwa . da wannan tunanin suka k'araso hospital inda suka iske minister tare da wasu manya likitoci suna jiran karasowarsu suna gama karasowa batare da 'bata lokaci ba aka turo gadon marasa lfy aka daurashi aka nufi zuwa wani special room da minister yabada umarnin akwantar dashi sannan suka d'aura masa drip har lokacin bai farfado ba ransa na hannun Allah. taimakon gaugauwa suka shiga bashi, da kyar suka samu nasarar dawo da numfashinsa daya d'auke sakamakon buguwar zuciyar daya samu. bayan numfashinsa ya dawo daidai ,minister ya dawo kusa dashi ya tsaya akansa yana karewa amininsa kallo tsab "tabbas wannan shine mutumin da zuciyarsa take cike da kewa da mararin sake d'aura kwayar idanunsa akansa bayan wasu shekaru da suka shud'e, sosai ya tsurawa fuskar Taufeek ido tamkar ranar yasoma ganinsa kallonsa yacigaba da yi kafin daga baya ya fita ya bar d'akin tare da bawa Ammi kad'ai umarnin shiga taga yanayin jikinsa amman sai ga Salema da shema na rigerigen shiga d'akin kusan atare suka iso kansa kowanensu na kokarin taga ta kai hannunta jikinsa. Salima ce tasamu nasarar rike laulausar tafin hannunsa cikin nata ita kuma Shema tayi k'ok'ari d'aga kansa ta d'aura saman cinyarta tana shafa sumar kanshi tana sauke naunauyen ajiyar zuciya. wasu daga cikin tsirarru'yan uwana suka shigo d'akin suna tambayar yanayin jikin nasa" da sauki Ammi tace can bayan kamar minti goma doctor Rak ya sake dawowa d'akin cikin tsantsar farinciki yake taya Ammi da Salema murna sake ganin Taufeek a rayuwarsu daga karshe yace "su d'an barsa saboda yana buk'atar hutu dan kwakwalwarsa ta sake samun natsuwa . zaune yake cikin motarsa kirar land cranch yana direving ahankali cike da matsanancin fargaba da tunani iri iri "ta inda zaiga Su'ad d'insa bugun zuciyarsa ,rayuwarsa yake "tunda abun nan ya faru bai sake samun natsuwar zuciya ba kullun fita yake bulayin nemanta cikin gari, "duk inda yasan zai ganta daman idan baiyi tunanin zai ganta ba yaje amman har zuwa wannan lokacin ko ci karo da me kama da ita zuciyarsa baiyi ba. wani lokacin haka zai samu guri gefen titi yayi parking ya d'aura kansa saman sitiyarin mota yayita kukan xuci yana zance zuci yana hasko fuskar matarsa mafi soyuwa cikin ransa . haka zai d'auki lokaci zaune yana tuna rayuwar da sukayi abaya tun kafin ya aureta da bayan aurensu, a halin yanzu kusan haushin kowa yake ji ganin yadda aketa sha'anin farinciki , alhalin an sa shi yana tattare da tashin hankali . kiran wayarsa ake yafi sau goma sha amman da zarar ya duba screen din wayar yaga kiran daga Musty ne "sai yaja dogon tsaki tare da katse kiran a ganinsa kiran me zai masa? "Lokacin daya rasa matarsa lokacin shi ya bude sabon shafin rayuwar farinciki ,wani kiran ne ya sake shigowa ya buga sitiyarin motar da k'arfi sannan ya d'auki wayar a fusace "lafiya malam zaka dameni? "dan Allah kayi harkar gabanka nayi tawa ya ja tsaki yana k'ok'ari kashe kiran Musty yayi saurin dakatar dashi "please abokina karka d'auki zafi dani karka d'auka ban damu da damuwarka bane ko babu halakar komai tsakaninmu dole na tayaka jaje da jimamin tare da tayaka neman matarka. "wallahi Ak na damu k'warai da rashin sanin inda Su'ad take kawai kafafuna ke tsaye amman ni kad'ai nasan irin tausayawar danake maka........ "dakata dan Allah malam banson long talk kiran me ka min yanzu bayan kun gama shan budurin bikinku ? "Ai wallahil azim haushinku nake ji gaba dayanku har Ammi da Umman Su'ad idan kowa yayi abinda yaga dama ita Umman Su'ad bai kamata ta dinga karfafawa Ammi zuciya ba "kamar batasan ciwonta ba' " well daman nasan nafita damuwa da Su'ad d'in. "karka ce haka Ak mahaifiyarta ce fa ta dai yi kara ne saboda kwanciyar hankalin Ammi,"dan malam dakata karka cikani da magana "kwanciyar hankalin banza da wofi mutun yarasa d'a sukutum guda amman ya zauna yana.. sai kuma yayi shiru yakasa k'arasa abinda yaso fad'a. "yanzu dai ka sausautawa zuciyarka In sha Allahu tana hannu nagari kamar yadda Ummanta ta fad'a inji cewar musty .. Ak ya runtse mayatattun idanunsa da suka gama sauyawa zuwa jajja sannan yacigaba da mgn "Musty bansan yadda zanyi da rayuwata ba, bansa inda zanga su'ad ba, zuciyata zata buga idan narasa ta wallahi mutuwa zanyi muddin na rasata ka taimakeni musty ka ajiye hidimar bikin nan ka tayani neman matata da cikin jikinta "cool down Mana
Chapter 261 · 0% Book details