Sashe 131
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
zauna yana huci dan cewa yayi sai ya mata illar da har ta mutu ba zata manta dashi ba ... shi kansa commission ya dade baiga mace me taurin zuciya irin su'ad ba, ya sallemi umma yace ta wuce gida zai nemata . "bazani koina ba commission duk abinda za'a yi ayishi agaban idona ,yarinyata tayi laifi km ta amsa laifinta har ta bayyana inda yarinyar take an daukota "me zai hana abani beling diyata na wuce gida daita? "idan km zamu shiga koto ne to? "duk mgnr bai kai ga hk ba amman yanzu zamu so musan sbd me su'ad din ta sace amaryarsa aranar kamunta sannan musan abinda yasa take bibiyar wannan yaron? "ni nasan halin yarinyata hk kawai babu wani dalili bazata dinga bibiyarsa ba ,kai dai tmbyi shi wannan mara kunyar ko akwai abinda yayi mata.. karki fada hk domin idan kikace hk ya nuna ala'mun kina bin goyon bayan diyarki da daure mata gindin yin duk abinda tagadama which's bad.. "ga ta nan agabanka ka tmbyeta tunda nake da su'ad ban taba cewa ta aikata mugayen ayyuka ba, kullun fada da addua nake mata, duk uwar arxiki bazata so diyarta ta dinga abinda su'ad takeyi ba ,nasan bata da gsky acikin lamarin amman tunda ta amsa laifinta ai ina ganin komai zaizo da sauki tunda ko koto akaje alkali zaiyi saurin zartar mata da hukucin da yadace . "ok yanzu dai kije gida domin musamu muyi binciken dayakamata akan aikinmu kina kallo tun awa uku nake fama daita amman taki bani hadin kai. babu inda zani commission zan dai tsaya a kasa najira har lokacin da zaku gama sannan matsawar wannan dake huci kmr maciji ya illata min yarinya zan shigar da kara koto . "reacting dinsu irin daya banbacin kadan ita uwar batayi kama da yar ba sannan yanayinsu ba daya bane inji commission wanda yayi mgnr cikin ranshi. "ok kije waje kijiramu ,umma ta nufi kofar fita tare da budewa ta fice. commissionier ya numfasawa yana kallon AK dake huci kmr kumarcin maciji sannan ya kalli su'ad dake girgiza jikinta ya nuna mata kujera da hannunsa ala'mun ta zauna kusa da AK . "karka damu ranka ya dade barni a hk kawai AK ya kallota a kaskance yana jan tsaki da karfi dan har ranshi yasoma tafasa akan yadda commission yayi mata . tsakin daya ja yasa su'ad sakar masa harara tare da cewa kallon km fa? ak yayi mata banza dan bai ga abin bata bakinsa wajen bawa amsa ba, shi kuwa commission bai damu da jin abinda tace ba yasoma mgn kmr hk muna son ki sanar mana ko akwai wani abu dake tsakaninki da abdulkabir wanda yasa kike bibiyarsa duk inda yaje, akaro na karshe.. sannan meye hujarki na sato masa amaryarsa aranar kamunta? murmushi mugunta su'ad tayi tana duban commission a kyakyace sannan tace babu komai ranka ya dade... "karya kike ina jin ba wannan ne Karo na farko da abdulkabir ke kawoki gurinmu akan matsalar kina takurawa rayuwarsa ba dan hk karki kuskura kice mana babu komai domin wannan karon ina tabbatar miki ko shi bai dauki mataki akanki ba hukuma zata dauki mataki da hannuta ,dan hk tun wuri ina umartarki ki sanar mana da gskyr lamari ,sai mu sakeki salin alin batare da an taba lfyr jikinki ba. amsar data bashi da farko ita din ta sake gaya masa wato babu komai ,yayi juyin duniya daita akan tasanar masa amman taki ta tsaya akan babu komai har suka shiga exchange word da commission yayinda AK yazama dan kallo agurin cike da mamaki. commission ya rasa ta ina zai bullo mata yayi nasara akanta shr yayi kawai yana kallonta can km wani idea yazo masa. yayi saurin gyara zamansa "yace idan baki gaya mana gskyar lamarin abinda yasa kike bibiyar abdulkabir ba zamu tsareki tare da mahaifiyarki har sai mun gama bincikenmu akanki . "a wani dalili? ta tmbyeshi "naga a dokar kasa babu dokar data bada wannan damar tsare wani akan wani ya aikata laifi ,nice nan nayi laifi ni yakamata ku tsare ba mahaifiyata ba sbd ita bata muku komai ba. "za'a soma wannan dokar akanki matsawar baki gaya mana gsky ba. ,duk inda ran AK yake yayi matukar baci, da iskancin yarinyar . commission ya dubeshi abdulkabir ko zaka iya tuna ko wani abu ya taba shiga tsakaninka daita ko ta cacar baki ne? AK ya dago idanunsa dake cike da tsantsar bacin rai ya zubawa commission yana kallonsa, sannan ya bude bakinsa da kyar "me zai shiga tsakanina da wannan yar iskar yarinya wallahi ina tabbatar maka ko hanya ban taba hadawa daita ba idan ba'a dan wannan lokacin ba.... commission ya dauki waya yasoma daddanawa , can aka dauka "yace asp ganiyu,yakira sunan yana jujjuya kujerar dayake kai zaune "bangare asp ganiyu kuwa kamewa yayi sosai tare da cewa yes sir.. " matar data fito daga office dina yanzu ku tsareta ku kaita cell dan... ai su'ad najin hk ta birkice tasoma kuka muryarta na craking tace pls commission kar saka mahaifiyata cikin cell bata cancanci shiga cell ba ,ita din me daraja ce ba kmr sauran iyaye ba. "tunda baki son asaka mahaifiyarki cikin cell why not ki gaya mana gsky "akwai matsalar ne commission........ " ita gskyr da kake bukatar sani akwai matsala akanta idan na fadeta . "dan girman allah commission kar ka bari na fadi ita wannan gskyr fadar abinda ke tsakanina da abdulkabir daidai yake da fadawata cikin halaka ... "kenan dai akwai wata a kasa kenan ? "AK dake zaune yace ka daina wani lallabata daday dan nasan babu wani abinda na taba yi mata arayuwata. " kawai dai tsabar iskanci ne irin nata . "aiko yau zata ga karshen iskancin daya fi nata matsawar bata fadi gsky ba. yakarasa mgnr tare da cewa kai asp ganiyu ka aiwatar da abinda nasaka kawai, dan har lokacin yana kan layi. "jikin su'ad na rawa tace zan fada commission.... "zan fada da dai a saka min uwa cikin cell na gwamaci na fadi koma meye tsakanina dashi idan yaso duk abinda zai sameni na yarda yasameni, takarasa mgnr tana kuka wiwi. ta juyawa musu bayanta ahankali tare da hade hannuwanta duka waje daya ta rufe fuskarta hawaye nabin kuncinta...... commission ya dakatar da asp ganiyu sannan ya fuskance da kyau. "uhm muna jinki ? ta juyo ahankali tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen na sake gangaro mata, sannan ta bude bakin da kyar zan tasoma mgn "zangayi komai dake tsakanina da abdulkabir wanda yasa nake ikirarin sai ya aureno dole da bibiyar duk inda yaje amman sai agaban iyayensa da mahaifiyata......... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE