Sashe 229
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
zuwa wannan lokacin yasan matsalar soyayya ce ke d'awainiyya daita amman yana ji aransa zai iya cire soyayya kowaye ya dasa nashi. sam abdulkabir baiyi yunkuri zuwa duba jikinta ba duk da yadda jama'a sukayi ta zuwa ta bangarensa, wannan abu yayi matukar taba zuciyarta dan haka su'ad ta masa a sallameta ita tagaji da zaman hospital doctor saif yashigo ya iske ana fama daita akan ta tsaya ta kara samun sauki sai shagwaba takeyiwa ammi tana ganin shigowar doctor tayi dif da bakinta . muryarsa a kasalance yace "ammi kmr yadda yaji ana kiranta dashi "akwai damuwa ne? "babu wata damuwa likita mamana ce dai ta takura dole gida take son xuwa tagaji da zaman asibiti. ya d'an saci kallonta yaga zoben hannunta take kallo aransa yace ko ba'a gaya masa yasan zoben soyayya ne ganin ita yake kallo ta hade ranta sosai tana cigaba da kallon zoben. tsura masa ido yayi sosai yakira sunanta" su'ad kiyi hkr gobe Inshaallahu zamu baki sallama ai kinji sauki sosai tayi saurin girgiza masa kai" ok karki damu gobe zaki tafi gida. Shi kuwa ak yana can rawar jikin akan zeey dinsa kasancewar gobe za'a meida aurensu ,a massalacin kenan ranar da za'a sallamo su'ad , hakan yasa ammi tasamu likita yabar tatun sallamar man sai wani sati sosai dr saif yaji sosai dan baya son rabuwa daita . washegari da safe aka d'aura auren zeey da abdulkabir akan sadaki million daya wanda hkn yasa dady karan kansa yayi shock sai da abun girgiza zuciyarsa har ya saka ayar tambaya akan lamarin ,yakira ak byn d'auri aure yayi masa fada akan sadakin daya bayar yayi yawa albarkan aure ake bukata abdul ba yawon sadaki ba "dady karka damu shima sadaki me yawa yana kawo albarka aure ni da kumun addua kawai akan auren nan... aranar da aka daura auren zeey da abdul babu wanda yayi ganganci sanarwa su'ad sannan kuma a ranar zeey ta tare a shohon gidanta na green hill estate.. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE