← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 289

Sashe 262

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zamu ganta Inshaallahu yanzu dai kana ina? "ina ikoyi express " "Ok ka d!aure ka k'araso gida yanzu ,nan yashiga gaya masa abinda ya faru wani irin wawan birki ak yaja kiiiiiiii wanda yasa Musty tsorata tare da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, "kayi tuki ahankali fa ya fad'i haka tare dayin dayasanin gaya masa abinda ya faru , shiru Ak yayi zuciyarsa na beting sannan yasoma magana cikin sanyi murya, "da gaske kake yi Musty? nannauyen ajiyar zuciya Musty ya sauke kana "yace Allah kuwa. "Daman na dad'e da wannan tunani Ammi ce takasa fahimtata ganinsn zuwa yanzu amman fa akwai tashin hankali fa..musty yace "ka dai kayi tuki ahankali sai ka karaso muna hospital Droctor Rak "ok gani nan zuwa just give me 20 minti..... ko cikakken minti shabiyar basuyi da gama wayar ba sai gashi ya iso hospital d'in Musty ya tarosa suka jera zuwa cikin d'anki da aka kwantar da Taufeeq sai da gaban Ammi ya fad'i sanda tagansa yayi wani irin rama tamkar wanda yayi shekara da ciwo bakinsa ya bushe wanda ya nuna ala'mun baya cin abinci kasa hak'uri tayi tashiga goge hawaye, shi kuma yakarasa gaban gadon da Taufeeq ke kwance yana jan numfashi ahankali yana fitarwa ya tsura masa ido yana kallonsa, wanda wannan tsayuwar tasa yasa madam shema cike da wayyo da dabara ta kwace hannun Taufeek cikin na Salema..... wani irin kunya Umman Su'ad ta tsincin kanta cikin d'an haka yasa ta mike tsaye tsam taja baya kad'an ta jingina bayanta da bangon d'akin tamkar wace aka dasata wani sabon tashin hankali ta tsinci kanta ciki,wasu hawaye masu dumi suka sake yin nasarar biyo fuskarta tana k'ok'arin sharesu.. tsawon minti goma AK na tsaye akansa yana dubansa kafin daga bisani ya d'an saci kallon Umman su'ad ta kasan idanunsa "wato ma kukan masoyinta take bata d'iyarta data nema tarasa ba? gutun tsaki yaja akasan zuciyarsa sannan ya juya cike da izza zai bar d'akin yaji saukar muryar Ammi cikin kunnuwansa "Abdul ina zaka kuma? batare da ya juyo ba yacigaba da tafiya "zanje naci gaba da bulayin neman matata tunda bata da gatan da zai iya nemota da ya wuceni .. Ammi ta mik'e daga zaunen datake tace "dakata Abdul ya tsaya cak kamar yadda tabashi umarni har takaraso garesa ta kai hannunta cike da tausayawa halin dayake ciki ta dafa kafad'arsa. sannan tace "su'ad na da gata wanda kai kanka kasan da haka.. yayi saurin katse ammi ta hanyar cewa "ni bansan da wani gata datake dashi ba "Ammi ki duba fa cikinku babu wanda yayi k'ok'ari tayani nemo matata kowa hidimar biki ya sanya agaba "ke Dady eiman Musty umman s. .sai yayi shiru tare da dungule hannunsa ya naushi iska" amman babu komai zan cigaba da nemanta koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar rayuwata" daman kince kar na kuskura na sake zuwa gareki matsawar babu Su'ad zan tafi neman matata tunda ni ta zame min dole.. yak'a rasa maganar kamar zai zubda hawaye wanda hakan yasa kukan Umman su'ad tsananta eiman takaraso itama "yaya dan Allah k.... "banason jin komai daga bakinki kema aurenki ne agabanki ,"ku barni ni kad'ai dina ma na isa nemota a duk fad'in duniyar nan yakarasa maganar tare da sanya kai yabar d'akin. Umman Su'ad ta fashe da kuka abubuwa gaba d'aya sun cunkushe mata gaba daya duniyar ta tsaya mata cak gaba d'aya kalmominsa na mata nuni da bata damu da diyar cikinta ba yarinyar da ita kad'ai tasan iya wahalar datasha akanta duk duniya babu wanda zai so Su'ad kamar ita dan itace silar zuwanta duniya kuka take sosai har da shesheka Ammi ta rungumeta ajikinta tana rarrashi gaba d'aya tarasa me zatace mata.. tafiya yake Musty na biye dashi abaya "meyasa kakeyin irin haka? "gaba d'aya maganganuka babu d'a'a acikinsa ko babu komai bazaka fita jin d'acin ranshi su'ad ba "karya kake Musty ya juyo a fusace yana nunasa da yatsan hannusa "nace karya ne wannan maganar banza ce tunda abun nan ya faru kaga hawayenta? "ko kaga ta nuna damuwarta sai yanzu data sake cin karo da masoyinta tana kuka saboda ta tsinci masoyinta cikin wani hali . ak yakira sunan Musty tare da rik'o tafin hanunsa ya d'aura daidai tsatin zuciyarsa dake dokawa da karfi"kaji yadda zuciyata ke beting? " zuciyata na bugawa ne akan su'ad wallahi duk nafiku sonta da bukatarta a halin yanzu "Allah na rokeka ka sake wulakata rayuwar Zeey datayi silar rabani da matata ,"ya Allah kar ka sausautawa lamarunta Allah ka sake had'ata da mugayen alkaba'i iri ir... "ummmmmm Ak karkayi haka Musty yayi saurin d'aura hannusa kan bakinsa domin hanasa karasa abinda yake son fad'i "ko babu komai Zeey yar'uwarka ce," halaka ta zumunci ta had'aku taci darajar danganta dake tsakaninku ka yafe mata abinda tayi maka "kama barta taji da lalurar dake damunta. a matukar harzuke ya fizge hannun Musty daga bakinsa yaja tsaki ya juya yasoma tafiya ,yabar Musty tsaye agurin yana kallonsa cike da tausayawa kai tsaye gurin motarsa ya zarce ya shige ya fizgeta a guje ya bar harabar hospital. . har zuwa washegari Taufeeq bai farfad'o ba gbdy yan'uwa na tare dashi anatayi masa addua AK ma ya sake zuwa ya duba yanayin jikinsa . yayinda Ammi ta bukaci akawo mata ruwa cikin cup tayi addua sosai had'e da d'ago 'kansa tabashi ya sha sannan ta shafa a kansa zuwa fuskarsa, haka ta dinga yi masa har tsawon a wani takwas sannan akasamu ya sauke naunauyen ajiyar zuciya hade da dafe gefen 'kansa dayaji yana matsananci sara masa sannan ahankali ya ware kyakkyawa idanunsa a saman celling d'akin. zuwa wani lokaci yasoma kallon d'akin da jama'ar dake tsaye akansa ,sunyi masa tsuru da idanu suna kallonsa. adduar still Ammi keyi tare da sauran Jamar dake tsaye akansa ,yayinda Shemah ke zubda ruwan hawaye tana karanto duk addua datazo bakinta tana shafamasa saman goshinsa, Salema ma addua takeyi tana cigaba da kuka tana son isa inda yake kwance amman takasa aikata hakan gudun kar Ak ya isketa a gurinsa yayi mata wata fassarar daban. tana jin aranta gara ta tsaya inda take tacigaba dayi masa addua.. d'agowa yayi ahankali saboda jin kansa dayayi akan cinyar mutun .. karaf sukayi 4eyes idanunsa ya tsarke cikin idanun wata daban ba salemarsa ba da zuciyarsa taci karo daita ba, "k'ok'ari tashi yayi a matukar tsorace yacigaba da kallon jamar d'akin daga k'asan zuciyarsa yake tunanin ko wacece wannan matar dake tare dashi ba Salemarsa ba ...? A hannkali kuma komai yashiga dawo masa daki daki lokacin da idanunsa ya sauka akan salemarsa dake tsaye tana kallonsa tana zubda hawaye wasu na sake gangaro mata, ita din ma kwayar idanunshi take kallo kirjinta na wani irin bugawa daf daf!! sautin muryar Ammi yaji ta doki cikin dodon kunneshi wanda yasa ya d'auke idanunsa akan Umman su'ad ya maida kanta "tabbass wannan yar uwarsa ce mafi soyuwa arayuwarsa.." Taufeek d'ina Ammi takirasa ya kasa amsawa illa idanu daya zuba mata ta matso kusa dashi sosai "kayi min magana dan Allah ina kwad'ayin na sake jin sautin muryarka acikin kunnuwana domin tabbatar da dawowarka cikin wannan duniyar.. Ahankali ya bude bakinsa da kyar yace "Aunty Baraka.... yakira sunan Ammi cikin sanyi muryarsa me dadin sauraro "ina hajiya ta ina umman mahmud da mahmud suke..? take Shemah ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba sakamakon abinda taji yace wani sabon tashin hankali ta tsinci kanta ciki .. .. Ammi tace" Masha Allah, Allah abun godiya "Allah mun gode maka daka nuna min wannan rana Alhamdullahi "ashe zan sake riskar farinciki irin wannan? kowa a d'akin babu abinda yake furtawa sai kalmar Alhamdullahi Allah mun gode maka daka nuna mana wannan ranar ...... Ammi tacigaba da magana bayan ta sake yin kusa dashi sosai tana fuskantarshi " abinda nake so ka fuskanta nasan bayan halin daka tsinci kanka cikin jirgi baka cikin natsuwarka duba da yanayin tambayar matarka da d'anka dakayi a halin yanzu, "ala hakikanin gaskiya mun rasa Hajiya asanadin labarin mutuwarku da muka samu labari, nan dai tashiga labarta masa abubuwa da suka faru tun daga farko har k'arshe yayinda shi karan kansa kwakwalwar kansa ke hasko masa wasu abubuwa kafin jirginsu ya kone, shi dai yasan yana rungume da matarsa a wannan lokacin rungume kawai yake daita amman gaba d'aya, hankalinsa da tunaninsa na gurin Salema yana tunani halin dazata tsinci kanta idan taji labarin mutuwarsa yaji wani abu tamkar guguwa ya raba tsakaninsa da matarsa zuwa wani b'angare daban inda kanshi ya bugi wani makeken dutse daga nan bai sake sanin abinda ya faru dashi ba hawaye kawai Taufeek ke zubarwa yana sake hasko wannan tashin hankali me girma da bazai ta'ba mancewa dashi ba ... yayinda Shemah ke faman kallonsu tana son gano wasu abubuwan dake faruwa daki daki idan zata fahimci zantuttukan da Ammi keyi ,matarsa da d'ansa sun dade da rasuwa" to wacece wannan Salemar datayi sanadiyyar dawo dashi cikin duniyar tunaninsa? wanda d'anuwanta yayi iya k'ok'arinsa na yaga ya dawo dashi abun ya faskara har mutuwa ta riskeshi....... hawaye yake ta zubarwa sakamakon rasa mahaifiyarsa da matarsa da d'ansa dayayi sannan ya maida ganinsa ga salemarsa mafi kusanci da zuciyarsa dake tsaye har wannan lokacin kuka take. ahankali ya yafitota da hannunsa ala'mun tazo gareshi hawaye take zubarwa tana cigaba da kallonsa ta kasa zuwa inda yake har sai da Ammi tace "salema kije gareshi dan Allah da taimakon Allah da taimakonki ,muka samu wannan faricikin da muka dad'e da fidda rai da samunsa, "dan Allah ki taimaka kije gareshi yakara samun natsuwar zuciya ahankali Umma Su'ad tasoma daga kafafonta domin isa garesa tana karasawa tasamu guri ta zauna daga bakin gadon tana satar kallonsa wanda shi d'in ma kallonta yake cike da tausayawa sai dai shi ba wannan zaman datayi yaso ,yaso ne tana karasowa ta rungumeshi ajikinta amman duk da haka sai daya kamo tafin hannuta cikin nasa ya dinga massaging ahankali ahankali yana cigaba da dubanta tare da jin wani irin sauyi na daban agaba daya ilahirin sansar jikinsa ,takoina ajikinta jike yake sharkaf da ruwa gumi tun daga samanta har kasanta ....ahankali yasoma magana cikin sanyi murya yayinda idanunsa ke kanta "salemat...... yakira sunanta tare da kai hannunsa yana shafa cikinta
Chapter 262 · 0% Book details