← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 289

Sashe 13

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wasallam:* *bayyanal Abdi wa bayyanal kufri tarkussalat* *Allah's messages (s. a. w) said :the difference between the servant of Allah and infinitely is to abandon prayers* Page 5 Ammi na nan zaune inda su Malik suka barta. idanu kawai ta zuba masa tana Kare masa kallo cike da tausayawa. wanda har zuwa lokacin AK bai dawo daidai ba.kwata kwata baya ma cikin hankalinsa. addu'oi tashiga karantowa tana tofa masa takoina a sansar jikinsa tare da zubawa sarautar Allah. "Ahankali ta mike tsaye jikinta a matukar sanyaye ta koma Kan daguwar kujerar dake dakin Ta zauna tayi facing dinsa tana cigaba da kallon danta.. Tunani tashiga Yi .Ta inda zata fara neman maganin wannan azzabben ciwon dake son yiwa rayuwar danta nakaso. Ajiyar zuciya Ta sauke da karfi Kana ta zarce da tunani tun daga lokacin da mummunar ciwon nan ya tsarki tilon danta nmj bata da kwanciyar hankali daidai da second 1 burinta arayuwa bai wuce tasamu inda zata samo maganin matsalarsa ba . adddua kullun cikin yinta take magani kuwa ta kota ina karbo masa ake takowani bangare daga daginta dana mahaifinsa .daman mutane sunce babu uwar da bata sha wahalar ya'yanta ba, kafin tazama uwa ba. Dan hk dole matsalar danta yazamo tata matsalar domin samun inganci lafiyar arayuwarsa da samun kwanciyar hankalin zuciyarsa shine nata kwanciyar hankali ita yanzu Duk yadda zata raba tilon danta namiji da wannan ciwon zatayi..... ...... Can kmr minti 30 tsakani ciwon yasoma sakinsa yana barin jikinsa,ahankali natsuwarsa da tunaninsa suka dawo gangar jikinsa. Cikin sanyin jiki ya yunkura ya tashi zaune bisa tsakiyar gadonsa tunani yashigayi. ina su musty da akil da Malik suke? iya tunaninsa suna tare suna hira atsakaninsu ne. sannan shiyasan basuyi sallama da junansu ba. to ina suke? Tmbyr da yayiwa kanshi Kennan wanda bashida me bashi amsa tmbyr.... Ahankali idanunshi suka sauka akan mahaifiyarsa dake zaune opposite dinsa tayi shr idanunta na kallon sama sannan fuskarta da alamun damuwa fal. sosai tayi zurfi cikin duniyar tunani abinda shi kanshi bai san dalilin jefawarta cikin wannan damuwar ba . da kyar yasamu ya iya bude bakinsa yakira sunanta cikin tautaushiyar muryarsa me cike da tsananin dadin da sauraro ammi ...... Firgigib ammi ta dawo cikin haiyacinta daga duniyar tunanin Data lula tana dubansa cike matsananciyar damuwa maramisaltuwa ,tana me mikewa tsaye da sauri jikinta na rawa tare da cewa na'am yarona sannu yakake jin jikin naka yanzu ? taso taso mike kabaro inda kake Atare tayi masa wannan tmbyr jikinta na tsananta rawa . mikewa yayi tsaye yana kokarin saukowa daga kan bed din kmr yadda ammi tace dashi . ta nuna masa kan kujera alamun ya zauna ita km tashiga yayyafa ruwan magani tun daga kan inda Ciwon yatasar masa har xuwa kan gado inda ciwon ya sakesa . duk AK na zaune yana kallonta . take km abinda ya faru yashiga xuwan masa daki daki cikin brain dinsa, shi dai yasan hira suke da abokansa daga nan suka sako hirar onye har zuwa sanda yaji kanshi yafara sarawa. Sannan yanzu gashi yaganshi daga shi sai amminsa km cikin wani yanayi na daban me wuyar fasaltawa. Duk sanda zai ga amminsa irin hk cikin halin tashin hankali da rashin natsuwar zuciya yasan akwai matsala. ko ciwonsa ne yatashi ko akasin hk . runtse mayatattun idanunshi yayi sosai yana jin bugun zuciyarsa a sarari, sbd zuwa yanzu yagama sanin ciwonsa ne ya tashi, sosai yake jin zafin Ciwon dake damunsa da son yiwa rayuwarsa barazana mara iyaka ... Wai meke faruwa dashi da rayuwarsa ne? Me yaka mata yayi akan wannan matsala dake neman dakushe farincikinsa ? Babu... babu abinda zakayi Abdulkabir hk Allah ya tsaro maka taka kaddarar rayuwa . wannan ciwon yana daga cikin jarabawar ubangijinka gareka baka da yadda zakayi addu'a kawai shine mafuta gareka . zuciyarsa tabashi amsa da hk.. hawayen tausayin kanshi da amminsa suka shiga xubowa bisa kuncinsa. yayi saurin saka tafin hannunsa ya dauke hawayen dake tsiyayo masa sbd bayason amminsa tagani zai kara mata damuwa. ahankali yashiga furta kalmar alhamdullahi alhamdullahi alhamdullahi I know this critical sickness is a geft from my God ...babu abinda, zan iya ko nace daya wuce godeya ga Allah .... Ammi tagama Duk abinda yadace taje Ta hada masa ruwan wanka Ta zuba magani ciki ta dawo inda yake zaune tana sake Yi masa sannu tana me boye tsananin damuwar datake ciki, tace abdulkabir kaje kayi wanka . Ga ruwan maganinka can na hada maka, da kyar ya iya mikewa ya nufi bathroom dinsa.hannushi rike da jallabiya. yaje yayi wanka zuciyarsa cike da tsoro da frigicin abinda ke damunsa. yanzu da a dakin onye da yayi niyar zuwa dazu wannan Ciwon ya tashi me zai faru Kennan ? da me zaicewa amminsa da dady'nsa da iman da zeeey dinsa...... ? da ina zai Kai wannan katuwar abun kunyar ciwonsa ya tashi a dakin karuwarsa ? Da wannan tunanin dayake tayi har yasamu yagama wanka . koda ya fito tuni ammi tagyara masa dakin tsab sai kamshi turaren wuta ke tashi takoina . gefen gado ya disina ya zauna sanye da jallabiya . yana kallon mahaifiyarasa . wani irin farinciki mara iyaka ne ya mamaye zuciyarsa da ruhinsa . ya dinga arashin duk wanda yayi rashin uwa bakaramar hasara yayi ba. sannan duk wanda yarasa uwa yayi kuka.... Uwa itace komai na arayuwar ya'ya. tausayinta yasa yaji kmr zai daina leifin dayake aikata a boye tun kafin wata rana Allah ya tomasa asiri,.. Ammi tace suwaye suka sha sigari adakin nan? Tayi tmbyr ne sbd tasan Danta baya cin ko goro ballantana wata aba sigari. muryarsa a kasalance irin ta marasa lfy Yace ammi su akil ne. sbd mene kai baka sha ka dinga barin ana sha maka a daki....? Sorry ammi bazasu sake ba better kar na sake ji nasake ganin ansha maka sigari adakinka ,ai tun baka kwadayin da ra'ayin shanta shansu anan zasu iya rebatanka... Ai bazan hadawa kaina fitina biyu Ba, ga neman mata ga shaye shaye ya fadi hk cikin ranshi kwanciya yayi yana me runtse idanunshi. Domin yasan hk kawai shi zai saka ammi tabar mgnr ta mike tsaye karkayi bacci katashi kasha magani Dan yunkurawa yayi ya manna bayan da jikin gado. Ammi Ta miko masa cup dake cike da ruwan magani ya amsa ya sha sosai domin shi kansa yana bukatar rabuwa da ciwon dake addabar gangar jikinsa sabanin da ,da kyar ammi take samun yasha magani . byn yagama sha ammi tace ya kwanta ya huta sannan tabar dakin. Zeey kuwa tana can tare da akil dinta suna sheke ayarsu son ransu suna jiyar da kansu dadi mara amfani . da kyar Zeey tasamu akil yabarta . ba ita ta dawo gidan ba sai daf da magariba takaraso da kyar duk tagaji sbd wata uwar muguwar kasala datake ji ajikinta. koda tashigo gidan taga AK wani iri wani iri dashi tmkr wani mutun mutumi. duk ta damu ta rude ta tada hankalinta sai tmbyrsa take meke damunsa yayi mata banza. sai da ammi tayi mata bayanin abinda ya faru . kuka Ta fashe dashi tana kiran wannan wace irin maseeface dataki taki cinyewa? tana kuka tana zuba sambatu iri iri na rashin hankali . AK nagani tasoma shirmenta na kuka ya mike ya koma dakinsa sai da ammi tai ta rarrashinta tukun tabar kukan. wasa wasa fa tsakanin AK da Zeey shakuwa ce me tsanani tashiga tsakaninsu kowanne yana ji da dan'uwansa cikin ranshi kmr me. bama kmr Zeey ba datake jin tabbas bazata iya rayuwa muddin babu AK ba Dan wani irin shaukin kaunarsa ke shigarta a duk kwanan duniya . Zeey na zaune a parlour tana yanke kumbarta tana kallon wani seizing film iron lady bataji sallamar AK ba sbd zurfin datayi gurin kallon sai dai kawai ta dago idanuta taganshi tsaye bisa kanta yana kare mata kallon kasa da sama . "Wani irin masefafiyar faduwar gaba taji from know where ta dira cikin tsakiyar kirjinta, wanda bata taba jin Irinsa ba a duk iya tsawon rayuwarta. take zuciyarta tashiga rawa da tsalle. sosai itama take kallonsa tmkr zata cinyesa sbd matsanancin kyawun dataga yayi mata yau fiyye da koda yaushe datake ganinsa yanayin kallon dataga yana mata yasa duk sai taji ta tsargu Dan hk tayi Saurin sunkuyar da kanta kasa tacigaba da gyaran kumbarta. AK ya tsugunna agabanta yana murmushi ya Kai hannu zai riko hannuta niyyar amsa abin gyaran kumbar yacigaba dayi mata. tayi saurin janyewa . ya dago da mayatattun idanunsa yana zabga mata katuwar harara meyye hk na wani zabura Dan zan rike hannuki. haka nan sai ka dinga tabani ? Ta fadi hk ne sbd duk lokacin da zai tabata din sai taji wani sauyi atare daita . muryarsa a kasalance yace to menene Dan natabaki ni ba yayanki bane? Tsiyata daku Hausawan nan Kennan kidahumanci da kauyanci na dawainiya daku . kwata kwata bansan sanda zaku waye ba. Ta hararesa tana cewa Allah yaso kaima duk asalinka Kennan . AK ya mike tsaye tare da yunkurawa yana Cewa banson shirye ni kawo abinci koda da indomi ce Babu komai acikina ta kalleshi sosai zuciyarta na tsananta bugawa da sauri akan shi. wani irin tsananin sonshi ne take jin yana sake ratsa kowani shashi na tsantsar jikinta . ta lumshe idanunta batare data mike ba. AK yaja tsaki tare da cewa wai meye kika wani sakani gaba sai kallona kike ko na canza miki ne? tayi murnushi tare da yunkurawa gabadaya ta tashi da hanzarinta. " cikin takunta kmr batason taka kasa tana motsa ilahirin jikinta Tukun tabar guri . bayaanta yabi da kallon har sai daya daina ganinta. bata dauki wani lokaci ba ta dawo hannuta rike da karamin faranti Ta ajiye akan center table takoma Ta dauko masa ruwa da drinks ta koma Ta zauna tana wani yatsina fuska wai ita ala dole tagaji. Ak yace sai Ki taso Ki zubamin ruwa. Ta Dan harareshi tare da yin mgn cikin shagwaba tace kai yaya wlh kacika son jiki da shagbawa ruwan ma bazaka iya zubawa kanka ba? Eh banzan iya ba ke km tsarkin kiyuwa ba? Tayi tsuguno agabansa har yana hango
Chapter 13 · 0% Book details