Sashe 157
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hospital tana gida tana cigaba da jinyar zuciyarta tare da shan magani. kusan kwanaki biyu kenan da fitowarsu daga hospital amman AK ko take ko leke bai zo duba yanayin jikin su'ad ba tun ammi na dauriya sbd kar yaga kmr ta matsa masa dayawa, amman ganin iskancinsa sai gaba yake yasa ta buga masa waya byn yazo ta rufeshi da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba mgn yasoma yi mata domin kare kansa ammi ta buga masa tsawa kayi min shiru shashan banza kai yanzu har sai an maka mgn sannan zakazo duba jikin yarinyar nan, tun washegarin randa muka kawota rai hannun Allah da kai baka sake yunkurin neman inda muke ba wallahi idan kayi kuskuren da wani abu yashiga tsakaninka da zeey ba su'ad sai na tsine maka .... wayyyohly Allah ammi ak ya furta hkn tare da dafe kirjinsa da hannunsa na dama sakamakon matsanancin bugawar da dayake jin zuciyarsa ta yi masa ,sannan ya rarrafa gaban ammi ya riko kafafunta "pls amminah kiyi hkr karki min hk karki tsine min..," kibari nasamu natsuwar zuciya tukun ki taimakamin ammi tace "mgnr natsuwa babu ita matsawar bakabi umarnina ba . cikin rauni murya da zuciya "shikenan ammi bazan taba kuskuren aikata abinda zai sake bata miki rai ba ,"ta shi kabarmi guri takarasa fadar hk tana barin gurin zuwa dakinta da su'ad take. ******** duk wata tarairaya da nuna kulawa su'ad ammi take bawa hatta umman su'ad tadazo gidan sake dubata ta yaba da kullawar ammi ga diyarta sannan ta sake amincewa da kaunar da ammi kewa mahaifin su'ad ta gsky ce ,duba ga yanayin irin soyayyar da tattalin datake mata . misalin karfe takwas na dare ranar lahadi wanda yayi daidai da kwanaki goma da daurin aure ak da matansa, aka shirya zainab tsab cikin wasu haddaun doguwar rigar shadda blue black har kasa wace tasha aikin stone work aka lullube mata kanta zuwa jikinta da farin mayafi sai wanka ruwan turare da'aka mata , aka fito daita zuwa part din dady domin yayi mata fada byn mamanta da sauran dagi sun mata sannan aka nufi part din ammi daita nasiha ammi tayi mata me rasa zuciya na tsakani "ya" da uwa kmr yadda tasan zata yiwa eiman ko su'ad sbd zeey itama kmr diyarta ce cikinta koba ak ta aura ba, akwai shakuwa me girma atsakaninsu sosai wace sukayita acan baya, yanxu ne ma tarasa gane kanta da gindinta tun dawowar su'ad gidan .... byn ammi tagama mata fada kai tsaye farfajiyar gidan akayi daita inda mutane da sauran dangi wadan da basu rigada sun koma baz suke tsaye domin yiwa amarya rakiya dakinta sababbin motoci ak aiko dashi kusan guda goma wanda duk mota daya akwai abakinsa daya cikinta wanda zai ja motar. aunty bilki da aunty malika sune rike da hannu zeey har zuwa jikin wata haddadiyar mota wace tafi dukkanin motocin gurin kyau da tsada suka bude mata gidan baya tashiga sai kawayen amarya mutun biyu sha'awa tashiga ta zauna kusa da zeey nuratu km tashiga gaban mota aunty bilki da aunty malika suka nufi motar dake bayan ta zeey . ahankali securities suka bude tafkeken get din gidan motoci suka soma fita daya byn har sai da gbdy motacin suka gama fita wajen gidan suka jeru sannan suka soma kokarin barin unguwar zuwa gidan AK dake Hill Green estate.. ahankali ak yake daga kafafunsa jikinsa sanye cikin wata tsadaddiyar shadda buwa fara sol. me shegen kyan da tsadda sai kyalli shaddar take zubawa kallo daya zakawa shaddar dake sanye a jikinsa ka tabbatar da tsadarta tsinsiyar hannunsa daure da agogon gold kafafunsa sanye cikin wasu tsadadden takalmin Gucci ,yayi matukar kyau na fitina da daukar hankali ga wani azababben kamshi turare disiner dake tashi a ilahirin sansar jikinsa wannan kamshin turaren dake tashi ajikinsa babu yadda za'a yi wata diya mace ta shaka bataji mamallakinsa ya burgeta ba . kai tsaye dakin amminsa ya nufa ahankali ya daura hannunsa kan handle din kofar ya bude da su'ad idanunsa suka soma cin karo dashi tana kwance rigingine tasanya pillow abayanta suna hira da ammi dake zaune a gefenta yakarasa shigowa dakin bakinsa dauke da sallama batare daya dauke idanunsa akanta ba, sbd wani azabben kyaun dayaga tayi masa duk da tayi maseefar ramewa amman hk bai hana sihirtaccen kyawunta fitowa ba, shi gani ma yayi kmr ciwon datayi kara mata wani kyau yayi ,sosai ya kafeta da mayatattun idanunsa yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta. kwata kwata bai yi yunkurin dauke mayatattun idanunsa akanta ba , ahankali ta dago kanta idanunsu suka tsarke cikin juna ta sauke fararen idanunta cikin nasa atare zuciyoyinsu ya buga da maseefar karfi ,take tayi saurin dauke idanunta acikin kwayar idanunsa zuwa wani gefen daban sbd bazata iya jurar kallonsa ba zuciyarta banda dukan uku uku babu abinda take. wata karamar stood ya janyo zuwa gaban ammi ya zauna yana fuskantarta sosai daga bisani muryarsa a matukar kasalance yasoma motsa labbansa "ammi mun wuni lfy? "lfy ta amsa masa atakaice . su'ad ta yunkura zata tashi daga jinginar datayi domin basu guri ammi ta dakatar daita ta hanyar cewa "ina zaki km ? su'ad ta langwabar da kai ala'mun shagwaba kana muryarta cike da sanyin dadi" tace zan shiga cikin dakin na kwana ne ... "koma kiyi zamanki idan ma kwanciyar ce kiyi anan ,dole tasa su'ad takomawa ta kwanta tare da juya musu baya dan ba yadda zatayi bazata iya musu da ammi ba. kokuwa tashiga yi da numfashinta dake kokarin barin gangar jikinta "yanzu wannan shirin fa da yayi na zuwa gurin zeey ne? tayiwa kanta tmbyr a kasan zuciyarta ahankali ta furta ya Allah allow my brain to rest, "dan allah abdulkabir ka kyale zuciyata da rayuwata su huta hkn. wani azabban kishi ne yashiga tasomata wanda ya haddasawa zuciyarta bugawa da karfi karfi ji take kmr ana sa guduma ana dukan tsokar dake makale da kirjinta, yadda kirjinta yake dukan uku uku hk kowace gaba ajikinta take rawa, kallo daya ammi ta mata ta gane bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankali har ma ta fara datasanin tsaida ita. "ammi AK yakira sunanta cikin wata irin murya me maseefar sanyi cike da rudani "uhm ina jinka "sai daya sosa keyarsa sannan yace "daman naxo na miki sallama ne.... ka kyautawa kanka Allah sanyawa rayuwar aurenka albarka, Allah yabaka iko da karfin zuciyar yin adalci atsakanin matanka," Allah yasa wannan auren dakayi yazamo silar daurewar farincikinka da kwanciyar hankalinka, sannan ta mike tsaye tasoma tafiya shima ya mike ya biyo bayanta har parlour 'nta taja ta tsaya tana kare masa kallo daga samansa har kasa cikakken namiji ne ajin farko me cikakkiyar sura wanda bakowani nmj Allah yake bawa baiwar dake tattare dashi ba ita kanta tasan yaronta ya hadu takoina, numfasawa tayi ahankali cikin rage sauti muryarta takira sunansa abdul ....na'am ammi nah "karkayi kuskuren waskewa da mgnta.. bazanyi kuskuren aikata hkn ba sbd mahimmanciki gareni idan ma kince kar naje gurin zeey a yau zanyi zamana tare dake har lokacin da kika lamunce min, ta sake sauke naunauyen ajiyar zuciya jin abinda yace "shikenan abdul Allah ya tsare min kai da tsarewarsa "amen ammi nah tare suka fito dashi suna tautuinawa kasa kasa har zuwa farfajiyar gidan inda su musty ke zaune zaman jiransa cikin mota har inda sukayi parking din motar ammi ta kaisa tare da bude masa gidan baya yashiga ya zauna tana cigaba da yi masa adduar takarasa mgnr ta hanyar yi musu addua gbdy Allah ya tsaremun ku gbdy, atare suka amsa da ameen . ta meida kofar motar ta rufe taja ta tsaya tana kallonsu har suka bar gidan zuciyarta cike da matsanancin fargaba. bangare AK ma shiru yayi cikin motar yana jin wani irin acikin zuciyarsa tausayin amminsa ya tsaya masa arai kmr yacewa musty ya juya ya koma ,baya son ganin rauni a fuskar mahaifiyarsa balle damuwarta.. hayaniyace ta kware atsakaninsu ,gaky AK kayi dacen mahaifiya me matukar kaunarka shakuwarku da soyayyarku da ammi yana matukar burgeni abun na taba min zuciya inji cewar malik gsky ammi uwace har da rabi wlh yanxu hk ji nakeyi kmr na koma gurinta tun ba'aje koina ba nasoma jin kewarta wlh yayi mgnr muryarsa cike rauni . " kunji dan duniyar dan iska nan ko .....musty dake tuki ya fadi hk tare dubansu malik dake zaune abayan mota ta mirrow. "meyasa bakayi zamanka ba? musty yacigaba tuki yana mgn ku kalli mutumin dayaketa Faman maseefa da azalzala ayi ayi sauri akaisa amaryarsa nacan na zaman jiransa zai wani ce ga zance ga mgn kai dai ka bi yarinyar mutane ahankali karkaje kayiwa amarya shigar sauri nasan yadda kake rawar jikin nan sai wani ikon Allah ,nasan tsohon jarabace zata mike zanga zanga . dry suka kwashe dashi gbdynsu banda AK daya ji ranshi yayi mugu mugun baci sakamakon tunowa dayayi bazai yi komai da zeey ba yau , har suka iso estate din tautaunawa suke atsakaninsu suna kai wa bakin tafkeken get din gidansa musty yaja burki yana hon "kar damu da yin hon din dan ana zaku tsaya babu me shigar min gida yagane min mata yakarasa fadar hk yana fitowa daga cikin motar yana hade rai kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa. "me kake nufi? "abinda nake nufi kenan na fada ba sai na sake maimaitawa ba. "yanzu kana nufin ana zaka dakatar damu dan wulakacin inji cewar musty . "yes of course iyakacinku nan daga nan bana bukatar ku karasa ko nan da can, wata uwar ashariya malik ya lailayo ya maka masa " ai baka isa ba , tun baka soma jin dadin mace ajikinka ba zaka fara da salon iskanci... "babu wani zance iskanci sai gsky ku kama gabanku kawai tun dare bai karasa yi muka ba . " Allah dai ya shiryeka AK duk wanda yaganka yace yaga mutumin kirki karya yake wlh musty yayi mgnr yana juya kan sitiyarin motar kayi da me yi "a sauka lfy nagode sosai "dan Allah malam ka rike godiyarka bama bukata mara mutunci kawai . ak ya matso ta kusa da musty sosai "miko min laidar kazar sweet baby nah .. "gashi maye Allah yasa wannan rawar jikin da kake