← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 289

Sashe 128

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

iyayenki dana mahaifina danake ahalin yanzu, ki bar kuka ummana ina tabbatar miki kukanki yazo karshe zan dawo miki su'ad dinki sak ta da abin alfaharinki , bazan gujeki ba ummana . "na dauki kaddarar yadda kuka samar dani domin hk Allah yaso dani daman bata hanyar aure zanzo duniya ba. bazan taba tsallake kaddarata ba ki daina kuka takarasa mgnr tana gogewa umma hawaye wasu na biyo kuncinta ,na daina kuka su'ad kema kiyi hkr ki yafe mana kuskuren damuka aikata wanda ayanzu ko wani naga zaiyi irin abinda na aikata abaya zan bashi shawara .. tana karasa fadar hk tashige bayi tana wani irin kuka ta bar su'ad tsaye, itama kukan take har lokacin. "umma tayi wanka tare da dauro alwala ta fito ta shinmfida pray mate ta tada sallah . itama su'ad bayi tashiga tayi kmr yadda umma tayi sai dai ita kwanciya tayi akan gado dan kawai ta ragewa kanta xugin da zuciyar ke mata . juyi kawai take akan gado ta kasa runtsawa ana cewa bacci barowa ne amman ya gagara daukarta har asuban fari bacci bai zo mata ba. yayinda ita km umma har lokacin tana ta faman jera nafilfili. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 128 · 0% Book details