Sashe 114
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abubakar tafeeda gulunbe ni malaminta ne sannan ina sonta . km aurenta nake son yi.... shine ka tasa min "ya" agaba ka kwakume kmr zaka cinye min ita? duk fadin gurin nan bai isheka zama ba sai sanya min ita ajikinka .. kai tun yaushe ma kasoma zuwa gidan nan da banida masaniyar hkn? prof taufeek wanda yashiga tashin hankali ganin reaction din mahaifina yayi saurin cewa shekara daya da wata takwas kenan inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda naji mahaifina ke furtawa kenan yana sake maimaitawa sannan yace ina raye acikin gidan .. Kai a garinku aka ake neman aure ?prof taufeek yayi shiru ya sunkuyar da kanshi kasa abinda nake son sanar da kai yadda kaxo neman auren yarinyata kwata kwata bai yi ba amman na yafe maka sai abu naga da zagaya maka na dade dayiwa yarinyata miji .. da wani mugun sauri ya dago idanunsa yana duban mahaifina yace eh abinda kaji nace hk ne nayi mata miji dan hk ga hanya ka kama gabanka kabar min gida tun ban sa ma'aikata sun hukunta min kai ba . tunda mahaifina yasoma mgn naji zuciyata ta tsaya cak ta daina aiki na wucin gadi na dawo tmkr wata matacciya atsaye akan kafafuwana kusan minti biyu sannan zuciyata tacigaba da bugawa da karfi tmkr ana bugamin guduma mgnr babana ba iya kunnena kadai suka tsaya ba har cikin tsokar dake makale akirjina nake jin dacinta . matsowa nayi kusa da mahaifina ina kallonsa ina son ya sake mgn domin so nake nasake jin abinda ya fada din karya ne ba gsky ba . sbd dacin kalmar danaji ya fada lokacin. ahankali naga prof taufeek yayi kasa ashe dukursawa zai yi agaban mahaifina muryasa na rawa yace ba... ba kayi hakuri nasan nayi kuskuren gurin neman maka yarinya batare da ixininka ba amman dan girman allah karka hukuntani bisa wannan kuskuren dana aikata sbd ina son saleema ..so kuwa me karfi na kwadaitu da son aurenta nayi hk ne sbd kada na yanke mata karatunta ko kawo nakasa cikin rayuwarta. wanda bansa kuskure na tafka ba kayi hakuri dan girman allah karka rabani daita. rabani daita tmkr barazana ce ga rayuwata . nima dukursawa nayi jikina na kirrrma kmr yadda jikin prof keyi . hawaye kuwa kmr fomfo sai ambaliya suke saman fuskata ,bakina na rawa nace karka min hk ya babana... karka rabani da rayuwata ina son taufeek bazan iya rayuwa babu shi ba asanina nasan baka min miji ba kayi hakuri muyi kuskuren..... a fusace ya dagoni ya daukeni da wani gigitaccen mari ki min shr .. tunda har kinsa ki kawo nmj gidanku batare da sanin mahaifinki ba zaki iya yin feyye da hk ke idan diyar albarka ce ba gurina zaki turo sa ba . kwata kwata banji zafin marin dayayi min ba na sake cewa kayi hakuri baba tsoron aikata hkn nayi, ahankali naga prof taufeek ya mike tsaye ya tsura min ido tare da alamomin tmby iri iri akan fuskarsa sai ma nake hango zargina cikin idanunsa tsawon lokaci ya dauka yana kallona sannan ya juya yasoma tafiya nabishi na rungumeshi ta baya dole ya tsaya jikinsa kirrma kar ka min taufeek.... karka barni taufeek... karka tafi kayiwa babana mgn ta fahimta nasan zai gane irin son da mukeyiwa juna ... ya juyo dani tare da ware hannunwasa duka zai rungumeni yaga yadda mahaifina ke auno masa kallon tsana ya fasa ya zareni daga jikinsa yasanya kai zai fice na tsugunna a gurin tare da daura hannuna duka saman kai na rusa kuka me cin rai ina kiran sunansa don't go taufeek.. ka tsaya kabawa babana hakuri yana sona nasan zai baka aurena.... amman ya bar gurin batare daya tsaya ba wani irin haushi mahaifina yaji yakamashi agabansa na rungume wani ina kukan soyayya .. yaushe ne yayi wannan sakacin da rayuwata a tunaninsa duk tattalin dayakamata ya min bai ce dani komai ba illa cike da sanyi jiki ya kamo hannuna muka shiga cikin gida inda mamma take tana ganimu ta mike tsaye tana kiran lfy..? ina fa lfy yarinyar nan she zance take acikin gidan nan banida masaniya. bata isa yin zance bane ?mamma ta tmbyeshi . sannan shi wannan mutumin nasan yana zuwa gurinta dan tasanar min kafin yasoma zuwa.. ni dai nadakatar dashi sbd nayiwa "yata" miji dadewa.. bangane ba? yadda kikaji din hk nace sannan daga yau nayi cancelling zuwa wata makaranta ya juya yashige dakinsa ya barmu tsaye cikin rudani da tashin hankali sake rushewa nayi da wani sabon kuka nayi dakin da ake jinyar hjy babba na kamo hannuta cikina nawa ina kuka ina kiran hjy ki warke auren dole babana zai me da wanda bansani ba.. .. ki warke kakata nasan da kina da lfy ke kadaice zaki min gatan tsaida wannan auren.. yadda nake kuka hk naga hawaye na fitowa daga idanunta motsi take da bakinta da alamun son yin mgn amman babu hali sannan a wannan lokacin na fahimci tasoma fahimtar komai ganin wannan durkuson danayi ba shine mafita gareni ba nabar dakin da da gudu zuwa nawa na fada gado ina kuka har da shesheka na dauki waya nakira number taufeek amman yaki daga na sake shiga damuwa ji na dingayi kmr nayi hauka wani irin radadi da zafi zuciyata ke min na dawo tmkr mahaukaciya sabuwar kamu a dakin ina sambatu ina cigaba da neman layinsa . ***** byn kwana biyu prof taufeek ya sake zuwa na musamman gurin mahaifina,akan yayi hkr ya bashi aurena , amman furrr yaki yace shi yayi min miji. yace to ya barni na koma school kar ya tsayar min da karatu.. yace bazanyi ba naga ba yarka bace tawa ce ko lokacin danayi ra'ayin tayi karatu har nasata kai ne kasani . dan hk mlm ka tashi kabar min gida. ni kuwa iya tashin hankali nashige shi,gbdy duniya ta cakude min waje daya banta taba sani hk tashin hankali zai riske rayuwarta ba ,na dauka irin so da gatan da iyayena suke nuna min ko dabba na kawo ina so zasu amince . wata irin soyayyar prof taufeek ce kawai take yawo dani ahalin danake ciki. jin soyyyayyarsa nake tmkr itace madogarata banson kasra kaina domin ina son mallakarsa arayuwata bance hk zan kashe kaina kowa ya huta tunda abun nan ya faru na daina ci na daina sha sai kuka na shiga tashin hankali. rarrashin duniya mamma ta min akan nayi hkr na cire soyayyar taufeek acikin xuciyata nabi umarnin mahafina.ina kuka na dubi idanun mamma nace bazan iya cire sonshi ba mamma......ina son taufeek rasashi daidai yake da zaki rasani a duniya , yadda nashiga damuwa da tashin hankali hk mahaifiyata tashiga tashi hnklinta. wanda har sabani yaso shiga tsakaninsu da babana adalilina abinda bai taba faruwa ba kenan tun iya tasowata. na dauka radadin rashin amincewa zabin babana zai tsaya iya kaina ne amman sai naga yashafi mahaifiyata. daga parlour indake zaune na tsinci muryar babana yana cewa daman ke kike daure mata gindi sannan kike kokarin bata min tarbiyar yarinya sannan kece kike neman jifa zukatanmu cikin tashin hankali da tun farko zuwansa kin sanar min da nasan matakin dauka da yanzu batayi zurfi cikin soyayyarsa har hk ba nasan dabazataba kin karbar zabina ba.... kuka mamma take da idanunta tace na gode dawood da sakayar cin mutunci amman kasan bazan so lalacewar salemat sbd ni uwa ce kai km uba duk yadda ta lalace sai nafika shiga tashin hankali fiyye da kai amman naji duk bayaninka km na amsa laifina amman waye shi mijin da kayi mata. yaki gayama sai da rigima tayi rigima sannan yagaya mata nan fa jikinta yayi maseefar sanyi takasa cewa komai. sbd tasan abin yafi karfinta ,ya dawo kusa daita tare da kiran sunanta habiba lamarin ne yafi karfina .. ni kaina bansa zan iyawa mamana irin wannan auren ba me tattare da bakinciki Amman kiyi hkr tare da yimata addua. hawaye ne yashiga zubowa daga kwarnin idanun mamma tarasa wani irin aure mijin nata yake hadawa da ahlin hjy harira . idan auren zumunci yake da bukata ai hjy babba itama tana da tarin jikoki adakinta . meyasa bazai bawa wani daga cikinsu ba ,sai cikin jikiokin hjy harira.... ? muryarta cikin kuka tace kayiwa maza auren dole amman bai kamata kayiwa mace auren dole ba domin gudun abinda zaije yazo.. salema kadai Allah yabamu mace yakamata mubata farinciki ba bakinciki ba. mutumin dake sonta bashi da makusa meyasa bazaka bashi aurenta ba domin kwanciyar hankalinmu ..? nima bance yanada makusa ba nasa an bincika minshi mutumin kirki ne me nagarta amman idan nabashi auren salima nacewa hjy harira me... ? tsawon wata uku kenan ina tsare a gida babu inda nake zuwa zancen zuwa makaranta ma andaina mgnrsa. wanda kafin zuwa wannan dan lokacin nagama sa'insa da dangina da yan gidanmu gbdy akan prof taufeek babu wanda nake ragawa duk wanda bai son aurena dashi bana shayin na ci masa matunci hade da zagin rashin mutunci ,sannan sai alokacin nasan wanda za'a bawa aurena... wato yakub dan gidan goggota shima bashi da laifi ko makusa ta fanin kyau da halaiya amman zuciyata bashi take muradi aura ba.... wata ranar monday ina kwance adakina ba bacci nake ba amman idanuna a lumshe suke naji saukar hannu a wuyana har ansoma shafamin wuya na zabura na mike zaune ina zare idanuwa wazangani........ mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE