← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 289

Sashe 139

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sake tsoratani na fidda rai da tsammanin kubuta daga tarkonsu . "a hankali muke daga kafafunmu domin sauka kasa inda motar black mariya ke zaman jiranmu kawai naga daya daga cikin yan fashin nan ya arta da matsayacin gudu yana sauka akan step, ai take ihu da kururuwa ya cika koina a koto yan'sanda dake kai kawo a sorrounding gurin suka mimike tsaye tare da rufe kowace hanya dake cikin kotu ,ai barawon nagama saukowa kasa yaga an kulle koina na sorronding gurin, bai tsaya wata wata ba kai tsaye ya nufi katangar company din guineas dake manne da katangar kotu ya haura. ai nan police suka bishi aguje wasu suka zagaya suka shiga cikin campany ... cikin minti goma sai gashi sun kamoshi sai dai yaci uwar duka har bai iya daga kafafunsa ga jini daya rufe kanshi yana tsiyaya ... cell din dake cikin koto aka wuce dasu ni km aka hadani da police sbd sai yamma zamu koma prison, anan zamu yini tun abinci daren jiya ne acikina gashi idan baka nan bakada abinci km ko ansan kana kotu baza'a ajiye maka ba, sannan a kotun ma ba abincin zakaci ba.. "akalla duk byn wata uku sai mun ziyarci kotu gashi har na kai tsawon shekara daya cikin ta biyu mahaifiyata batasan inda nake ba. ana gobe zamu kotu muke zantawa atsakani yan dakinmu da makotan dakinmu inda akwai wadan da gobe inda munje kotu bazasu dawo cikinmu ba, kasancewar wa'adinsu yacika. nan duk wani me sako tsakaninmu yabasu zuwa ga danginsa , ciki kuwa har dani danabawa bukky sakona zuwa ga ore aminiyata. daren ranar kam nayi kuka sosai ina ji ina ma nice zanbar gidan yarin, su kuwa tsabar rashin jin mgn irin tasu da taurin kai "cewa sukayi dama an barsu sun cigaba da zamansu "menene babu acikin gidan yari"duk fa abinda muke so shi mukeyi babu matsi babu takura "muna waya muna shaye shayenmu yadda ranmu keso "to meye km yayi saura? "ni kam cewa nayi har duniya ta nade bazan taba zabar zama cikin gidan yari ba ,kai ko abinda zai sa na sake dawowa gidan yari bazan aikata ba. dry suka kwashe min dashi suna nuna da hannunsu, daren ranar kasa runtsawa nayi inaji kmr nice zan bar gidan. munje kotu wannan karon har da su ganiya wanda shari'ar mu tazo daidai datasu ,byn angama gabatar da shari'arsu aka shiga tamu wace babu wani ci gaba acikin shari'a tamu , sai bakinciki tare da bada kwanan wata da zuwa kotu bisa gaida . me shari'a ta mike byn tagama watsa mana tsadaddun turancinta muka fito daga cikin kotu zuwa harabarta kotu inda dandazon mutane suke . "wasu a zaune wasu a tsaye kowa kagani agurin sha'ani gabansa yake ,yayinda wasu kana kallonsu kasan cikin tashin hankali suke dan zakaga har kuka suke sbd masefar tashin hankali dake cikin kotu . muna zaune inda aka saba barinmu a duk sanda mukazo kotu. zaman dana saka masa suna da jiran tsammani ,muna kallon yan'uwansu bukky suka karaso garesu suka rungumesu suna murnar an sakosu ,. "alokacin babu abinda yaxo raina kmr ummana ita kadai nake so da kwadayin sanyawa acikin kwayar idanuna dan gbdy tashin hankali danake ciki yasa na tattara soyayyar abdulkabir na ajiyeta agefe nafi jin tausayin mahaifiyata , domin nasan tana can cikin tashin hankali rashina har na tsawon lokaci. ba'a cike wata biyu ba da tafiyar su bukky ina zaune naji ganduroba na kirana na mike cike da mamaki, domin lokacin shine karo na farko dana ji an anabi sunana da sunan anzo nemana . ahankali jikina a sanyaye nabi bayansa har zuwa cikin wani office. ore nagani zaune tana ganina ta mike tsaye jikinta na kirrma ni km sai hawaye sharrrrrr ta karaso gareni ta rungumeni ajikinta tana kuka "a she da gaske ne su'ad kina prison? "cikin kuka nace gaske ne ore gani kuwa agabanki acikinsa. "ya ummun su'ad take? nayi mata tmbyr ina kokarin barin gangar jikinta domin son sanin halin da mahaifiya take. "tana lfy ko yanzu kafin nazo sai dana biya gurinta km na sanar mata da gurinki zanzo har tayi adduar Allah yasa bake din bace a prison kmr yadda sako yazo mana. wasu zafafan hawaye suka sake zubo min. na runtse idanuna domin rasa abinda zan ce "garin yaya su'ad ? "garin yaya kika tsincin kanki cikin halin robboling? "kaddara ore "kaddara ce silar meidani hk km kin gaya min gsky nakiji . "a she shafuffukan rayuwata suna tattare da kaddarori bansani ba. "danasan hk zan tsinci rayuwata dana dauki shawarki kingan ni nan cikin prison da sunan robbiling akan soyayyar abdulkabir. minti 15 akabamu mu gana daita gasu har sun cika batare da hirarmu tayi tsawo ba domin har ganduroba yakaraso bisa kanmu ya tsaya yana bani umarnin komawa ciki ,itama yana bata umarnin wucewa. ina kallonta taciro kudi akalla zasu kai dubu biyar ta miko min na girgiza mata kai "ki bar kudin ore basu da wani amfani gareni hannuna ta janyo ta tura kudin ciki ta rufe ki amsa zasu miki amfani, ta juya tana kuka kafin nayi hanzari har tabar gurin nan nima na fashe da wani gigitaccen kuka, ganduroba ya matso inda nake tsaye tare da miko min tafin hanunsa ala'mun na bashi kudin, take babu musu na mika masa nasoma daga kafufuna zuwa cikin dakunanmu. tunda ore ta tabbarwa ummana Hali danake ciki ta tashi hankalinta, tayi kuka sosai har kukan ya janyo mata ciwo me tsananin a yadda ore tasanar min a wani zuwa datayi gurina . zanga zanga ummana tashiga neman yadda zata fitar dani daga prinson, duk kudaden gidan hayar gadona wanda mahaifina ya barmin babu wanda bata amsa ba domin kubutar dani amman babu biyan bukata lawyer's sai dai su amshe mata kudi su dinga mata yawo da hankali tare da saka mata rana, ahaka a wani zuwa da ore tayi gurina take gayamin yadda abubuwa ke tafiya. "nace tagaya mata tabar hasarar kudinta ta'ajiye watakila gaba suyi mana amfani ta min addua kawai domin shi nafi bukata daga gareta ahalin danake ciki. "na kara dace mata ta duba jakar school dina akwai wani diary ciki duk randa zata sake zuwa tazo min dashi duk . sati daya bata cika ba ta sake kawomin ziyara tazo min da littafin sirrin abdulkabir, cikin na duba naga cikakken address dinsa nataba nace ta binciko min komai akansa da halin dayake ciki . kullun da tunanin mutun biyu nake kwana nake tashi arayuwta mahaifiyata da abdulkabir burin raina yayinda kullun kwanan duniya zazzafar kaunarsa ke sake wanzuwa acikin zuciyata. duk sanda ore takawo min ziyara sai na tmbyeta lafiyar mutun 2 mahaifiytata da lafiyar abdulkabir dina tace min duk suna lafiya . hkn ne ke dan kwantar min da hnkli. lokacina dana cike shekara biyu cif na gahurta acikin prison har nazama shugabansu ganinya gurinn shaye shaye da harakar dabanci babu wanda ke kawo min rainin wayo ,wani irin karfi nake ji ajikina kmr shara'A bana jin tsoro kowa duk girmanka sai natakaka, wanda lokacin har gasar fada muke yi atsakaninmu km nice nake lashewa, ni kaina idan ina yin wasu abubuwan mamaki kaina nakeyi nasha sigari na sha wiwi wanda duk acikin prison muke samu . "wani lokacin ma ganiya kan bani shawarar me zai hana idan mun fito daga prison nayi join dinsu cikin harakar fashi. sai dai na kalleta kawai nayi dry ,rayuwa cikin prison agurina babu dadi sabanin gurin su ganiya da gang dinta domin su sun meida gidan tmkr gidansu sbd yawon kawosu cikinsa da ake. dan wannan zuwan nasu ba shine zuwansu na farko ba sun shasha zaman yari. muna samun abinci amman ba ishashe ba ,dan wanda ake bamu baya wani isarmu abinci ne gashi nan kmr loma acikin plet gashi always Bean's ne. sannan ana yawon kawo mana ziyara lokaci zuwa lokacin. akwai wani malami daya taba zuwa kawo mana ziyara ya gani ina shan tabar wiwi hankalinsa yayu mugu mugun tashi yashiga min wa'azi tare da jamin ayoyin alqurni me girma abinda yabashi mamaki bai wuce yadda duk ayar daya ja ba, zan amshe na karashe .. ya dade tsaye yana kallona sannan yashiga tmbyata dalilin xuwana gidan yari? " kai tsaye nace masa kazafin sata akamin batare da nasan yadda ake yinta ba... nan shima yace zaiyi iyakacin bakin kokarinsa gurin ya fitar dani daga prison . da zai tafi nace masa "ya taimaka idan zai sake dawowa yaxo mana da kayan abinci sbd dayawa daga cikinmi suna son yin axumi amman rashin wadatacen abinci ke hanasu yi. nagaya masa hkn ne sbd lokacin watan axumin ya karato km duk lokacin azumi ina ganin yadda suke wahala daga karshe ajiye azumin suke . ya tabbar min da zai yi bakin kokarinsa da yarda allah . " zance taimakon abinci kam ya tabbata domin tirala guda akayi na kayan abinci iri iri , ba prison din danake ba hatta na gefenmu sun cin albarkacina . zance taimaka min da malamin yace zaiyi ne ya sha ruwa domin shi kansa babu irin shige da ficen da baiyi ba dan ganin na fito amman abu ya gagara. dan hk na dauka shima rashin fitowar wata kaddarar sakamako ce gareni na sabawa umarnin mahalicina danayi.. akwana a tashi babu wuya har ka'idan da kotu tabani tacika na fito tare da su ganiya muna munar wanda ni duk nafisu murna. akan hanyarmu daga kiriri zuwa oshodi muke bawa juna addrshin gidanjenmu sannan na tabbatar musu matsawar basu bar harkar fashi da makamin ba, kar suyi kuskuren tunkarar inda nake suma mance munsan juna . ganiya ta tabbatar da sun daina bazasu sake aikata hkn ba , a daidai under bridge din oshodi muka rabu da junanmu nashiga motar me xuwa ikeja su km suka shiga motar me xuwa munshi ol'osha... ina fitowa daga prison nasoma kokarin haduwa da abdulkabir dina kwasma ore take sanar min ai aure zaiyi abinda yasa bata sanar min ba tun ina prison ba bata son nashiga damuwa akan wanda nake ciki. to tunda daga wannan ranar da ore tasanar min nasoma nemo hanyar da zanbi ganin ni kadai bazan iya ba, yasa na nemi taimakon ganiya nace ina son tabani goyon baya akwai aikin
Chapter 139 · 0% Book details