Sashe 135
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN *bissimillahir rahmanir rahim* *hasbunallahu wa ni'imal wakil* page 50 juyowan nan da zai sai dimmmmm naga mutumin yayi wata irin faduwa kasa, yasoma shure shure da kafafuwansa jikinsa na wani irin rawa tmkr mazari, kunfa na fita a bakinsa yayinda gbdy idanunsa sun kakkafe ko bakin cikinsu ba'a gani. yarinyar takaraso da gudu inda yake kwance yana shure shure cikin rawa jiki tasoma furta inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. kafin kace me mutane sun zagayeshi kowa na fadar albarkacin bakinsa akan ciwonsa, yarinyar ta tsunguna gabansa cikin wani irin kuka zata kai hannuwanta duka zuwa jikinsa. wani matashin saurayi dake tsaye kusa dani yayi hanzarin dakatar daita ta hanyar cewa karki soma kai hannuki jikinsa wannan ai mugun ciwo ne ,ba'a kusantar me irin ciwon ko tsallaka inda ciwon ya tashi. cike da matsanancin tashin hankali yarinyar "tace yayana ne fa uwarmu daya ubanmu dashi da zakace kar nata ta'bashi .... kuka take sosai tana kiran "pls yaya ka tashi jama'a ku taimaka min dan Allah "ku kama min shi mushigar dashi cikin mota takarasa mgnr tana kallon mutane dake tsaye makil akanta ita da yayanta dake kwance yana share share da kafafunsa, kumfar na fita daga bakinsa tana gogewa wasu na sake dalalowa . ni kuwa na tsinci kaina tashin hankali mara misaltuwa, iya firgita iya tsorata na tsorata ,ganin abinda ke fita daga bakinsa ,wannan shine Karo na farko dana taba ganin abu makamanci hk. yayinda duk tarin mutane da cike makil zagaye dashi babu wanda yasoma kokarin kusantar inda yake, sai surutai suke zubawa tare da mgnr ciwon. "ni kuwa zuwa lokacin bana iya hangosa sbd yawon mutane da sukayi dandazo agurin, cikin maganganinsu ne na tsinci wani dattijo dake tsaye tare da wata yarinya wace muke depertment daya daita, yana cewa ai wannan kafurtaccen ciwo ne wanda baya tashi tozarta mutun sai cikin jama'a ga da tsoratarwa, wanda samun maganinsa ke da wuya a wannan lokaci, amman idan akayi dace akan samun maganinsa a wani kauye dake cikin idiroko . jikina har lokacin rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,lallai wannan ciwo yaci sunansa kafurtaccen ciwo me tozartar da mutun a bayyanan nasi ,tare da tsoratarwa nayi mgnr cikin zuciyata, ni kaina son karasawa inda yake kwance nake son yi amman tsoro da fargaba ciwon nake ji har cikin zuciyata ga km wani tausayin gayen dake ratsa kowani shashi na gangar jikina,wani irin tausayinsa nakeji yana taso min wanda bansa ni kaina dashi ba . zuciyata da gangar jikina ban rawa babu abinda suke tunda nake banrtaba ganin irin ciwon ba, ciwo makamancinsa ma ban taba gani ba ,duk surutan da mutanen gurin keyi yana shiga cikin kunena daram, ganin duk yawan mutane dake gurin maza da mata babu wanda yayi kokarin taimakawa yarinyar, da ala'mun kowa najin tsoro kamuwa da ciwon ne yasa suka kasa taimaka mata. cike da sanyi jiki nasoma daga kafafona ina ratsa mutane domin kokarin son isa inda yake, nesa kadan dashi naja na tsaya na kasa nakarasawa, amman ina hango yanayin dayake ciki ,hankalina yayi mugu mugun tashi sbd ni da yarinyar kadai bazamu iya taimaka masa ba. matsowa nayi sosai kirjina na wani irin harbawa da sauri sauri, koda na isa nakarasa na tsaya akan gayen, take na tsinci kaina cikin wannan yanayin nadaban tabbas nayi matukar razana dan gane da ciwonsa , dan hk wayata na daga na kira ore aminyata nace dan Allah ta taimaka ta turo min gayun unguwarsu dake zaman banza "nakara da sanar daita abinda ke faruwa nace dan Allah suzo yanzu ko nawane zan biyasu su taimaka min. bayan zuwan yan jagaliyar unguwarsu ore suka taimaka mana nida yarinyar aka daukeshi zuwa cikin motarsa, aka kwantar dashi abayan motar ,yarinyar tashiga gaban motar ni km na sallami yan jagaliyar, nashiga gidan baya inda yake kwance jikina na rawa na daga kansa na daura bisa cinyoyina, yarinyar taja motar aguje muka bar gurin, ahankali na cire dankwalin kaina nashiga goge masa fuska zuwa bakinsa da kunfa ke dalala har wannan lokacin . tun cikin mota yarinyar takira iyayensu bansa me suka fada mata ba naga ta dauki hanyar best step promise dake lagos island ....gudu take sosai ni km ina zaune na tsura masa ido ahankali ina jin sabuwar kaunarsa da sonsa na kara shigata,zuciyata na wani irin tsalle da bugawa raina na raya min abubuwa masu tarin yawa akan gayen, muryata kasa kasa cikin wani irin yanayi nace Allah kabawa wannan bawa naka lfy.....yayinda yarinyar ke tuki tana wani irin kuka cike da matsanancin tashin hankali. cikin minti talatin muka iso hospital tun kafin mu karaso iyayensa har sun isa ,suna cikin hospital din isowarmu keda wuya likitoci suka gaye motar aka shiga kokarin fitar dashi daga motar zuwa kan gadon majinyata, ni km aka barni zaune cikin motar da zance zuci babu wanda ya lura dani . amadadin na fita daga cikin motar nakama gabana, sai nacigaba da zama ina karewa cikin motar kallo tare da tunanin duk yadda akayi wannan matashin dan babban mutun ne duba ga yanayin motarsa suturar jikinsa da yadda likitoci suka shiga rawar jiki dashi, ina wannan tunanin ne ahankali idanuna ya sauka akan wani dan karamin littafi wanda gbdy jikinsa ja ne sai digon zanen ruwa zinari da akayi ajikinsa. cike da matsanancin sanyin jiki da fargaba na kai hanuna na kan litaffin ina shafawa kafin daga baya na dauka ina kallo. tsawon minti goma dauna zaune ina kallo littafin batare dana bude ba, sannan na mayar dashi na ajiye inda nagani, na fito daga cikin motar ina dube dube sannan na kama gabana zuwa gida. daren ranar zaune na kwana sbd tsananin tashin hankali danake ciki ,idan na runtse idanuna da zumar yin bacci sai naga ciwon mutumin yana min gizo da yadda yake shure shure kunfa na fita abakinsa, idan km na bude idanuna wani sabon tashin hankali ne domin wani azabben soyayyarsa ce ke farmakan zuciyata ,hk na raya wannan daren batare dana runtsa ba, sannan babu abinda yazo cikin raina kmr na sanarwa ore abinda ke cikin zuciya sbd ore kawata ce sosai tun secondry school muke tare daita, up to university tare muke sai dai department dinmu daban, ranar da abin ya faru da mutumin batazo school ba sakamakon ciwon kai da take fama dashi. tun asuba dana tashi ban koma bacci ba nashiga gyara koina agidan tare da yin abinci sbd alokacin ni nakewa mahaifiyata komai duk da kasancewata ni kadai da haifa , hkn bai sa ta sangartani ba. ita kanta mahaifiyata ta fuskanci ina cikin damuwa amman sam na kasa sanarmata, gashi jiya tana kallona kwana nayi juyi na kasa runtsawa duk juyin datayi sai taga idanuna biyu, ina gama komai na shirya na nufi gidansu ore. na koro mata halin dana tsinci kaina agame da gayen jiya ,har muka nufi makarata ina bata labari da yadda naji dattijon ya fadi inda za'a samu maganin ciwon. kai tsaye gurin *dorisimi* muka nufa sbd binciko mutumin jiya dana gansu tare . batare da wata shan wahala ba muka gano mutumin, byn mun gaidashi a mutunce nace masa naxo ne akan mgnr dana ji yayi jiya akan inda za'a samu maganin ciwon farfadiya. cike da matsanancin mamaki ya tmbyeni me zanyi dashi ? "tace nace masa nima ina da ciwon ne shiyasa nake son sanin inda zan samu mgnanin, naunayen ajiyar zuciya mutumin ya sauke cike da tausaya naga yana kallona, sannan yashiga karanto min full address din zanbi nasamu maganin yayinda ore dake gefena zaune ta ciro biro da farar takarda daga cikin jakarta tashiga rubutawa. "yace daga nan zaki shiga mota xuwa *songo 'ota* idan kin sauka a sango zaki karasa zuwa Under bridge sai ki tsallaka hannuki na dama ki shiga mota me zuwa idiroko ,sai ki sauka a *ow'odi idiriko* bus stop ,kina sauka zaki ga yan machine ,sai kice gidan alhaji tapa zaki kai tsaye za'a kaiki sbd mutumin ba boyayye bane,yana kaiwa nan yayi min fatan alkhairi tare da fatan samun nasara. muka durkusa har kasa mukayi masa sallama muka wuce. muna kan hanyar dawowa gida ne ore ke ban shawara me zai hana na raba kaina da wannan wahalar...... nace sbd me zatakira aikin taimaiko da tsigar wahala? "wannan ba taimako bane son zuciya ne kike son aikatawa "ta yaya bakisan mutun ba bai sanki ba zakiyi risking life dinki akanshi ?takirara mgnr tana kiran sunana kana ta ja ta tsaya ,nima na tsaya ina kallonta batare dana amsa mata ba . "me zai hana ki hakura da son gayen nan karki saka kanki cikin wahala "akwai maza dayawa a office fa. "bazan iya ba ore dan baki san yadda nake ji bane, ki tayani da addua kawai, byn ina matsanacin sonshi ,aikin alkhari zanyi ,kamata yayi ki karfafa min gwiwa nakarasa mgr tare da yin gaba na barta ,ta biyo byna da sauri tana min mgn har muka shigo cikin unguwarmu shawarar ore take bani akan nabar zance gayen amman furrrr naki, nace naji nagani idan ma dan karta rakani ne, take bani shawara tayi zamanta ni kadai dina ma zani . daidai office 's qsuters muka rabu daita na wuce gida. washegari tunda asubar fari nabar gida da zumar zuwa school ,na nufi *idiroko*, da taimakon address din da'aka bani. byn dogon layin dana iske nasamu ganin alhj tapa. zaune nake gaban alhaj tapa byn nagama koro masa abinda abinda yakawoni gurinsa ya dago da idanunsa dake kan kasar dayake duba, ya kalleni "kana yace me matsayin shi wanda zaki amsarwa magani? bakina na rawa nace saurayina ne wanda zan aura. "ya sunan mutumin da sunan iyayensa nayi tsuru tsuru ina kallonsa kmr yadda yake dubana, sai daya sake maimaitawa sannan nace bansani ba "amman kika ce sauranyinki ne wanda zaki aura ?na girgiza masa kai ala'mun eh. "shine km baki san sunansa ba? nayi shr tare da tsura masa ido kawai alamun rashin gsky . "idan baki san sunansa ba kina iya barin gurin nan yanzu dan aiki bazai taba yiwuwa ba, dole sai da sunansa dana iyayensa tukun zamuyi aiki sbd mahimmanci aikin, domin aikin akwai hatsari sosai acikinsa dan hk kije ki nemo sunansa sai ki dawo kiji