Sashe 73
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sanye ajikinsu. da sauri ya dauke idanunsa akansu yana ambaton suna Allah , ya salam ya furta yana girgiza kai zuciyarsa na wani irin harbawa ,muryarsa ahankali ta fito ta yadda basu jishi ba. sbd Allah dady waye yayi mata irin wannan dukan..? shi bai ma damu da irin raunukan jikin ore ba kmr nata. commission yace mahukunta ,sbd an tabbatar min byn rashin kunya da cin mutuncin da suka yiwa ma'aikatantanmu ita waccen ya nuna inda su'ad take tsaye har da marin inspector kule tayi..... kasa cewa komai ak yayi ,ya dan juyo ya sake satar kallonta sannan yasoma mgn da commissioner sun dan dade suna zantawa inda daga karshe AK yace kmr yadda nayi maka bayanin komai dazu, so nake tarabu dani da rayuwata taje tayi nata rayuwar sbd ni daita sam bamu dace ba. kafin commission yayi mgn yaji sautin muryarta cikin kunenshi ba kada hankali abdulkabir ko nace hankalinka bai cika ba, a zabure ya juyo yana kallonta da mayattun idanunsa. inda kasan wahalar dana sha akan soyayyarka bazaka fadi hk ba. da wuya da azaba zai sa na barka da yanzu an wuce gurin ,ina sake tabbatar maka da *sai ka aureni dole* commission ya bude baki yana cewa bazai yiwu kice hk ba, tun da ba'ayin aure ta hanyar da kike biyo . idan ma kina son ya aureki ne, kamata yayi ki natsu ki dawo haiyacinki ,domin a yadda kike din nan babu me ganinki hk yace zai aureki indai ba mahaukaci bane ... wannan mahaukacin dakake mgn akai gashi nan zaune agabanka km ko yana yawo tsiyarara da hauka tubaran shi zuciyata tagani km takamu da sonshi .dan hk kagaya masa ya aureni kawai a wuce gurin, ko km ka tabbatar masa da yanzu aka soma wasan...musayar mgn suka dingayi da commissioner babu wata tsoro ko fargaba wanda daga karshe commission yace a sallami ore abar su'ad . byn ore ta fita commission ya mike tsaye tare da zagayowa zuwa inda take tsaye yace ta zauna tare da nuna mata wata karamar kujera. ta zauna tana cizan lip's dinta na kasa batare da takalli inda ak ke zaune ba yayinda shi kuwa AK duk motsinta akan idanunsa take.ya kasa dauke idanunsa akanta . commissioner , yayi shiru kawai yana kare mata kallo. naji duk abinda kikace kina son shi wannan yaron irin son da bantabajin irinsa ba ko atahiri. sai km kikayi rashin sa'a shi din ba sonki kmr yadda kike masa. amman yanzu ina son kimin wani abu guda daya . kiyi hkr ki hakura dashi tun da shi baya sonki idan kika natsu kikayi addua da hkr sai Allah yabaki wani wanda yafishi.. abinda bazai taba yiwu ba kenan ta fadi hk sbd ganowa datayi wayo kawai commissioner ke son yi mata. , ina son kasan wani abu kai ma, abdulkabir kadai zuciyata ke so da muradi kasancewa tare dashi matsawar bai yanto zuciyata ba, damuwata zata kasance damuwarsa, matsalata zata addabeshi . duk wannan bakar rayuwar da nakeyi akan shi ne fa. sai kawai na hakura wata ta aur.....da sauri abdulkabir ya mike tsaye cikin tsananin fushi yake fadar baki isa ba... baki isa ki tursasani aurenki ba ..ko saka zuciyata abinda batayi niyya ba. wuya da azaba tattare da matsin rayuwa yanzu kikafara sha koma nace baki ga komai ba . kima soma kukan rasani.dan kuwa zaki rasani rashi na har abada dan bazan taba aurenki ba. dan hk ki tashi kibar office din nan yanzu tun kafin in zamo ajalinki ,ki bar duniya da huja. , cikin tsananin firgici da faduwar gaba ta dago fuskarta wace take wanke da ruwan hawaye tana kallon cikin kwayar idanun masoyinta mafi soyuwa azuciyarta . "ahankali ta mike tsaye zuciyarta tmkr zata buga .... still idanunta na cikin nashi batare da tace masa komai ba ,domin tasan matsawar batayi abinda yace ba ,bakaramin aikinsa bane yayi mata dukan mutuwa agurin ahkali cike da sanyi jiki da tausayin kanta ta mike tasoma tafiya tare da bude kofar ta fice daga office din. komawa yayi zauna tare runtse mayatattun idanunsa ,hannusa yasa yana shafa fuskarsa dashi gbdy yarasa me zai sake cewa akan lamarin yarinyar. commission ne yashiga bashi baki kafin daga baya ya bude baki da kyar yayi masa sallama. koda su'ad takarasa gida da gudu ummanta taje ta rungumeta ,tana kukan da murna ganinta. dan gbdy hankalita ba'a kwance yake ba ,babu inda bataje nemanta ba. daga karshe ne aka tabbatar mata tana police station. zamewa tayi daga jikin ummanta ta isa inda mirrow yake ta tsaya tana karewa kanta kallo, sannan tashiga bayin dake manne da parlour wanka take ahankali tana wanke kowani gaba dake gangar jikinta, ta dade bata fito ba, tana gasa jikinta da raunukan jikinta . tana fitowa ta iske ummanta ta shirya mata abinci ta daura mata akan dan karamin stood ,batabi ta kan abincin ba dan bashi ne agabanta . tashige kuryar daki ta janyo jakarta ta ciro tabar wiwi tayi babban nade tare da kunawa tasoma busha hayaki tana lumshe fararen idanunta . take hayaki ya bude dakin ,zariya take tana sambatu akan ak tana zukar tabarta har dai ta kai ga hayewa gado ta kwanta hawaye na gangaro mata .umma dake zaune cikin zullumi a parlour tasoma jiyo warin tabar wiwi da sautin kuka, da sauri ta banko kofar dakin cikin tsananin fushi take fadar bakiga komai ba yanzu kika soma kuka ba dai akan namiji kike neman kassara rayuwarki ba. maza maza ki tashi kibar min gida tun kafin na tsine miki ki karasa lalacewa kibi duniya da hujja tunda daman rayuwar kaskanci kika zabawa kanki.. cikin tsananin firgice da tashin hankali ta dago fuskarta daga kwanciyar datayi tana kallon fuskar mahaifiyarta mafi soyuwa gareta . muryarta na rawa tace ki taimaka ...ki taimakeni ummana ki taimaki rayuwata ki sanyaya zuciyarki salama ki min addua ki cire kalmar tsinuwa agareni ki cigaba da nemammamin shiriya da sausauci wahalar da nake ciki agurin Allah. sannan ki hango irin damuwar da nida ke zamu shiga agaba a sanadiyar tsiniwarki gareni, domin duk halin da zanshiga zai fi miki zafi da ciwo akan kowa. amman karki damu zan bar miki gidan nan duk da kasancewarsa na mahaifina ne ,wlh zan bar miki gidan nan km a yanxu bazan jure bacin rai da damuwa irin hk . da me zanji damuwar danake ciki ko km da kalaman tsinuwarki gareni, domin dana zauna ki dinga tsinemin na kara lalacewa gara nabar miki gidan na huta tana karasa fadar hk tajanyo akwatin kayanta ta bude wardrobe tasoma zuba kayanta tana gama xubawa ta zuge akwatin ta juyo tana kallon ummanta. ina matukar kaunarki ummana ,kece jigon samar dani a duniya duk da bansa kotawace hanyar kika samar dani ba. amman ina jinki cikin zuciyata, banida kowa bani da komai sai ke kadai. ina rokon Allah ya sanyaya zuciyarki yabaki ikon yi min adduar shiriya da kariya gareni, ba hk na kasance abaya ba kece kika kawoni duniya kika tarbiyarta dani sannan daga baya kika tsince rayuwata hk, ni kaina banason wannan rayuwar danakeyi amman babu yadda zanyi dole na karbeta itace kaddarata . tana gama fadar hk tasoma jan akwatinta har ta bude kofar ta fita allah sarki ai umma nagani fitar su'ad ta zube kasa tana kuka tmkr karamar yarinya uwa da "dal kenan sai Allah a zabure ta mike tana kuka da kiran sunanta su'ad ..su'ad dina dan Allah ki dawo karki tafi ki barni bazan iya rayuwa babu ke ba. ke kadai gareni duk duniya banida kowa sai ke, a parlour ta risketa tana kokarin bude kofar ta rungumeta ajikinta karki tafi bazan iya rayuwa babu ke ba na hakura na dauki kaddara....dole ce tasani yanke wannan hukuncin kamota tayi ta zaunar daita umma kuka su'ad kuka babu me rarrashin wani. ba dan dole ba mezai sa tayi tunanin yanke alaka da tausayawar dake tsakanin uwa da yarta ahankali cikin matsanancin damuwa ta daga hannuwanta sama cikin muryar kuka da rauni ta fara addua ya Allah ka shirya min yarinyata .Allah ka kawo mata natsuwar zuciya da kwanciyar hankali. Allah ka canza mata rayuwa fiyye da wace tayi abaya .Allah kazama gatanta . takarasa fadar hk ta janyo hannu yarinyata tana cigaba da kuka. ummana ki daina kuka dan girman allah zan canza ..ni dai ki cigaba da min addua hk suka kasance ranar cikin kunci da matsanancin damuwa, daga karshe umma ta janyo tablet din abinci tasoma bawa su'ad abinci abaki tana ci sosai ta dinga cin abincin kasancewar cikinta ya bude dan tabar wiwin datasha if not abinci bazai samu damar shiga cikinta ba. byn tagama ci umma ta dauko mata ruwa me sanyi ta mika mata. ta karba ta sha har lokacin idanun umma bai bar zubar da hawaye ba, ahankali ta juya takoma daki ta kwanta a inda tasaba kwanciya tunanin rayuwarta ta baya tashigayi. tunawa ta dingayi da abubuwan da suka faru idan ita batayi sa'ar uwa tagari ba wacce tayi sanadiyar ruguza rayuwarta, yarinyarta fa? duk wata kulawa da tausayawa da tarbiya babu wace bata tsaya tsayin daka tabawa su'ad ba . akarshe ga yadda takasance.. anya ba tarin zununbanta dana mahaifinta ne ya afka kan yarinyar dabata ji ba bata gani ba. tashiga juya kai tana kuka tabbas ta tafka babban kuskuren arayuwarta wanda bazata taba gogewa kanta shi ba.. byn kwana wasu kwana su'ad na gida tana jinyar kanta dan idanunta sun dan dan sabe sai dai abinda baza'arasa ba. samun saukinta keda wuya ta fito neman ak amman gabadaya ta neshi tarasa ,duk inda tasan zata gashi ko taji duriyarsa taje babu shi babu alamunsa. dan hk ta yanke shawarar zuwa gidansu. ta shirya cikin doguwar rigar material har kasa, wace ta lafe mata ajiki,ta fidda ainihin Shep din jikinta da kirjinta dan rigar ta kamata sosai daga sama daga kasa km flay ce ta yane kanta da dan karamin mayafi baki .kafafunta sanye cikin takalmi flat suma baki ,sosai tayi kyau kasancewarta fara sol doguwa , ta fashe ilahirin jikinta da turaren me sanyin kamshi da taba zuciya. kai tsaye gidansu ak ta nufa. kusan minti goma tana tsaye abakin karamin get din gidansu tana tunanin ta yadda zatayi nocking. sai ta kai hannuta da