← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 289

Sashe 167

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zan fito dan babu abinda zakayi...... duk mgnr dayayi sai ta meida masa da martani, ta cikin dakin. ransa a matukar fusace ya baro jikin kofar ya dawo parlour 'n ya tsaya dafe da gashinsa kwata kwata ya kasa samun natsuwar cin abinci har ammi ta dawo daga part din dady yana zaune ya zabga uban tagumi"ya ka tasa abinci gaba batare da bude ba "anya kuwa lfy kake abdul tun da kashigo gidan naga ala'mun kana cikin damuwa. sautin muryarta yasa ya dago yana kallonta fuskar a hade tmkr hadari kwata kwata babu annuri farinciki a tattare da shi sannan muryarsa cike da sabon rudani" yace babu komai ammi amman wallahi azim ki gayawa wannan yarinyar tashiga hankalinta dani inda ba hk ba wata rana zan dargatad'a miki ita. "karka soma abdul kar naji kar nagani,me yayi zafi ? "me ma tayi maka daga fitata yazu? babu kawai yace ataikace tare da mikewa tsaye yasoma kokarin barin parlour ammi ta bude plete din abinci taga bai ci ba ta dago idanunta tun bai kai ga fita ba " bazaka ci abinci bane? "uhm yayi mgnr muryarsa a dakile to a sauka lfiya abincin ma zai kara mana aiki ta sake tura masa wani haushi aiko ya shaki haushi zuciyarsa sai tafarfasa take ya isa inda yayi parking din motarsa yashiga ya tadayar aguje ya bar gidan. yana isa gida kai tsaye dakinsa ya shige ya kulle kansa, shi kadai yasan yadda yake jin zuciyarsa wuni ranar bai sake lekowa ko parlour kasa ba ,yana kwance adakinsa sallah kawai ke tadashi ,Zeey data lura kmr yana cikin damuwa, hankalinta yayi bala'i tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye zuwanta biyar dakinsa amman har wannan lokacin kofar dakinsa a kulle yake ,hkn yasa ta hakura ta koma tare da shiga kitchen domin daura musu abinci dare ,duk da ko na safe dana rana bai ci ba sai zubarwa tayi dan babu wanda zata bawa. ranar ma kmr daren jiya takasance masa tunanin abubuwa suka hanashi runtsawa , duk inda ya motsa tunanita ne ,kwata kwata ya kasa runtsawa har gara jiya ma ya samu bacci ya dan daukeshi akan yau , yadda yaga dare hk yaga rana koda gari ya waye gbdy ya canza yayi wani zuru zuru dashi yayi ramar dole ,wanda kallo daya zaka masa kasan yana cikin damuwa, koda yaje office ma kasa aiwatar da komai yayi ga tarin file file's nan gabansa amman ya gagara tabasu . ******** daga office kai tsaye gidansu ya wuce kmr yadda yasaba, domin xuciyarsa na kwadayin son ganinta ko zai samu natsuwar zuciya, amman abun takaicin koda ya isa gidan ko me kama daita bai gani ba balle ita, duk da yasan tana ciki gidan sbd shi taki fitowa ,dan hk ya wuce gida ransa a matukar bace bugun zuciyarsa na kara tsananta. yana zuwa gidan ya zube a parlour 'n kasa inda zeey take zaune tana shan kayan fruit tana ganinsa takaraso garesa cikin sauri dan ta lura da yanayin yadda yashigo gidan cike da matsanancin damuwa ta iso kusa dashi "my life sannu da zuwa ya office kmr kagaji dayawa ko? ya dago da mayatattun idanunsa ya dubeta"me kika gani? "baka saba zama parlour'n kasa ba ,na lura da hkn ne tun lokacin da aka kawoni kai tsaye dakinka kake wucewa ,ta mike tsaye ta nufi dakinsa da briefcase dinsa a hannuta sannan ya mike yabi bayanta yashigo dakin daidai lokacin data shiga bathroom dan hada masa ruwan wanka ta fito ta same shi zaune a gefen gado yana kwance agogon hannusa takaraso da sauri ta tsuguna gabansa tare da soma cire masa takalmansa. "yau duk sai naganka wani iri kmr kana tattare da damuwa ko duk gajiiyar ce? bai tanka mata ba asalima ko kallon inda take bai yi ba yasoma balle mabalin rigarsa. "ko baka jin dadin jikinka ne? yaja dagon tsaki ransa a matukar bace.. "dan girma Allah ki barni karki dameni da tmbayoyi kmr wata majistret.. ... gabanta ya bada wani rassssss yashiga dukan tara tara ta dago ahankali ta dubeshi domin tabbatar da reaction dinsa fuskarsa a matukar daure kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa jikinta yayi sanyi sosai hankalita ya tashi har tagama balle masa mabaling rigarsa ya mike tsaye ko kallon inda take bai yi ba ya nufi bathroom ta mike ta dauke takalmansa ta kai su cikin shoerak ta ajiye takoma dakinta zuciyarta cike da tunani iri iri anya kuwa aikinta ajikinsa bai soma samun matsalaba kuwa ? tayi kanta tmby tana kallon jikinta ko akwai matsala daga agurinta ne byn tunani datayi yanzu nan ma komai Norma tagani jikinta tsab babu wata makusa da zai saka taga yanayinsa hk ta sake feshe jikinta da turaruka masu masefaffun kamshi ta dawo dakinsa ta ciro masa kanana kaya wanda tasan yafi bukata inda ya dawo daga aiki . yana fitowa ta nufi gurinsa da sauri dan taimaka masa, bai so hkn ba amman ya kyaleta har tagama shafa masa lotion da turare madadin taga ya dauki kayan data ciro masa sai taga ya nufi wordrobe dinsa ya dauko wasu daban daga nan jikinta ya sake yin sanyi tai tsaye tana kallonsa tabbas akwai gagarumar matsala me girma dake shirin faruwa daita tana tsaye ya fito batare dayace mata komai ba ko kallon inda take, koda bai taba kusantarta ba yana bata kulawa sosai baya barin cikin damuwa adan zamansu tabi bynsa tana kallonsa kirjinta na wani irin bugu har yakai bakin kofar fita daga parlour muryarta na rawa "tace my life abinci fa "sai na dawo...... tunda ya bar gidan ta kasa zaune takasa tsaye har sai data kai ga kiran kawarta bj take sanar mata da komai tare da cewa kozata taimaka taje mata gurin na kan dutse "bazan iya zuwa wannan guri me hatsari da bin kaida ba, ke dai ki daure ki fito kije da kanki hb bj karki min hk kinsa komai fa har yanzu AK bai kusanceni ba da zarar naje da kaina dole boka na dutse yace sai anyi sex. oh shine ni zaki turani sbd bansa ciwon kaina ba ya gurji banza wlh ban zuwa koina sai dai idan wani gurin ne daban ba gurin wannan dan iskan bokan ba,wanda ko dan rakiya baya dagawa kafa sai yaci "pls now bolaji...... "ke wlh ban xuwa tayi mgnr tana katse kiran. gidan ammi ya sake komawa ,dole yau ya ganta idan ba hk babu zaman lafiya yana tunkaro kofar shiga part din ammi yasoma jiyo kamshin daddaden kamshin turarenta me tsayawa arai da sauri yaja baya kadan ya boye daga byn kofar parlour ammi tana gama karasowa gurin itama tasoma jiyo kamshin turarensa cak ta tsaya tare da yin shr tana shan jini jikinta tana kallon ilahirin gurin gabanta na dukan uku uku kmr ta koma sai km fasa tacigaba da tafiya yana kallonta ta inda yake ta isa har inda securities din bakin get suke zaune ta mikawa daya daga cikinsu kudi shi dai bai san abinda tace musu ba amman gbdy zuciyarsa ta hautsine bakinciki ne me tattare da matsanancin kishi ya caki zuciyarsa har takaraso zara gota shi ya hanzarta fitowa daga maboyarsa sai ganin mutun tayi agabanta ya mugun tsareta da ido yana kallonta ransa a matukar bace sai wani huci yake kmr mayunwacin zaki tayi saurin jan da baya zata gudu ya cafko hannunta cikin nasa jikinta na rawa ta bude bakinta zata kurma ihu sbd matsananci tsoron dataji, ya toshe mata baki da hannunsa daya yashiga janta zuwa byn part dinsa na gidan tana tirjewa ganin hk yasa yasaka hannunwansa duka ya dauketa ya rungumeta ajikinsa ya manne bakinsa danata waje daya ta yadda babu me iya jiyo sautinta . suna isa ya direta bisa kafafunta ya hadeta da kirjinsa har yana jin tudun brest dinta yana cuking kirjinsa ya lumshe idanunsa yana busa mata hucin numfashinsa muryasa a kasalance "yace ni kike zagi jiya su'ad? har yanzu ban wuce zagi ba agurinki wai ina soyayyar da kike ikirari kina min? "ok daman soyayyar iya baki ce bata gsky ba? tayi shr taki yin mgn. "sannan me ya kaiki gurin masu gadi? nan ma shr tayi masa kmr wace bata mgn. "bana bukatar ganin kin sake zuwa inda suke duk abinda kike bukata ga eiman ki aiketa zata .mgnr duniya yayi mata amma furta taki cewa wani abu dan hk ya tsura mata idanunsa kawai yana kallonta tabbas tana da matukar kyau na daukar hankali da fixgar mutun zuwa gareta koda kuwa mutun baiyi niyya ba tsawon lokaci ya dauka yana kallonta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke karuwa akanta. ita din ma ayau wani irin kallo take masa wanda ke tabbatar mata akwai wani abu da yayi masa shamaki cikin farincikisa gbdy yanayin fuskarsa da ilahirin jikinsa sun gama nuna mata rauninsa gabanta yayi mugun faduwa sakamskon tunani da zuciyarta ta jefeta dashi yayinda gbdy zuciyoyinsu suka shiga bugawa atare most especial AK daya fita shiga damuwa a yanzu dayake tsaye agabanta kiyayyarsa karara yake hangowa cikin idanunta "muryarta can kasa kasa kmr zatayi kuka tace "zan wuce ina da abin yi, "meye shi abinda zakiyi wanda yafi mijinki mahimmanci? "miji fa kace? "yes of course miji kuwa tsayaye... "gsky ni banga wani tsayayen miji ba anan dan hk kabarni hanya na wuce dan ni ban daukeka amatsayin miji ba "koda kuwa kana matsayin mijina ne na ajiyeka na wani lokaci sbd ahalin yanzu bana bukata yin rayuwa tare da kai....... wayyohhly Allah wani abu yaji ya tsaya masa akahon zuciya wanda yasa shi ya matsawa baya kadan yana dubanta cike da sanyi jiki kafin daga baya ya runtse mayatattun idanunsa gam gbdy canzarwata yana daure masa kai kar dai abinda yake zargi a game daita ne yake shirin faruwa dashi .....? aiko idan hkn yakasance akwai matsanancin damuwa domin kuwa zai addabi rayuwa kowa dake cikin koda ya bude idanunsa yaga wayam babu ita babu alamunta kafafunsa yashiga dagawa da kyar bai ko kalli part din ammi ba ya nufi kofar gidan kmr wani zautacce sbd a can motarsa . wannan haduwar tasu yasa gbdy su'ad ta kaurace masa sbd tasan a yadda take matsanancin masefar kaunar shi, yawon haduwarsu zai iya rusa mata budget dinta wanda
Chapter 167 · 0% Book details