← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 289

Sashe 132

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
*bissimillahir rahmanir rahim*
*hasbunallahu wani'imal wakil*
page 48
yadda suke kallonta cike da matsanancin mamaki sbd da furucin datayi, hk itama take binsu da kallo daya byn daya most especial AK dake zaune wanda gbdy ya tattara hankalinsa kacukan akanta byn ya tsareta da mayatatun idanunsa yana kallonta.
wani birkitaccen yanayi ya shiga kafin daga baya ya dawo cikin haiyacinsa ya sake ware idanunsa sosai akanta bakinsa mgn yake son yi amman ya kasa sarrafa harshensa.... .
ita kuwa wani bakinciki ne ya tokare mata kahon zuciyarta wanda yasa hawayen idanunta tsananta gangarowa bisa kuncinta .
"batason bayyana wannan sirri dake tsakaninta da abdulkabir, wanda yake daidai da tarwatsa rayuwarta a karo na biyu matsawar tayi kuskuren fadarsa . amman babu yadda zatayi da rayuwarta ya zamemata dole ta bayyana wannan sirri kodan martabar mahaifiyarta .
tayi hkr ta jurewa kaddararta data samar daita balle wannan damuwar......tayi imani duk abinda ke tafe da shafukan rayuwarta daga Allah ne.
tayi mgbr imani da hukuncisa gareta tare da yarda da kaddararta me kyau ko akasin hk .
abubuwan dake faruwa daita kaddara ce wace bata isa ta canzawa kanta ba.
commission dake zaune ya sake gyara zamansa lokacin dayake jin wani irin tausayin yarinyar yana bin Jinin jikinsa.
ya tabbatarwa kanshi tabbas akwai wani sirrin boye dake tsakaninta da abdulkabir.......adduarsa Allah yasa ba abinda yake tunani bane ya taba shiga tsakaninsu....
muryarsa ahankali ta fito gurin cewa "ki natsu ki dawo cikin haiyacinki nima tmkr mahaifin abdulkabir ne duk abinda kika san yana tsakaninki dashi ki sanar min dan ina tabbatar miki tmkr yaje kunen mahaifinsa ne.
dan hk karkiji komai zaki iya sanar dani komai .
girgiza kanta tashigayi tana kuka wiwi tare da daura hannuwanta duka bisa kanta alamun tana cikin tashin hankali sannan muryarta cike da kuka tace "kmr mmahaifi kace ,kmr mahaifi kuwa bazai taba zama mahaifi ba, dan hk ka kirasu zuwa nan kawai, ko muje gidansu tunda na rigada na amince zan fadi komai ......takarasa mgnr tana sake sakin wani Sabon kuka me taba zuciya sbd tuna makomarta da zarar ta bayana komai dake tsakaninsu.
juyin duniya commission yayi daita akan tasanar masa amman fafur taki tace zatayi mgn amman sai agaban iyayensa ,dan hk ran ak yayi matukar baci ya zabura ya mike tsaye ilahirin jikinsa na kirrma ya damki hannunta cikin nasa cikin matsanancin fushi yasoma janta commmission na masa mgn ,yayi banza dashi ya nufi kofar fita daita, kafin commission ya ankare tuni har ya fice daga office din.
janta yake tana biye dashi abaya tana kuka kmr ranta zai fita har ya iso farfajiyar police station , kai tsaye inda yayi parking din motarsa ya nufa daita ya bude mata gaban mota ya watsata ciki ya Rufe murfin motar da Karfi ya zagaya yashiga mazaunin direba ya tayar a fusace.
tun daga nesa umman su'ad ta hango yadda AK ya sauko daga saman commmission janye da hannun su'ad yana janta har ya sata cikin motarsa.
cike da matsanancin tashin hankali tasoma kokarin cima masa amman ina har ya tada motarsa, dan hk ta kurma ihu da kururuwa neman dauki tare da daura hannuta saman kanta tana kuka daidai lokacin da commission yakarasa saukowa yace ta bar kuka tabiyo bayansa suje.
tunda ya fita daga harabar police station din ya figi motar a guje duk wanda yaga irin gudun dayake dole ya bishi da kallo, wani irin gudu yake falfalawa akan titi na fitar hankali har suka iso unguwarsu bai ce mata komai ba itama hk batayi yunkurin cewa wani abu ba bayan sheshekar kukanta daya tsananta karfi ,yayinda AK yashiga tunani yadda zata kasance atsakaninsa daita agaban iyayensa gbdy tunaninsa ya tafi ne gurin son tuna baya ko ya taba wata mu'amula daita ko wani abu makamanci hk, amman har ya iso kofar tafkeken get din gidansu 'kwalkwaluwarsa bata hango masa komai daya taba shiga tsakaninsa daita ba.
hon yashiga dannawa da iyakacin karfinsa wanda ya firgita securities din bakin get yayinda take jikin baba me gadi yashiga rawa. cikin hanzari suka isa suka bude masa .
yasanya hancin motarsa xuwa cikin farfajiyar gidan yayi parking yasoma fitowa yana gyara zaman rigarsa ko rufe motar bai gamayi ba yace karamar tantiriya sai ki samu fitowa gamu agidanmu , kin fitowa tayi tacigaba da rera kukanta me taba zuciya, ganin zata bata masa lokaci yasa yazagaya ya fixgota daga cikin motar yashiga tafiya daita yana zaginta har zuwa parlour'n ammi inda ya tarar da iman da wasu daga cikin family's dinsu .
yana karasa shigowa parlour'n yayi wurgi daita wanda kadan ya rage kanta bai bugi glass din center table ba, ita km sai kuka take kmr ranta zai fita muryarsa a hargitse yace "sis ina ammi? yaya lfy dai ko? "ina ammi da dady yayi mgnr cikin karaji...? ta zubara ta mike tsaye cikin gigicewa ta nufi kitchen amadadin ta nufi bedroom din ammi. ya bude baki zai sake mgn kenan yaji sautin muryar
ammi.
abdul gani lafiya km na ganka hk duk a hargitse ?ammi ki zauna ina dady da kowa da kowa wannan karamar karuwar tantiryar shugaba yan iskan ce ke son gayamuku wasu banzanr magana wanda ni bansan dasu ba yakarasa mgnr yana nuna inda su'ad ke durkushe tana risgar kuka...fuskar nan nata yayi jawur.
zama ammi tayi a daddafe tana kallon inda su'ad ke durkushe gbdy takasa samun natsuwar zuciya hk kawai taji Gabanta na wani irin bugawa da sauri sauri tayi saurin runtse idanunta gam tana karanto addua acikin zuciyarta .
karasawa yayi har inda su'ad ke durkushe tana rusa kuka ya damki wuyanta ta baya wanda yabawa fuskarta daman bayyana sai daya gama kare mata kallon tsab sannan yashiga janta bisa gwiwowinta yana matso daita zuwa inda ammi ke zaune tana jin kmr ana fixgar rayuwarta .
sannan muryarsa a zafafe yace ammi ki bude idonki ki kalli idanun wannan tantiriyar mara kunyar da zantuttukanta ya kasa tsayawa akaina har sai ta dangana da iyayena.
ahankali ammi tasoma kokarin bude idanunta kirjinta na bugawa daf... daf ...tare da daurasu kan fuskar su'ad dake durkushe bisa gwiwowinta ai da wani irin sauri ammi ta dafe kirjinta sbd yadda taji gabanta yabada rassssssee .....tsoro da matsanancin firgici AK yaga ya bayyana a saman fuskar ammi dake zaune jikinta har rawa rawa yake yayinda shi km zuciyarsa tashiga bugawa da karfi.
ita km su'ad numfashinta ne ya soma barazanar daukewa sbd kukan datake cikin tashin hankali, da km yadda ya damki byn wuyanta.
cikin sanyi jiki Tasoma kokarin raba hannunsa da wuyanta ,amman ta kasa kwatar wunyata daga hannunsa .
zuba mata ido ammi tayi sosai tana karewa fuskar su'ad kallo tsab tare da jin zallar faduwar gaba . take kwalkwaluwarta tashiga caji akan wannan fuskar da take kallo agabanta .
ahankali ammi ta kai hannuwanta duka bisa fuskar su'ad ta kamo tana mata wani irin kallo zuciyarta na tsananta bugawa da karfi..
kafin daga karshe tasoma shafa fuskar su'ad jikinta na sake daukar rawa... shi AK km har lokacin yaki sakar mata wuya sai huci yake kmr wani kumurcin maciji.
yadda jikin ammi ke rawa hk murya take rawa gurin cewa "abdulkabir a ina kasamo wannan fuska?
wannan fuskar duk inda take nasanta, fuska ce wace bazata taba bace min ba har illa yauminl kiyamati..
ammi wannan fa itace mahaukaciyar yarinyar dake bibiyar rayuwata.....
a matukar tsawace ammi katse shi ta hanyar cewa "ubanka wannan fuskar ta wuce ka siffantata da mahaukaciya... ....dan ubanka ka sakar mata wuya.... wani irin yammmmmmm yaji ajikinsa tare da cire hannunsa a wuyar su'ad yana kallon ammi cike da matsanancin mamaki..wani abu yaji yashiga bin jikinsa tunda yatsun kafafunsa har zuwa cikin kwalkwarsa idan wani ya gaya masa ammi zata iya zaginsa akan wannan tantiriyar karuwar zai ce karya ne, sai gashi da kanta km agaban yarinyar datake kirarin bata son ya aureta take zagin ubansa.
cikin rawar jiki ammi ta mike tare da mikar da su'ad dake wani irin kuka yarinyar ya sunanki....? menene sunan mahaifiyarki da mahaifinki? a ina gidanku yake? ajere ammi ta shinga yiwa su'ad tmby wanda ita km kwata kwata takasa bude bakinta balle ta amsa mata.
cikin kuka ammi tace dan girman allah ki gaya min wacece ke da sunan iyayenki?
sill su'ad shiru tayi taki cewa komai.
ammi ta juyo a firgice tana kallon AK afirgice "maza maza kaje gidan minister kuzo tare yanzu yanzu ,yau ranar ce mafi dadi da farinciki arayuwata , byn wasu shrkaru da suka wuce " ammi wai tsaya menene hkn kike yi nifa bangane nufinki ba?
a think yau ne rana ta farko da kika soma ganin wannan yarinyar kin santa ne ko yaya? ya sake tmbyrta.
"kaje kawai ka kira min minister shi dady'nka yanxu yanzu shi dai ak gbdy ya rude ya kasa aiwatar da umarnin ammi ,sai wayarsa ya ciro cikin aljihun wandonsa ya kiran number minister , dana dady'nsa tare da sanar masu da sakon ammi sannan yakara da su hanzarta domin amminsa na cikin wani hali kar su dade.
atare motar commission data dady'n AK suka jero zuwa cikin harabar gidan .sukayi paking sannan suka fito suka nufi cikin part din dady.
zaune suke gbdy'nsu har Minister da bai dade da karasowa ba dady'n AK commission da mahaifiyar su'ad wace tunda tashigo itama taji gabanta na dukan uku uku ta dukar da kanta kasa ,sai maman zeey da hjy kakar AK, sai wasu daga cikin yan'uwan ammi kowa agurin kallon fuskar su'ad yake wanda hkn yasa tun kafin shigowar minister itama ta dukar da kanta kasa kmr yadda ummanta tayi tare da saka bakin mayafinta ta rufe bakinta zuwa hancinta.
amman duk da hk idanun jama'ar dake parlour 'n na kanta dauke da tmbyoyi iri iri .
banda dady'n ak wanda shi tuni ya dade da taba ganin fuskar da sukayiwa wannan kallo..
parlour'n ya dauki shiru sosai kusan na minti talatin babu wanda yayi yunkurin mgn acikinsu kafin daga bisa ahankali commission ya katse shirun da gurin yayi ta hanyar soma bayanin abinda ke tafe dasu da km dalilin zuwansu danshi bai wani hankaltu da yanayin da suka ciki ba ....
kafin commission yacigaba da bayaninsa ammi tayi saurin hanzarin katse shi.
ta fuskanci dady'n AK da minister sosai wanda shi alokacin ya matsu yaji wani abu daga bakin ammi ,dan jin dalilin dayasa akayi masa kiran gaugauwa .
cikin rawar murya ammi tace "minister dad'y abdul wani abun mamaki nagani yau " ehem meye shi wannan ? suka hada baki gurin cewa daita hk. mikewa tayi cikin sanyi jiki takarasa har zuwa inda su'ad take zaune tasa hannunta ta dago fuskarta tare da tsaita fuskar ga minster da dady'n ak wani irin zabura minister yayi tsaye yana nuna fuskar su'ad hannunsa na karrrrrrr gbdy har da jikinsa rawa suke ...... yayinda dady shi kallon fuskar kawai yayi yana sake tuno mamalakinta.. da kyar minister yasa
mu ya daidaita numfashinsa tare da sanyawa jikinsa natsuwa amman har lokacin jikinsa rawa yake cikin in.. ina... yace " aunty ina kika samo wannan ........?
mmn sudais ce
SAI KA AURENI DOLE
Chapter 132 · 0% Book details