Sashe 144
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jinsa yana mgn tayi masa banza "sweet baby dake fa nake mgn amman kin yi banza dani? zeey ta dago idanunta dake fitar da ruwan hawaye ta kalleshi tare da antaya masa uwar harara . "ki tayani yiwa mahaifiyata biyaya dan Allah ki janye mgnr fasa aurena, ta mike a fusace ta fara mgn domin tana ganin shima yana son auren "bazan aureka ba, abdulkabir na fasa aurenka na km fada. AK ya sanya hannuwansa ya dafe kirjinsa gami da zaro ido idanunsa sukayo waje yace "akan dan zan auri su'ad zaki ce kin fasa aurena, kenan ba soyayyar tsakani da Allah kike min ba? "ina sonka feyye da tunanika ina tabbatar maka da soyayyarka zan mutu amman wallahi akan nayi sharing dinka da wata yar jagaliya gara na hakura da auranka... " nabarka kaje ka aureta dan bazan zauna da wata kishiya agidanka ba. ganin abun nata kmr tana son haukace masa yasanshi matsota da hanzarinsa ya kai hannunsa ya rikota yana fadar "baki isa ba wallahi baki isa ba ai tun farko kece kika fara nuna kaunarki gareni tun bansan so ba nazo na kamu da matsanancin soyayyarki dan hk ki canza wani zance wanda zan fahimta amman ba zance fasa aurena ba. " ni kaina bana son yarinyar ke nake so gidana dan ke kadai na gidanashi sbd me zaki nemi tayar min da hankali? "nagaya miki babu yadda zanyi dole ko ina son yarinyar ko bana sonta dole na aureta sbd bin umarnin iyayena ko kina son iyayena su tsine min akan rashin aurenta ? ta sake jifansa da wata muguwar harara, ai dole ka fakaice da fadar hk man byn ni nasan kana sonta kana son aurenta amman kazo kana yaudarata. "nidai nace na fasa aurenka na bar mata kai idan ma cinyeka zatayi karewar so taje tayi ta kaya ni kam gara mutuwa ta akan na zauna da kishiya .. ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya daita dan hk ya rikota zuwa jikinsa yana rarrashita tare da fada mata wasu sanyayyun kalamai amman a maimakon taji dadin kalamain sai ma taji tmkr yana watsa mata garwashin wuta ne ajikinta tayi kokarin kwacewa daga jikinsa amman takasa domin yayi mata kwakkwarar rikon da bata isa ta iya kwatar kanta daga gareshi ba. kuka me sauti ta sakar masa, kan kace me zeey ta haukace masa dukansa take da yakushi amman yaki sakinta "karabu dani mana , ak ya girgaza mata kansa tare da cewa bazan iya rabuwa dake ba, kema kinsani dan hk kiyi hkr wallahi tun iya tsawon rayuwata banta furtawa wata mace ina sonta ba ko son aurenta sai ke. kiyi hkr ki dauki kaddara domin babu yadda banyi dasu dady ba akan a fasa auren tun kafin mgnr tazo gurinki amman sun tsaya tsayin daka dole na hadaku tare. "bazai yiwu ba na hakura da kai na bar mata Allah bazan iya sharing dinka ba dan hk na bar mata kai. kada muyi hk dake mana ta zabga masa harara cikin kankanin lokaci ta rikita masa kwalkwaluwa jinsa yake tmkr ya rutsa ihu. ita kanta tasha mamaki yadda ya sukurkuce mata yana rarrashi, amman ba abin mamaki bane tunda tasan har lokacin akwai miyagun ayyuka akansa wanda tasirinsu ya wuce yadda take tunani, amman banci hk abdulkabir zata dinga wannan salon iskanci bai mata dukan mutuwa ba, ko yace shima ya fasa auren. "amman ji yadda ya wani rude ya gigice akanta yana fama bata hkr gsky ta jinjinawa aikin boka na kan dutse. rungumeta yayi tsam ajikinsa sannan ya lalubo kunnenta yana rada mata wasu sirri kalamai game da yi mata alkwarin zai riketa amana km bazai taba hada gado da su'ad da sunan auratayya ba dan hk itama ta taimaka masa yayiwa iyayensa biyayya ya auri su'ad ba dan yana sonta ba. da irin wadan kalaman AK yasamu ya shawo kan zeey ta amince da bukatarsa duk da tasan ko ya kusanci su'ad hkn bazai taba karya asirin data masa ba domin daita da su'ad din duk sammakar ne babu cikakkiyar budurwa acikinsu. "muryata ahankali tace na amince ,sbd murnar abinda tayi masa AK yayi mata alkwarin zai mallaka mata zukekiyar motarsa dayasa aka turo masa daga span domin yin angonci daita . tayi matukar yin murna da wannan kyauta . ********* ammi tashirya taje gurin islamic malamin dake bada maganin farfadiya, byn ammi tagama koro masa bayani yanayin ciwon su'ad da yadda akayi ciwon ya dawo kanta mlmin yace azo su'ad. jiniyace ta cika gbdy ilahiri unguwarsu su'ad har zuwa kofar tafkeken bakin get din gidansu inda tarin motocin minister lafiya suka ja birki suka tsaya ,aka bude masa bayan mota ya fito ammi dake zaune cikin daya daga cikin motocinsa ta fito suka nufin cikin gidan. shigarsu yayi daidai da fitowar umman su'ad a firgice tana ganinsu tayi mugun bata rai sannan ta juya zuwa cikin daki inda ta bar su'ad zaune gabanta na dukan tara. bakinsu dauke da sallama suka sanya kansu cikin parlour gidan jin sautin muryar yasa su'ad saurin dagowa da kanta idanunta ya sauka akansu ta mike da sauri gabanta na cigaba da faduwa yayinda ummanta takoma ta jingina bayanta da jikin bango tare da daura hannuta kan TV tana dan bubbugawa ahankali . idanunta na sama tana kallon ceiling din dakin batare da tace dasu komai ba . ammi da minister sukayi kansu gurin zama dan ganin ko kallon kirki basu samu daga umman su'ad ba balle su samu arxikin gurin zama. "muryar ammi a sanyaye tace diyata zo gareni na sake jin duminki ajikina, ko naji sanyi tare da rage radadin dake cin zuciyata. " yau tsawon shekaru shirin da yan kai ina bulayin nemanki cikin duniya. "diyata da... a matukar hassale umman su'ad ta katse ammi ta hanyar cewa " wace diyarki anan ina ganin kmr kina cikin rudu amman anan babu wata datayi kama da diyarki. "wannan "ya"tace ni kadai.... "karki yi hk salema karki yi yunkurin sake raba yarinyar nan da danginta alhalin suna tsananin sonta? "karka gaya min hk doctor ince agabanka komai ya faru.. dan haka babu wani zance "ya" anan su'ad diyatace dana haifa cikin ganiyar kunci rayuwa da rashin wadataccen soyayyar dangi . "bari nagaya maka ko taufeek ne zai dawo duniya bazan taba mika su'ad ga danginsa ba balle babu shi araye takarasa mgnr tana goge hawayen daya zo mata. "kenan kin yar da kice salemar taufeek ? " tabbas nice salemar da kasani, kmr yadda nida kai mukasan su'ad diyar taufeek ce sai dai duk duniya babu wanda ya isa ya rabani daita. duk maganganunsu suna shiga cikin kunnen su'ad daya byn daya idan zata fahimci inda zantattukansu ya dosa kenan zarginta ya tabbata ,har yana shirin zamowa gsky ,wadan nan bayin Allah suna da halaka me karfi daita .. "to su din su waye gareta ? tayi kanta tmby. a matukar tsorace take bin umman da mutanen dake zaune a parlour 'n. sautin muryar mutumin ta sake ji cikin kunnuwanta "tun wancen lokacin naso na bayyana komai amman kika hana wanda sanadiyar hk akayi rashin hjy ,dangi suka shiga halin ha'ulai amman a wannan karon wallahi wallahi baki isa ki rabamu da jinin taufeek ba. "na isa Doctor sbd nice nan na kawota duniya ko lokacin danake shan wahalar nakudar haihuwarta akwai daya daga cikinku daya tayani? "tmbyrku nake kun tayani shan zafin nakuda haihuwarta ne? "bamu tayaki nakuda ba amman ke kinsa ba diyarki bace ke kadai tunda bake kikawa kanki cikin ba. "har wani abun takoho ne akan cikin da aka nunawa duniya ba'a so sai dai a haifa byn rai "kasani doctor ina mugun jin kunyarka wallahi if not da idan nagaya muku wata mgnr har ku mutu ba zaku mantani ba. zaiyi mgn ammi ta dakatar dashi mubarak bawannan long talk din ya kawo mu ba yanxu saleema kin zauna muyi mgn ta fahimtar juna. umman su'ad ta zauna tana jiran jin abinda ammi zata ce "atsanake ammi tasoma mgn saleema bamunzo gurinki dan murabaki da diyarki bane, nan tayi mata bayani me maganin da sukaje gurinsa ne , wanda ya tabbatar musu da dole sai an zo masa su'ad yaganta. umman su'ad bata amince ba alokaci daya sai da aka kai ruwa rana sanan ta amince . cikin sanyi murya ammi tacigaba da mgn atsanake kmr farko kiyi hakuri saleema ki sake rungumar kaddararki kmr yadda kika fada a wancan ranar cewa kaddara acikin jiniki take. "wallahi wallahi ko ki yarda ko karki yarda muna sonki ke da diyarki, nasan ko lokacin baya taufeek bai taba gaya miki ina daga cikin wadan da basu son aurenki dashi ba,bangaki ba alokacin amman naji araina ina sonki kasancewar dan'uwana na mugun kaunarki. ammi ta tsaya ta numfasa sannan tacigaba "an dai samun matsalar ne daga gurin hjyrmu wace itama daga baya tayi datasani dan ina tabbatar miki datasan daga baya hk abubuwa zasu kwabe da bata hana aureku da taufeek ba. "asanadiyar rashinki da cikin jikinki hjy tarasa rayuwarta har ta mutu bakinta bai daina ambarta sunanki ba. ina rokon alfarma da arziki kiyafe mana darajar allah da km darajar soyayyar dake tsakanki da taufeek sannan ayanzu ki lamunce min na wuce da mamana... "saleema ammi takira sunanta cikin sanyi murya "kin cika yar halak kin tabbatar mana da ke din me amana ce da rike alkwari ce tunda kika cika burin taufeek byn kinsa baya raye . "kika iya hakuri da juriyar da kika sakawa diyarki sunan mahaifiyarmu wannan abun kadai da kika mana ya isa a jinjina miki.. tun lokacin da ammi tasoma mgn kuka saleemat take wanda tasa minister goge hawayensa dan mganrsu na tuno masa da aminisa.. "kiyi hkr kiyi hkr ki manta komai daya gabata mu maida hankulanmu akan lafiyar diyrmu .. cike da matsancin sanyi jiki su'ad takaraso ga ummanta ta riko hannuwanta duka cikin kuka muryarta na wani irin rawa tace "umma wai su din su waye dan Allah ki gaya min halakarsu da mahaifina ina son sani me ye dangantakarmu dasu? muryar umma cike da matsanancin kuka tace "yayar mahaifinki ce uwa daya uba daya shi km wannan aminin mahaifinki ne wanda Allah kadai yasan tsakaninsu.. a zabure su'ad ta juyo tana kallon ammi da minister da ke zaune dukkaninsu