← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 289

Sashe 124

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amman matan tayi buruusss dani sai ma sake maimata kalmar data gaya masa a daki take . muna cikin wannan halin matarsa ta shigo a haukace kmr an korota bansa yadda akayi tasan da zuwanmu ba . " kawai ta tsura min ido tana kallona babu wani bata lokacin ta sheidani bata manta fuskata ba ina ganinta naji zuciyata ta buga da matsanacin karfi amnan na kudircewa raina, zan jure duk wata azabar rayuwa indai zasu amshi cikin jikina . zuwan matarsa bai saka hjy fasa mgnrta ba taufeek.... takira sunansa a matukar fusace nace ka dauke min wannan yarinyar kabar min gidana daita wallahi zan iya tsine maka sanadin wannan yarinya wallahi wallahi kaji rantsuwar dan muslimi matsawar kenan ,kaga ka Auri yarinyar nan sai dai bana duniya. gbdy na daburce narasa yadda zanyi jina ya dauke kwalkwaluwata ta tsaya cak ta Daina aiki Nasoma fige fige ina zare ido tmkr me cutar hauka ina kallon fuskar taufeek so nake ya tabbatar min maganganun mahaifiyarsa duka karya ne ba gaske ba.... na kamo hannunsa na rike gam cikin nawa muryata na rawa nace taufeek gaske ne abinda naji mahaifiyarka na fada wai bazaka aureni ba ..? kafin yace wani abu nasoma jan gwiwona zuwa inda matarsa ke tsaye tmkr andasata nace kiyiwa Allah da manzonsa kisa baki hjy ta amince kiyi hkr nasamu muhalli agidanki mijinki kawai nake da muradi auren zan kai hanuna jikinta tayi saurin ingizani zata daga hannunta ta sauke min mari taufeek ya rike hannun tare da cewa karki soma wannnan ganganci, nace dan Allah kabari ta mareni matukar zata bari na auri mijina bazan taba damuwa ba. gbdy na gigice ina ta basu hakuri sai alokaci nasan ba mahaifina kadai keda ra'ayin rekau ba.. nasake dawowa gurin taufeek na rike hannunsa kace karya ne wai bazaka aureni ba. ya rike hanuna dake cikin nasa sosai sannan ya bude bakinsa yace min eh hk mahaifiyata tace amman ni ina sonki tare da cikina dake jikinki . yadda na tabbatar miki a can baya ina sonki bazan gujeki ba har yanxu hakan ne acikin zuciyata.. ina sonki sale..... tsawar hjy ce ta katse shi ya kasa karasa mgnr . dauketa nace..... ita matarsa kuwa cewa tayi muddin tana raye itama bazamuyi aure ba sannan takara da cewa taufeek ina sake tabbatar maka wannan ba matarka bace daduronka ce . amman indai aureta ne sai dai kayi sa alahira idan anayi ,amman ba anan duniya ba. amman a duniyarmu sai dai wannan ta zauna matsayin karuwarka a tana gama fadar hk ta juya cikin matsanacin kuka tashige dakin hjy tace yanzu taufeek agaban matarka kake cewa kana son wata da nuna kulawa da tsantsar soyayya..? ahankali yace hjy yazanyi kece mutun ta farko dazaki fahimceni amman kika juya min baya kamoni yayi zuwa jikinsa ya mikar dani idanun nan nasa sunyi jawur dasu bai taba tsammanin wannan ranar zatazo masa ba . bai taba tunanin mahaifiyarsa zata kawo masa matsala a soyayyarsa da salema ba. yasan tayi hkn ne sbd farinciki mee'ad if not hjyrsa me matukar son farincikinsa ce . "lokacin dana mike tsaye yasoma tafiya dani marata ta sake tsargawa ta rike gam nayi saurin dafe gurin sbd radadin azabar dana ji . sai km ga jini ya shiga biyo fafuna na tsaya cak na kasa tafiya jikina na rawa . ganin hk yasa taufeek ya daukeni agaban mahaifiyarsa wanda wannan abun dayayi min ya sake jefa zuciyata cikin tafkin kaunarsa ,km hkn ya sanyaya min raina ko babu komai ya nuna mata irin son dayake min. kai tsaye hospital din wani amininsa ya nufa dani likitoci suka ce masa ina bukatar hutu ne idan ba hk cikin dake jikina zai iya zubewa dan har yafita daga cikin mahaifata ya koma byn mahaifa. ina kuka wiwi cike da tashin hankali nakira sunansa muryarta a raunane taufeek....ya dago idanunsa da sukayi ja yana kallona tare da son jin abinda zance, kayi hakuri kabari a cire min cikin nan ....... sbd me? sbd ingantuwar rayuwarmu data cikin domin shine first step daya kawo mana matsala da danginka nasan banci wannan cikin da killa mahaifiyarka zata amince ka aureni amman sanadinsa kiri kiri hjy ta nuna kinta da cikin nan.. karki damu da zance kowa ni danayi cikina ina son abuna. ba'a alfahari da irin cikin nan amman ina miki rantsuwa da mahalicina ina mugun kaunar cikin jikinki sannan ina bukatar sa araye ya fada min hk. yana tsura min ido yanacigaba da kallona nace pls taufeek.. ya katseni bana son wulakanci salema cikin da muka samu lokacin muna cikin ganiyar cin wahalar rayuwa da tashin hankali iri iri kinsa walahar danasha kafin na dasar kwansa .. matsawar bakya son bacin raina karki sake min zance zubar da ciki. daren ranar ciwon ciki ciwon mara yasani gaba banda murkususu babu abinda nake tun yana min sannu har ya tafi kiran doctor kafin doctor tazo har jini yasoma tsiyaya tmkr an bude fomfo jini har da kudaji kudaji taufeek naganin yadda jini hankalinsa yayi matukar tashi yakaraso gareni jikinsa na rawa ya rike hannuna lokacin da doctor ta turo kofar tashigo takaraso inda nake dazamar soma dubani tunin cikin ya fita amman naci wahala taufeek na tsaye akaina yana min sannu sai da doctor tace ya fita ya bar dakin . amman kasa aiwatar da hkn yayi ya dawo gefena ya tsaya agabansa aka gama komai tare da min allurar bacci. koda na farka da fuskarshi nasoma cin karo yana zaune akan kujera hannushi cikin nawa yana ganin na bude ido y shiga jero min sannu sannan yaje hado min ruwan tea yabani nasha muryata a sanyaye nace cikin ya xube ko ? ya daga min kai ala'mun eh .nima na lumshe nawa idon sbd ban ji dadin da cikin ya xube ba sbd yadda naga ya kwalafawa ranshi akan son ciki. adduar nashiga yi acikin zuciyata allah yasa hjyrsa ta hakura ya aureni tunda cikin ya fita. sannu ya dinga min tare da kamo hannuna cikin nasa ya kira sunana salemat cikin sanyi murya zaki tafi ki bar rayuwa sbd cikin ya zube ko? ya fada yana kafeni da kyawawan idanunsa wayanda kallonsu kadai ke haddasawa zuciyata shiga wani yanayi na daban girgiza masa kai nayi hawaye na gangarowa ta gefen idanuna . karki yaudareni salemat nasan kinbiyoni ne sbd cikin jikinki banci hk da yanzu wani ne zai mallakeki . " ko babu komai na godewa Allah da kwai na yayi tasiri ajikinki. nifa ba kin biyoka nayi ba ...to me kikayi? ni dai ka yarda bakin biyoka nayi ba sannan bazan fita rayuwarka ba amman kamin alfamar daya ina son ka zauna cikin rayuwata idan har kamin hk zan yarda da tarin kaunarka gareni sannan zankasance tare da kai muddin rai naja numfashi na sauke.. ina sonka taufeek har bansan yadda zanyi ba kawai na tsinci kaina da fada masa hk. " na gode da soyayyarki gareni kin tabbatar min da hakikanin soyayyar gasky kike min. ki nuna min ni din kike so bawani abu dana mallaka ba ,ina tabbatar miki zan zamemiki sanyi idaniya zan baki kulawa zan zamemeki komai.. kai zanwa godiya taufeek kamin halacci arayuwa ka nuna min ba kowani nmj bane maci amanar soyayya....... yayinda maza dayawa suke butulcewa masoyansu lokacin bakinciki da tashin hankali akan samuwar ciki amman kai baka gujeni ba ka tsaya tsayin daka wannan kawai ya isheni farinciki lokacin da likita ya shigo ya samemu muna makale da juna yayi murmushi tare da cewa laila majnun ya furta hkn kassncewar abakinsa ne km yasan komai dake faruwa yakarso still yana murmushi yace sai kuzo ku wuce gida da alamun lafiya tasamu. " kwana na uku a hospital aka sallemini sbd naji sauki sosai taufeek ya sanar da hj y cikin jikina ya zube the nest thing hamdala tayi sannan ta daura da cewa ni dai bance ku kashe rai ba sbd cikar burinku domin bashi zai sa na amince da wannan auren ba ... ******** taufeek ya nemi yar'uwarsa da suke uwa daya uba daya daita, akan ta shawo masa kan hjy ta amince da aurenmu abu na farko data gaya masa shine ya gigigiza zuciyata taufeek ni kaina ina son yarinyar kasancewar tana sonka kaima kana sonta . amman inda matsalarta take mee'ad ce kai kanka ka san yadda mee'ad take agurin hjy. diyar yayanta ce da suke ciki daya. km itace ta riketa har zuwa aurenta, sannan aji ance itace kan gaban gurin bayar da gudumuwar ayi mata kishiya da wata. " kaima kasan hkn ba abu bane me yuwa ba. yanxu aunty shikenan sbd mee'ad ni za'a tauye nawa hakin... ? ka dai kayi hakuri... babu wani zance hkr dazanyi kawai kisan yadda zakiyi ki shawo min kan hjy wallahi matsawar ban auri salema ba zaku iya wayar gari kurasan gbdy ok naji zan sake tuntubarta kaima ka tsananta addua akan lamarin sukayi sallama. ni dake kwance kan cinyarsa nace ni dai aunty ta taimaikawa rayuwata tasa baki hjy ta amince da aurenmu . karki damu duk runtsi zamu kasance da juna sannan da yarda Allah hjy zata yarda da mgnr aurenmu na lumshe idona sbd dadin danaji. haka taufeek ya dinga yiwa mahaifiyarsa naci da zariya akan ta hakura tabari ya aureni . tace sam bazata yarda ya auri karuwace ba . tun yana bin daginsa su sa masa baki har ya kai ga nemo manya mutane su bata baki. lokacin da sukazo kayita jamata ayoyi da hadesai imani da kaddara da hakuri akan hukunci Allah tace shikenan ta hkr Allah ya sanyawa rayuwar auren albarka.ai mutanen nagama barin gidan tashiga zazzaga masa fada ta inda tashiga bata nan take fita ba. ta sake rantsuwa tare da tabbatar matsawar tana raye bazai taba aurena ba muddin km ya aureni sai dai ya canza wata uwar sannan ya biyata nononta dayasha. "hk ya dawo inda yayi min masauki kafin ya sai min wannan gidan da muke ciki, yayi kuka da idanunsa ranar kwanan kunci mukayi daga ni har shi, fuskarsa ta kunbura nima har lokacin kuka nake jinake kmr rabuwarmu tazo ina kukan rashin kaunar da mahaifiyarsa ta nuna min da km abinda babana yayi min . ni kaina yarasa wani irin son mukewa juna
Chapter 124 · 0% Book details