Sashe 76
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
juya ba dan ranshi yaso ba, koda ya isa bakin kofar bai ce daita komai ba dan bai jin zai iya aikata abinda dady yace, dan hk yakarasa ya kai hannunsa kan nata domin fixgota ,wani irin shock yaji ajikinsa tun daga tsintsiyar kafafunsa har zuwa tsakiyar kanshi take an jona masa wutar lantarki. take jikinsa yasoma rawa yadda yaji ajikinsa hkn ce takasance daita dan hk da sauri ya fixgo hannuta da karfi yayi wurgi daita cikin tsakiyar parlour yana sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da kallon hannunsa . muryarsa ahankali yace dady ina zuwa kabani minti biyu yanzu zan fito.? nakara maka minti uku akai kashiga ka fito ina jiranka. tsaki yaja akasan ranshi tare da dago mayatattun idanunsa wayanda suka koma ja ya daurasu akan agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa. lokaci ya wuce sosai tsaki sake ja yashiga bedroom dinsa hade da shigewa bathroom, bathtub yashiga yayi wanka ya wanke hannunsa daya taba jikinta dashi sosai sannan ya fito .. ya saka wasu kananan kayan dagon wando baki da riga shirt itama bata ya fashe ilahirin sansar jikinsa da turare , ya sake fitowa zuciyarsa na matukar bugawa da karfin gaske. ya zauna akan kujerar dake facing din dady, murmushin takaici dady yayi yana dubansa tare da girgiza kai. yayinda su'ad ke zaune rakube a gefe kanta ta soke akasa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta ta dago ahankali sakamakon kamshin turarensa daya kaiwa hancita ziyara, ta daura idanunta akansa yana zaune yana wani cincin magani,idanu ta tsura masa sosai tana kallonsa kmr zata cinyeshi, gbdy ta manta ko a ina take da gaban wanda take zaune ... har sai da dady yayi gyaran murya sannan ta dawo cikin hankali da natsuwarta ta sake sunkayar da kanta kasa. dady ya sake duban ak cike da hade rai dan ma kar ya kawo masa rainin sense yace wace wannan yarinyar? yayi mgnr yana nuna inda su'da ke zaune sunkuye da kanta tsaki yaja acikin zuciyarsa sannan ya bude bakinsa da kyar muryarsa can kasa kasa wanda idan ba saka kunne mutun yayi ba bazai ji abinda yace ba. yace dady yarinyar nan ce... yana gama fadar hk ya koma ya dan meida bayansa da kujerar dayake zaune kirjinsa na bugawa tare da runtse mayatattun idanunsa .. amman me nace maka akan yarinyar? dady banzan iya daya daga cikin abinda kace min ba sbd bata cancanci hkn ba. i can'tmarry her dady coz she's not my type i can't marry her coz she's prostitute.. i can marry her coz.....short up dady ya bugasa tsawa a fusace kai meye ba dan iska ba ai irinta itace daidai da aurenka ba kamilar mace irin zainab ba, wace ta tsare imaninta tare da tsarkake zuciyarta.. kai kasan baka bukatar mace irinta meyasa kake aikata barna. ina tabbatar maka wannan ita irin matar data dace da kai.. dady yakarasa mgnr yana furzar da iska i can't marry her coz she's not my type i can't marry her coz she's prostitute shine kawai abinda su'ad ta dinga maimaitawa acikin zuciyarta .yayinda mgnr ta dinga mata yawo a ilahiri gangar jikinta da kwalkwaluwarta ,wai meke shirin faruwa dani ne? meyasa zuciyata ta kamu da matsanancin son wanda bai kaunata oh my God what wil i do now? take zuciyarta ta bata amsa da ki tsaya kiji abinda mahaifinsa zaice first, kafin kinsa matakin dauka akaro na karshe. dan hk ta goge hawayen dake ta tsiyayowa daga kwarnin idanunta a tun sanda ak yasoma mgnr bazai aureta ba idanunta ke kansa tana kallonsa tana zubar da hawaye ganin dady yaki sake cewa komai , yasa tasoma jan gwiwowinta zuwa inda AK zaune tana kuka tana rokonsa karka ce bazaka aureni ba... da ka gujewa aurana gara ka kasheni na huta da bakincikin wannan rayuwar ta juyo tsaitin dady . dan Allah dady kace abdulkabir ya aureni ....wlh ina matsanancin son shi da gsky . zanyi duk abinda yake so... zan .. wata uwar razananniyar tsawa ya buga mata ta hanyar katseta da hannunshi daya, wlh idan kika sake furta wannan bazan kalmar zan miki dukan mutuwa.. na yarda ka kasheni abdulkabir...... . wlh ka kasheni matsawar baka raba gangar jikina da numfashi ba bazan daina furta maka wannan kalmar ba... dau taji saukar mari akan kuncinta ....take wasu taurari sun gilma ta cikin idanunta . tasa hannunta ta dafe daidai inda hannunsa ya sauka tana kallon cikin kwayar idanunsa . maza maza ki bar nan ya nuna mata hanyar fita wallahilazim na sake ganin kafafunki a kofar gidan sai nasa andaure min ke muddin rai stupid kawai wace batasan ciwon kanta .. jikinta a sanyaye ta Mike tsaye kirjinta na harbawa da karfi tana jin yadda kirjinta yayi mata nauyi tmkr an daura mata dutse. take wasu zafafan hawaye suka shiga ambaliya suna zubowa akan kuncinta. har ta juya da niyyar barin gurin dady yakirata . ta juyo ahankali idanunta cike da hawaye, tausayinta ne ya sake kamashi muryarsa a matukar sanyaye yace ki kara hakuri, ni din nan da kike gani nine mahaifin abdulkabir ..... ina me tabbatar miki matsawar abdulkabir mijinki ne bazai taba tsarewa aurenki ba ....kiyi tafiyarki Inshaallahu zan nemek... manage pls .......... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE