← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 289

Sashe 197

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

motar cikin gida. a falo ya tarar da eiman da su'ad zaune suna kallo suna hira akan kallon da suke ,kallo daya tayi masa tasan yana cikin damuwa me tattare da tashin hankali amman ta dauke kanta ta meida kan TV shi kuwa tsura mata idanunsa yayi sosai yana hasko fuskar mutumin daya baro yanzu, kai ashe ma mutumin bada amminsa yayi kama ba da matarsa yayi kama ,ahankali ya dauke kanshi ya meida kan eiman dake masa sannu da zuwa "sis ina ammi? yaya lfy dai ko? "ina ammi dai, abdul gani lafiya dai naganka ka dawo yanzu ? ammi ki zauna kiga wani abun mamaki kar dai ta tsaya dogon tmby yasa tasamu guri ta zauna su'ad da eiman nagani hk suka tashi atare suka tashige daki. yakarasa kusa daita ya xauna, gama zamansa ke da wuya ya ciro wayarsa dake cikin gaban aljihun rigarsa yana duba hoton daya dauka yanzu , sai daya kare mishi kallo sosai ya tabbatar da mutumin daya sani ne ,sannan ya mika mata wayar idanunta ta daura akan screen din wayar tana kallon hoton me dauke da fuskar da baza taba mantawa dashi ba a iya tsawon rayuwata sai dai wannan ba wanda take tunani bane sai dai kuwa inda kama ce.. jikinta a matukar sanyaye tace "abdul a ina kasamu wannan tsohon hoton me kama da dan'uwana? "ammi ki tashi yanzu muje gidan senator wannan ba tsohon hoto ba mutumin dake cikin hoton nagani da idona agidan senator bankole har ma mun tautauna a tsakaninmu dashi . "girgiza kai tasoma yi can km tace "abdul bashine mutumin da kake tunani ba tabbas fuskarsa ce amman bashi bane, inda ace shi dine dana ce, yau ce rana mafi dadi arayuwata dazata kasance byn wasu shekaru da suka shude..... takarasa mgnr tana zubda hawaye "ammi ki kiyi hkr ki daina kuka wlh dana san zuwana da wannan zance zai sa kiji babu dadi da banzo ba ,amman kiyi hkr nima abun ne ya daure min kai kamar tayi yawa gsky ," Allah na halita ammi har mgnrsu fa iri daya babu wani abu dazaki kalla ajikinsa kice bashi bane amman jikinsa da komai da komai iri daya yazo daga kasar koria domin bude kafaninsa na Airvoice km shi keda mallaki mahbub airline yana da hannu jari da dama a campenies na kashe duniya yana da a abuja lagos kano sokoto da sauran garuruwa anan Nigeria amman shi wai asalin mutumin kasar koria ne. "kai ma kaji da kunneka mutumin dake da tarin dukiya kmr wannan me hadashi da wanda kake tunani ,"kama ce kawai km hk Allah ke lamarinsa tashi kawai kaje kayi abinda zakayi mun dade da daukar wannan kaddarar "yaushe ne tafiyarka zuwa koria? "jibi idan Allah ya kaimu yana dubanta cike da tausayawa, parlour'n ya dauki shr na wasu yan mintuna sannan ya motsa bakinsa ahankali ya kira sunanta cikin sanyi murya "ammi....... "na'am abdul ta amsa muryata a sanyaye " dan Allah ammi ki bani aron su'ad man mu tafi koria tare ,na miki rantsuwa da Allah bazan cutar miki daita ba, ki duba yadda nake matsanancin son yarinyar ,ta yaya kike tunani zan iya cutar da abinda nake so. "ban hanaka daukar matarka ba, ko tafiya daita duk inda kake so ba amman kayi mata zance tafiyar da kanka idan ta amince meye nawa aciki abdul nifa yar addur a sauka lfy ce jikinsa a matukar sanyaye ya mike tsaye yasoma kokarin barin parlour'n .. "bazan wani wahalar da kaina gurin neman izininta ba tunda narigada nagama shirya komai na tafiyarmu tare daita ,sai dai kawai ki laluba ki nemeta ki rasa yayi mgnr cikin ranshi yana karasa ficewa. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 197 · 0% Book details