Sashe 140
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da zasu tayani . dukkaninsu daga ita har ore babu wanda nagayawa abinda nayiwa AK ta wajen nemomasa lfyr jikinsa sbd sharadin alhj tapa daya gindaya min. aiko ganiya ta tattaro min duk wasu gang din yan'iska dake munshi olosha muka shiga aiki neman yadda zan rabashi da zeey tare da karuwarsa onye..... gama bada labarinta ke da wuya su'ad ta mike tsaye domin isa inda ummanta ke zaune tmkr an dasata agurin gbdy ta dawo mutun mutumi agurin azaune tana kuka tana al'ajabin abinda su'ad ta aikatawa rayuwarta ,aiko tafiya daya biyu tayi sai luuuuuu ta zube kasa tasoma rawar jiki irina masu cutar farfadiya tare da shure shure kunfa na fita daga cikin bakinta. umma ta zabura ta mike tayi kanta zata kai hannunta ammi tayi saurin dakatar daita, da sauran mutane dake kokarin kai hannusu jikin su'ad sannan cikin rawar jiki ta nufi dakinta shima dady ya nufi cikin dakinsa. maganin da suke yiwa abdulkabir amfani dashi suka dauka cikin sauri suka dawo parlour'n suka shiga rige rigen yi mata amfani da maganin lokacin AK ji yayi kmr kasa ya tsage ya nutse ciki ya huta da kunya tare da ganin wannan tashin hankali dake faruwa agabansa, wani irin ya dinga ajikinsa lokacin dayake kallon su'ad cikin yanayin cutar farfadiya. " yanzu hk yake kasancewa a duk sanda wannan dan iskan ciwon ya tasamarsa? yayiwa kanshi tmbyr yana takaicin ciwon. sauran mutane da suke gurin tsaye suke kan su'ad suna karanto mata addua ,sai data dauki sama da awa daya tana shure shure sannan ta farfado bakinta dauke da adduar dataji mutane na karanto mata ,sannan ta fashe da wani gigitaccen kuka kafin ummanta takarasa gareta har ammi tarigata tare da kamota zuwa jikinta tana shafa bayanta sannan ta nufi kan kujera ta zauna tare daita ta kwantar da kanta bisa cinyoyinta tana kukan me cike da tausayawa rayuwarta. ahankali ammi ta daura hannuta bisa sumar kanta tana shafawa tana sake zubda hawaye . tsawon min 15 su'ad tana kwance bisa cinyar ammi tana jin wani farinciki from know where yana bin gangar jikinta kana ta yunkura ta mike jikinta tmkr ba nata ba ta zauna tana duban dukkanin mutane dake parlour 1 byn 1. lokacin da ta gama farfadowa commission ya dubaita "yace kinyi ganganci akan mutumin da bai ce yana sonki ba ki tashi kije har wata uwa duniya nemammasa magani cutar farfadiya ,sanadiyrsa kika tsinci kanki bursuna har na tsawon shrkaru 3 byn shi yana da ma wace yake so har sun kusan yin aure. "amman kin san kin tafka babban kuskure arayuwarki ko? "cikin tashin hankali ta bude bakinta tace ehhh.. "amman dolensa ya aureni . "na yarda na zamo kota biyu ce... bangaren ak kuwa shiru yayi tare da zabga uban tagumi yana kallon su'ad domin rasa abinda zai ce mata yayi, shi fa a yadda yake ji ko me za'a yi bazai iya aureta ba sbd baya jin sonta . ahalin yanzu zuciyarsa zeey kawai take matsanancin so, amman sbd abinda tayi masa bazai iya kallon tsabar idanunta ayanzu yace bai sonta ba . ahankali muryarsa atsanake ta fito gurin cewa naji dukkanin bayaninki km na gode sosai bisa kasadar tsaida rai da rayuwarki da kikayi akaina . "amman abinda nake so dake shine kiyi hkr ki ajiye mgnr aure atsakaninmu ,kinga ahalin yanzu ana tsaka da hidimar aurena da wata amman zan baki million goma kije ki fara sabuwar rayuwa. " km duk lokacin da kike bukatar wani taimako daga gareni a shirye nake da na miki shi ko wani iri ne... ina rokon Allah ya baki naki mijin wanda yafini amman ni abdulkabir ba wai dan bazan iya aureki ba, sai dan bani da ra'ayin auren mata biyu.. take jinta ya dauke dif ta daina jin komai dayake cewa, zuciyarta ma ta tsaya cak ta daina bugawa na wucin gadi kafin daga baya zuciyarta tacigaba da bugawa da sauri sauri na nan take su'ad tasoma kuka har da shesheka lallai ta tafka babban kuskuren kmr yadda commission ya fada . ta banzatar da rayuwarta akanshi, tayi zaman gidan yari akanshi ,ta kamu da cutar farfadiya duk akanshi daga karshe zata kasance zero batare da taga gudan jininta duniya ba.. .. jama'ar dake zaune a parlour'n kuka suke sosai barin ma ammi da umman su'ad wadanda tun sanda su'ad ta dawo haiyacinta basu sake cewa komai ba. AK ya fuskanci commission sosai sannan "yacigaba dady abu na karshe da zance a gaya mata shine aja mata kunne karta kara zuwa inda nake ko inda mamata take .....taje tayi rayuwarta nima ta barni bayi rayuwata amman zance aure babu shi. "you see ur life inji cewar commission dake zaune yana duban inda su'ad take ransa a matukar bace dan jin haushin abinda AK ya fada . "yanzu kinga karshen rayuwarki ko? "yanzu wa gari ya waya? su'ad naga jin abinda abdulkabir ya fada jikinta ya dauki rawa ahankali ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido sannan tayi murmushin gefen bakin wanda da gani kasan na bakinciki ne. batace masa komai ba ta isa inda ummanta ke zaune ta hade kanta da gwiwarta tana wani irin kuka.."ummana takira sunanta cikin rauni da sanyi murya "kiyi hakuri nasan na sabawa ubangijina sannan nayi miki ba daidai ba. "amman gashi tun a duniya allah ya nuna min iyakata ta hanyar jarabtata da maseefu iri iri,. "na nemi gafarar ubangiji bisa hadasa danayi da waninsa alhalin yace kada a hadasa da komai agurin bauta . "a yanzu gani agabanki ina rokonki ki yafemi duk da nasan ke din uwace guda har da rabi me yawon yafiya gareni .. "kece komai nawa umma banida kmr ki duk duniya kece kika kawoni duniya har nasan koni wacece amman naci amanarki da amanar tarbiyar da kika dauki tsawon lokaci kina bani akan "da" nmj, wanda bai dauki abinda nayi masa abakin komai ba, har yana ganin kudi shine sakayyar datafi dacewa dani ... "kiyi hakuri kice kin yafe min ummana ko zanga daidaita arayuwata...umma kuka su'ad kuka hatta commission da sauran mutane kuka suke sosai . umma ta dago idanunta da suka gama rikidewa suka koma tmkr garwashi wuta ta daurasu bisa fuskar tilon diyarta hawaye na sake bin kuncinta.. "na yafe miki diyata duniya da lahira da albarcin annabi muhammadu (saw) zakiyi albarka arayuwarki zakiga daidai arayuwarki . "ina adduar Allah ya rabaki da wannan cutar farfadiya data sameki "ba yau nasaba daukar kaddara ba. " kaddara acikin jinina take km zan cigaba da karbarta a duk yadda tazo min Allah yabani ikon cinyeta. tana karasa fadar hk ta mike tsaye tare da rike hannun su'ad cikin nata suka soma tafiya domin kokarin barin parlour ammi ta mike jikinta na rawa tare da dakatar daita baiwar Allah umman su'ad taja ta tsaya dan jin abinda zatace. ammi takarasa gaban AK ta tsaya tana masa wani irin duba muryarta na rawa "tace abdulkabir bakada imani balle tausayi "yanzu abinda yakamata ka gaya yarinyar da tallafi rayuwarka kenan? "me zatayi da kudin din banza da wofi kasani ni mahaifiyarkace wace tayi silar zuwanka duniya a yanzu ina baka umarnin auren yarinyar.... ammi takarasa mgnrta tana nuna inda su'ad take tsaye da hannunta... umman su'ad ta juyo ahankali tana kallon ammi, take zuciyarta ta kismamata ammi tayi wannan mgnr ne da wata manufa,killa kodan kasancewar fuskar da su'ad din ke dauke dashi ne.... dan hk tasoma karasowa har inda ammi take tsaye . "hjy karki damu balle ki takura masa kan sai ya auri diyata dole. "no no karki takura masa , sbd ni kaina bazan taba amincewa yarinyata ta auri mutun irin wannan ba me zanyi da suruki irinsa ........ mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE