← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 289

Sashe 142

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

acikinsu maman Zainab ce ta daura kanta akirjinta sam ta rude hkn yasanya bata ji numfashinta dake sauka kadan kadan ba. basu kansu ba hatta dady da mninster da suke maza wadanda akasani da dauriya sai da suka fara kuka, shi ak janta yayi ya rukunkumi ajikinsa yana ihun kiran sunanta yana zuba sambatu wallahi bata mutu dogon suma tayi ammi ki tashi karki mutu ki barni wallahi zanyi abinda kike so, zan aureta ki tashi zan aureta duk wanda ya kalleshi zai gane matsawar aka rasa ammi shima tabbas za'a iya rasashi jini ne yasoma fitowa daga bakin ammi da sauri AK mike jikinsa na wani rawa ya dauketa sai mota sanin bazai iya tuki ba yasa minister yasa direbansa yaja motar, motocin . biyar ne suka rufa musu baya, da mata da maza likitoci sunyi iya kokarinsu don suga sun ceto ranta amman ina abin ya gagara sun samata oxygen da na'urorin dan ganin tana raye amman ina har yanzu babu wani abu da zai nuna maka wato tabbas da rayuwarta . minister ya gigice dan yashiga mugun tashin hankali cikin firgici ya dubi tarin likitocin dake zagaye dashi "yace idan aka rasa aunty sam bazan iya dosar wadan nan family da zance mutuwarta ba. daya daga cikin likitocin yace" to yanzu yaya za'a yi kenan ? "wannan ikon Allah ne duk yadda Allah yaso da bawansa hk ce zata kasance dashi ,rayuwa da mutuwa km duk na Allah ne minister ya jinjina kai kawowar wata danja dake jikin na'urar da suka sanya ajikinta shi ya tsayar dasu daga tautaunawar da suke a tsakaninsu, nan minister ya hau hamdala acikin ransa dan ko na'uarar yayi nuni da tana raye bata mutu ba, take ransa yayi masa dadi suka hau nazarin yadda zasuyi ko Allah zai taimakesu . cikin ikon Allah numfashinta yacigaba da harbawa akai akai ,ransu yayi musu dadi nan fa suka shiga godiya ga allah da yayi musu wannan taimako, sun dau lokaci me tsawo akanta suna bata taimako har numfashinta ya dawo daidai dan har ta bude idanunta tayiwa minister mgn daga nan suka fito suka tarar da jama'a cikin zullumi da jiran tsammani. alokacin da minister ya bayyana musu cewar bata mutu ba tana raye hkn yayi musu dadi sosai dan hk tace tana bukatar ganin dady. abdulkabir har ya suma ya bude idanunsa amman sam baya gani ji yayi tmkr numfashinsa zai dauke amman yana jin ance ammi ta farfado har tayi mgn yasa ya mike cikin zafin nama yayi hanyar dakin minister ya sanya hannu ya janyo shi yana kallonsa cikin tausayawa. " yace ka hakura. ba wannan lokaci yakamata kaganta ba da karfi ya fixge hannunsa daga rikon da minister yayi masa ya nufi cikin dakin da ammi take kwance, yana shigowa yayi daidai da har lokacin idanunta a bude suke . yakaraso gareta yana yi mata sannu tare da kamo hannuta cikin nashi ya matse "ammi dan Allah karki tafi ki barni wallahi nayi nadamar kinbi umarninki danake kokarin yi. "amince zanyi duk abinda kika so. ta bude bakinta zatayi mgn kenan tari ya tsarketa, nan tashiga tari babu kaukautawa , "ak ya sake gigicewa ya matso gareta hankalisa a matukar tashe ya kamo ammi jikinsa "kiyi hkr ammina dan Allah ki yafemin wallahi nabi Allah da manzonsa nabiki zanyi duk abinda kike so, ganin tarin yaki tsayawa yasa murtarsa na rawa yace bari naje na kira likita "kabarni abdulkabir yaji sautin muryarta ta fito ahankali ..."kai ..kaine kake son zama silar daura min cuta ,zuwa gurin likitan me km zakayi? "likita bazai taba min mgnin abinda ke damun zuciyata ba ni dai kabarni, kama bar dakin nan gbdy bana son ganinka wani irin kuka ya rushe dashi wanda bakaramin tausayi yabawa ammi ba amman ta daure ta sake cewa kabar dakin nan idan km kafinson ganin mutuwata ne kacigaba da zama. ? mikewa yayi jikinsa na wani irin rawa rawa yabaro dakin karo sukayi da dady dake kokarin shigowa dakin dady yakamo hannunsa yana shafa kafadarsa yana cewa kayi hakuri abdul in Allah ya yarda amminka zata samu sauki . "kai dai kayi kokari kayi abinda zai kwantar mata da hankali, mahaifiyarka tana bukatar taimakonka ita din abar tausayi ce bata da kowa byn ku 2 da Allah ya mallaka mata sai danginta. wallahi dady zanyi duk abinda ammi take so zan aure su'ad matukar shine farincikinta shikenan ka kwantar da hankalinka . kwanaki 2 ammi tayi asibiti km cikin ikon Allah ta samu sauki amman kallo daya zaka mata kasan ta sha wuya ba yar kadan ba ,duk ta firgice ta fita haiyacinta, hk ma dangi dady hankalinsu ya rabu gida biyu wasu na asibiti tare da zeey wasu na gurin ammi . bangare su'ad kuwa rana da suka koma gida kasa runtsawa tayi gbdy ta kasa samun natsuwa hk ta dinga juyi agado sbd yadda soyayar abdulkabir ya dinga mata yawo a gbdy sansar jikinta sai zabure zabure take tana kuka jikinta yayi wani irin zafi kmr gawarshi, ummanta ma bata samu runtsawa ba ,sbd duk motsin su'ad din akan idanunta ne dan hk takoma kan gado inda su'ad ke kwance ta dagota tana share mata hawaye sannan ta rungumota zuwa jikinta tana shafa bayanta har sai da tayi shiru daga bisani ta saketa tare da zuba mata idanu tace "nasan har yanzu kina son abdulkabir ko su'adullahi ? su'ad tayi saurin girgiza mata kai ala'mun a'a. "karki ce min a'a nifa mahaifiyarki ce nasan kina son shi sosai , amman kmr yadda kika gaya masa kin rabudashi har abada ,ina son hkn ya zauna acikin zuciyarki domin kare mutuncinki . "karki dauki mgnr dana fada agaban iyayensa da wani tasiri sbd bazan taba miki auren dole ba duk runtsi duk wuya wanda kika kawo kika ce kina so shi zanbaki matsawar na yaba da nagartarsa zan barki ki aureshi? dan hk ki kwantar da hankali ki cire wannan damuwar. umma ta kamota suka kwanta kowane zuciyarsa cike da matsanancin tunani. a asibiti ammi ta nemi ganin minister akan tana son ya kara mata haske akan saleema bai boye mata komai ba ya tabbarta mata saleemar taufeek ce km su'ad diyarsa ce ai jin hk yasa ammi sake samun lfy da natsuwar zuciya wanda duk ya ganta ya san tana cikin farinciki . ammi zaune akan gadon hospital AK zaune daga gefen hangunta ,eiman akan kujera agabanta tana bata abinci abaki yayinda sauran mutane na zaune har da zeey wace ta fito byn kwana biyu da wuce suna hira kadan kadan. dady ne yashigo dakin bakinsa dauke da sallama gbdy suka hada baki gurin amsawa zeey cikin rawar jiki ta mike daga kan kujerar datake zaune ta mika masa ya zauna tare da cewa "abdul kunna TV can. ahankali ak ya mike yaje ya kunna tv ya dawo ya zauna yana mikowa ammi ruwa tare da maganinta, kunna TV ke da wuya wani malami islama ya bayyana yana magana akan cututtukan zamani kama daga hawan jini ciwon suga koda ciwon zuciya ciwon hakori asma har zuwa kan farfadiya.. ai jin hk ke da wuya ammi dake kokarin watsa koyoyin magani abakinta ta fasa ta ajiye take km jikinta ya dauki rawa, cikin rawar murya "tace eiman abdul ku daukar number wayarsa cikin sauri suka soma daukar number wayarsa har zeey wace batasan abinda za'a yi da number wayar ba yayinda me maganin rahmaniyya yacigaba da bayanin magunguna da yadda illolin ciwon ke nakkasa jikin dan adam. satin ammi daya aka sallamota daga hospital . mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 142 · 0% Book details