← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 289

Sashe 169

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *Allah messenger saw said a strong believer is better and dearer to Allah than a week one* Not Edit page 59 ammi wace gbdy ta sake shiga damuwa akan halin ko in kula da AK ke nuna musu daga ita har su'ad , yanzu hk zaune take akan gadonta tana tunani ,byn takirasa a waya akan yazo tana son ganinsa , tacigaba da zaman jiran karasowarsa har tsawon minti talatin amman bashi ba ala'munsa . dan hk yasa ta yunkura mike ta fito daga cikin dakinta xuwa parlour 'nta da niyyar shiga part din dady . daidai wannan lokacin ya shigo cikin parlour 'n bakinsa dauke da sallama dakatawa tayi lokacin data ganshi tana dubansa sannan takarasa tasamu guri ta zauna akan daya daga cikin kujerun parlour tana cigaba kallonsa sbd katuwar ramar dataga yayi. da saurinsa ya karaso gareta ya zauna agabanta ya takwanshe kafafunsa yana dubanta tare da son yin mgn amman kafin yayi mgnr tayi saurin cewa " anya kuwa abdul kana yiwa kanka adalci arayuwa? "anya kuwa akwai imani acikin zuciyarka? "kwana da kwanaki bakayi tunanin lekowa zuwa inda muke ba balle kasan halin da muke ciki "yanzu in ba wani kwakwarar dalili bane ko ciwon su'ad ne ya tashi sam baka son xuwa inda muke , "haba abdul hb abdulkabir muma fa muna da haki akanka a matsayinmu na iyayenka sannan ga hakin matarka akanka amman duk wannan bai sa mu cancanci kazo ka duba lafiyarmu ba. ahankali yaja numfashi tare da ajiyar zuciya ya fesar atare yana shafa sumar kanshi kana yace "ammi ba hk bane wallahi amman kiyi .... "to menene dalili idan ba hk bane uhm abdul? ammi ta katsesa tana tsareshia da idanunta,tana kare masa kallon tsab. gbdy duk ya rame ba kmr kwanakin baya ba .... numfashi ya shaka ya sake fesarwa ahankali kana muryarsa a matukar kasalance yace "ammi ina son zuwa gidan amman nakasa jurar nazo banga yarinyar can ba "wace yarinyar kenan kake mgn akanta? ammi ta tmbysa wanda sarai tasan ko wa yake nufi. muryarsa a matukar sanyaye yace "su'..ad yabawa ammi amsa da hk muryarsa na shaking , sannan muryarsa ahankali yacigaba da mgn "ammi ke uwa ce nasan kin fahimci wani abu a tattare dani wanda ya dangancin yarinyar ,narasa yadda zanyi da rayuwata "ammi narasa me ke damun tunanina akanta duk inda na motsa tunaninta . "cike da matsanancin bacin rai ammi tace "wai abdul har yanzu wannan busashen zuciyar taka bazatayi nadama ba ka rungumi kaddarar data zo maka . "da sauri ya dago mayattun idanunsa yana dubanta dasu tare da katseta ganin kmr bata fahimcesa ba, "ammi ba fa hk bane wallahi nasoma jin wani sauyi ne akan yarinyar wanda hkn ya haddasawa zuciyata shiga rudani gbdy tunaninta ya hana zuciyata sukuni shiyasa ma danaga bata kaunar ganina ahalin yanzu nima na kauracewa gidan amman ina ...ina... sai km ya kasa karasa mgnr wanda hkn yayi daidai da lokacin da su'ad ta sanyo kai tana kokarin fitowa daga cikin dakin eiman,jin furucinsa yasa taja da baya ta tsaya cak tare da boyewa cikin labule, gabanta na dukan uku uku take jikinta ya dauki rawa ta kamkame jikinta guri daya zuciyar na tsananta bugawa da sauri sauri wayyohhly kar kayi shr pls ka fada kace kana sona ...... . duk da bataji farkon mgnrsu ba amman taji karshen mgnrsa ...... dan lekowa tayi da idanunta daya ta yadda bazasu ganta ba, taga me ya dakatar dashi cigaba da mgnrsa amman sai gani tayi ya runtse idanunsa gam yana ciza gefen lips dinsa na kasa da karfi . ahankali idanunta ya sauka kan ammi dake zaune tana murmushi jin dadi wanda ta kasa boye farincikinta a fili da jin furuncisa, abinda ta dade tana zargi akansa ne km ta dade tana jiran ranar tabbatuwarsa , cikin matsananci farinciki ammi tace"banda abinka abdul meye a ciki dan ka kamu da matsanancin tunani su'ad ji nake su'ad din matarka ce km mallakinka wanda duniya ta sheda hkn ,ka kafi kowa sani irin tsaftatacciyar soyayyar datake maka, akanka ta sadaukar da rayuwarta da farincikinta , bai kamata ka tsaya bata lokaci ba gurin fahimtar daita ba, sai ka sanar mata da yadda kake jinta tayi masa mgn a bai bai kmr yadda shima yayi mata . marairaice murya yayi sosai yana me dukar da kanshi kasa"ammi ai wannan zance da ne ,amman yanzu su'ad ta daina sona kwata kwata bata kaunar ganina, ko baki ga yadda take min rashin mutunci ba a duk sanda muka hadu nima fa ba wai sonta nake ba kawai dai tunaninta ke addabar rayuwata amman da zaki taimaka kiyi mata mgn ta daina nuna min kiyayya ta dawo nuna min soyayya kmr yadda take min ada hkn kawai zai kwantar min da hnklina har na samu natsuwar zuciya. " wayyohhly Allah su'ad ta furta a fili tare da dafe daidai saitin zuciyarta da hannuwanta duka tana runtse fararen idanunta . "zaro ido waje ammi tayi tana kallonsa tare da cewa "ni din zan mata mgn? "lallai baka da aiki kaga ma tafiyata idan kaga tunaninta na neman halakaka zaka bude baki ka amayar da abinda ke cin zuciyarka ,"ni dai ka dinga zuwa ina sanyaka cikin idanuna. "wayyo Allah ni da yakamata na fito a mutun dina sak na bayyanawa ammi komai ko zata taimakamin, shine na tsaya wani kona kwana yayi mgnr cikin ranshi yana sake shafa sumar kansa idanunsa na kallon ceiling parlour 'n.... cikin hk yaji motsin fitowar su'ad daga cikin labulen dakin eiman tana auna masa wani irin kallo me firgita zuciya wanda yasa take yasha jinin jikinsa har gabansa ta karaso ahankali cikin sanyi tafiyarta me kama da tafiyar tsutsa ta tsura masa fararen idanunta tana kallonsa gbdy tarasa me yakamata tace masa, dan ji tayi kmr ta rufeshi da duka tsabar takaicin abinda ya gayawa ammi wai ba sonta yake ba alhalin ita tasan son ranshi kawai ya fadawa ammi dan kallo daya zakayi masa ka gane yana cikin shaukin kaunarta . kallonta yake kmr yadda ta tsareshi da ido kafin daga baya muryarta a matukar fusace tace "makaryaci kawai......... sannan ta juya da sauri tabar gurin sbd kukan da yayi yunkuri kwace mata. zaro idanu waje yayi sosai tare da bin byn da kallo cike da matsanancin mamakinta , zaune kawai yake a gurin amman gbdy ilahiri gangar jikinsa sunyi masa sanyi ji yayi kmr ana masa wanka da ruwan kankara ne "kardai taji hirarsu da ammi ? no no bata ji ba , nan fa yashiga comfuse na taji mgnrsa ko bata ji ba ,ya kasa motsawa daga zaune dayake illa gumi dake ta aikin keto masa a ilahirin jikinsa yana gogewa wasu na sake tsatsafowa, jikinsa a matukar sanyaye kmr yabita dakinta ya tmbyeta kotaji hirarsu ne amman yaga kmr zai kwabsawa kanshi idan ya aikata hkn dan hk yacigaba da zama cike da fargaba . koda tashiga dakin, rufe kanta tayi ciki ta fada saman gado ranta duk babu dadi tunani ne ya addabi rayuwata can km tasoma rizgar kuka me taba zuciya da tsayawa arai "why why why!!! abdul ? "meyasa bazaka soni koda kuwa bazai kai kwatankwacin wanda nake ba? "me ye laifina "meye aibuna pls arayuwa da bazaka soni ba ....kuka take sosai har da shesheka kmr ranta zai fita daga gangar jikinta kafin daga baya ta rarrashi kanta da da karfafa zuciyarta cewar yana sonta tunda tunaninta ya hanashi sukuni da wannan karfin gwiwar tasamu natsuwar zuciya tare da mikawa Allah lamarinta ta mike ta fada bathroom tayi wanka, ta canza kaya zuwa wasu haddaun kananun kaya riga da siket piny da ratsin baki baki ajiki ta yafe kanta da bakin mayafi ta sake fitowa parlour duk da yanayin da take ciki na kunci da bakincikin furucin AK amman hkn bai hana sihirtaccen kyawunta fitowa ba coz she look attractive zaune ta tarar da AK inda ta barshi batayi magana ba hk zalika shima baiyi mata mgn ba, sai dai yayi matukar damuwa da kalmar makaryacin data furta masa kalmar ta damesa tare da tsayawa a kahon zuciyarsa ,yana jin kmr ya zalincetane ta kowani bangare yasa ta furta masa hk . yayinda ya dinga ji ajikinsa kmr bata cancaci zalinci daga gareshi ba, yana kallonta ta wuceshi zuwa dining yabi bynta da kallo ta ja kujera ta zauna ta debi abinci a plet tasoma ci . alokacin dayake kallonta tana cin abinci kmr bata son ci ji yayi kmr ya isa gareta ya rungumota zuwa jikinsa yabata abinci yasanar mata da sirrin dake boye acikin zuciyarsa amman ya kasa aiwatar da hkn sai gyara zama da yayi yana kallonta yana hadiyar yawu . ahankali ya mike tsaye daga zaunen dayake cikin takunsa na isa ya karasa har dining inda take zaune tana tsakurar abinci ya tsaya bisa kanta yana kallonta, tayi tmkr tabasan da tsayuwar wani bil'adama agurin ba, ta sake debo abinci zata kai bakinta kawai taji zaraf ya rike mata tsintsiyar hannuta still idanunsa na kanta yana kallonta, ta dago fararen idanunta masu kalar madara da suke cike da matsanancin rudani da takaicinsa ta zubesu cikin kwayar idanunsa wanda hkn ya saukar masa da tarin kasala ajikinsaa har yanayinsa ya tsananta bukatuwa ,take feeling dinsa yasoma motsawa ahankali ahankali yana cigaba da kallon cikin idanunta yana jin yadda wutar kaunarta me tattare da tsagwaron sha'awarta ke taso masa yana circulating gangar jikinsa . tsawon minti goma ya dauka rike da hannuta yana kallonta sbd bakaramin kyau tayi masa ba cikin kayan dake sanye da jikinta batare da wani tsoro ko fargaba ba ta tsurawa cikin idanunsa nata kwayar idanu tana narkar dasu hk kawai take ji ajikinta lokacin nadamarsa ya kusa..... lokacin tunon sililin zuciyarsa yayi domin kuwa ko yaki ko yaso ya kamu da matsanancin kaunarta furtawa ne dai bazai yi ba, yayinda ita km ta tabbatarwa kanta sai ya furta wannan kalmar da bakinsa koda kuwa abinda zai aikata karshe kenan numfashinsa ya bar gangar jikinsa amman sai ya furta mata kalmar so.... yadda take kallonsa din nan tasan bazai taba iya tserawa soyayyarta ba koda kuwa zata furta bata sonshi ne. lumshe mayatattun idanunsa yayi yana me bude bakinsa da kyar
Chapter 169 · 0% Book details