← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 289

Sashe 87

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi masa sannu tare da kiran wayyohhhly allah yarinyar nan tana son kasheni dan babu me aikata wannan aika aikan sai ita. ai ko ya jigatuwa samuel ya jigatu sai haki yake yana rike kirji, ran AK kuwa in yayi dubu yayi mugun baci har ya ji baxai iya barin su'ad hk nan ba sai ya dauki mummunar mataki akanta. washegari tunda sanyin safiyya ak yasa police sukayi arresting din su'ad ita da ore da ganiya zuwa sa'c police station .akan laifin yunkurin yin kisan kai har sau biyu. tunda yan sanda suka tasa keyarta komai ya kwance masa natsuwarsa tasoma barin gangar jikinsa yayinda hankalinsa yayi mugu mugun tashi yarasa meke masa dadi. har yaje office ya dawo abun na taba masa zuciya. ranar kowa yagansa yasan yana tattare da damuwa dan ko agurin aiki kallonsa kawai ma'aikata keyi sbd ganin hankalinsa baya tare da gangar jikinsa . bai bi takan kowa ba yashige part dinsa kai tsaye ya kulle kansa. kwana nan su su'ad uku a police station cikin na hudu ya bada umarnin a sakosu .ko suna fitowa suka sake wani sabon shiri wannan karon akan onye ne sunyi rantsuwa sai sun rabata da ak ko tawani hali ne. duk wannan bidirin shirin bikin da'ake ake shirin gabatar acikin kwanaki goma dayayi saura akil bashi da masaniyya sai yau hankalinsa yatashi matuka har ya kai ga kiran number zeey tana dauka yace wai aure zakiyi tace injiwa ? atsawace yace inji uwarki da ubanki manufukar Allah to wallahi ki kwana da shirin sai dai ki tabbata matan mutun biyu .. domin duk wanda kika aura wani ya aurawa bazan barki sai kinyi da kinsani yin aure aboye batare da sani ba ki zana calander daga yau kwanan watan tashin hankalinki ya tsaya km kizo yanzu excellent hotel ina jiranki abukace nake dake muryarta a hasssle tace baza'azo ba sai kaje kayi duk abinda zakayi dan isaka kawai zako kisha mamakina wlh zan nuna miki ke karamar yar' iska ce tun bai gama mgnr ba ta katse wayar. tundaga ranar tarasa kwanciyar hankali kullun akil sai yakira ko ya turo mata soko gbdy ya addabe rayuwarta. 6:pm na ranar yau zeey da iman suka dawo gida agajiye kai tsaye bed room dinsu zeey ta nufa tacire kayan jikinta ta daura towul tashiga wanka.. Itako iman daman da yunwa ta dawo gidan dan haka tanufi kiching ta bude foodflask taga ba irin abinci da take so Bne faten doya ce datasha dry fish Dan hk ta dafa indomi. Ta dawo falon tana zabga uban tsaki wai ita tagaji. Ta ajiye plet din indomi kana tanufi firij tadauko madarar hollandia ta bude tadan kurba tanufo kan kujera Ta zauna da hollandia din tanasha tana cin indomin. Sai Data gama cin indomi tas ta maida plet kitchen ta dauki sauran holladia ta nufi dakinsu. Daidai Zeey tafito daga wankan tadauro alwala tana zaune akan kujerar dressing mirrow tana shafa manta me matukar kyau . kallonta ta tsaya yi sosai taga tayi wani masefar kyau sai ma taga yanayi Gyaran da aunty Zeey din take samu daga matar da ammi ta kawo mata ya amshi jikinta domin tayi kyau sosai duk da kullum cikin tunani take wanda tarasa dalilin hk. karasa Shigowa dakin iman tayi tun kafin takarasa shigowa Zeey tajawo hijab dinta tasa. Tsaki iman tayi tareda karasawa kan gado tazauna tana shan hollandia dinta tace tareda yatsina baki "Kyadeji dashi daga ganina kmr namiji kike wani sa hijjab aini wlhy na kosa allah yakawo ranar auren Naku da yaya kije can kiyi tamasa wannan kauyencin naki. Hade rai Zeey tayi tare da daukar robar manta ta jefama iman.. Allah iman kin mugun rainani Amman zaki gane Baki da wayo sai randa na tafi na barki naga wanda zaki komawa sawa ido. Kaucewa iman tayi robar bata sameta ba ta fada kan gadon kusa da pillow iman tace "Uhum ni bama wannan ba wlhy wani iri kewarki nike ji duk kwanakin nan Daria Zeey tayi tace a she dai ina da amfani. Sassauta murya iman tayi tace sosai ma aunty ai babu dadi mutun ya kwana shi kadai na rigada nasaba wlh Dan Allah aunty Zeey kice kin fasa auren.. zaro ido waje zeey tayi Sosai tana karayin wata dariyar tace "Toh yarinya baki da hankali auren zance na fasa kinsa shekaruna nawa yanzu 26 fa . kema Yaci ace kin tsaida masu xuwa gurinki. Tasowa iman tayi ta iso inda Zeey take ta dafa kafa arta kmr marainiya tace "Haba aunty dan allah kiyi hakuri nifa har yanzu yarinya ce tukun ban wani isa aure ba. Hade face Zeey tayi tace "Toh ni ina ruwana yanzu dai kiyiwa kanki fada wlh shawara nike baki karki ce sai kingama karatu as ending Ki rasa mashin shini takarasa mgnr tana dry. Kara marairaicewa iman tayi tace "Haba plxx dan allah ki taimaka kiyi min addua. Nasamu miji irin wanda zai kula Dani kmr yadda Yayana yake kuladake. Murmushi Zeey ta sake Yi tace iman allah ya shiryaki .da sa ido. ciki ciki iman tace sa ido fa ai naga yadda kike sonsa ne... Shi km sai ya dunga wani lallabaki.. Zeey tace " me kikace? Nan takara marairaicewa tace ni bance komibafa" tafada hakan tareda mata kwalo.. Murmushi Zeey tayi tace "iman indai ina tare dake dole sai kin sani nishadi duk da tarin damuwar dake cin zuciyata" nan idanuwanta suka canza sbd tuno akil da yadda yake neman ruguza mata komai.. Iman tace " haba my auntY karkiyimin haka mana bayan munata nisha i zaki soma kuka plx saki ranki kinji . Zeey tasoma kuka .iman tashiga tmbyrta Amman takasa fa a mata damuwarta. sosai iman tausayawa rayuwarta . amman tunani ko sbd rabuwa da zatayi da iyayenta ne. Dan hk tace haba aunty meyye abin damuwa keda auren gida zakiyi kullun idan kinso kina gida nifa wayasan inda aure zai kaini.? Zeey tarasa me zatace mata sbd tabbas bata san boyayen Al'amarin dake yawo da rayuwarta ba. Nan dai iman tai Ta lallashinta harta samu ta hakura tasa riga da siket na material. material din ya amsa jikinta ta dauki hijjab dinta tasa alokacin an kira sallar la'sar nan ta ta a salla ta idar tasoma kokarin shiga kichin kasancewar hanatu me aiki bata nan taje kauyensu amman jibi zata dawo koda ta nufi kitchen alokacin iman na bayi tana wanka. Jollof din shinkafa da taliya ta daura nan da nan gidan yadau kamshi Kamshinne yasa iman tayi saurin saka kaya doguwar riga mara nauyi me kalar ruwan kasa daman tana period Dan hk no need of sallah ta nufo kitche din tun kafin takaraso take cewa "Yammatan yaya wai wannan kamshi haka kai dagaji girkinnan sai yafi na kullum dadi'' Zeey dake yanka albasa idanunta na ruwa tace" kedai kika sani ni kizo ki karasa yanka albasar nan ta isheni" Karasawa iman tayi tajawo kujera tazauna taci gaba da danna wayrta tace "tab kinfa sanni inna yanka albasa se inyi kwana hudu hannuna na warin albasa duk wankewar dazanyi ma hannun baya fita" Zeey ta goge hawayen dake zuba saboda zafin albasar tace "Bakomi idan kinje gidan mijinki naga uban da zai miki. Kai Kai matsalata dake aunty zance bai wuce miji aure... OK ni din kike cewa hk barin yayanki ya dawo. Iman tace aah yi hakuri anty ki dai hadani da wani banda shi. "Uhum da shi zan hadaki yarinya Ki gane kurenki. To kawo nayi miki shi kenan a'a barshi banaso znyi komi ke dai zauna ki tayani hira kawai Dariyar farin ciki iman tayi tace shiyasa nake sonki... nan iman tafara bama Zeey labarin littafin *GADAR ZARE* *Na hauwa A Usman jiddar* kasancewar ita meson karance karance ce sabanin Zeey datafi meida hankalinta akan kallo . sosai labarin yayima Zeey dadi sannan ya tsaya mata a zuciya barinma balarin Abdul da zaid da zarah Ta tausaya musu sosai. Iman tace "ai ina baki labari ,dadi ya barki . Allah aunty Ki dinga karatun novel yana dabe kewa uwa uba GA darasusukan dake ciki. Ammam Kinki ,dana turo miki novel din kin karanta da kanki kiji dadin dake cikin novel din yanzu hk ana kan rubutashi. Murmushi Zeey tayi tana zuba jalof din a kula wanda yaji dry fish kana Zeey tace "kai iman naji dadin novel dinnan gaskia muje ki turomin baza'a barni abaya zanso naji karshenshi . iman tace angama matasss Zeey tayi murmushi ta nufi daninig domin jera musu abincin da ruwan faro da fresmilk suka dawo parlour akan karpet din dake tsakiyr falon suka yada zango suka soma cin nasu . Iman ta kunna makeken t. v din dake parloun. .kowa ya dauki spoon suka faracin abinci iman naci tana santi. Zeey ta girgiza kai. Iman takai lomar abinci baki tace "Wlhy Yayana ya huta sam bazeji wata mace ta burgeshiba . Freshmillk Zeey takai bakinta tadansha kana ta ajiye kwalin tare da sa murfi ta rufe tace "Meyasa kikace haka " Yauwa kinga kinada komi da ana miji . Zai gani ajikinki ya rude musamman ma hips dinki tako ina allah ya wadataki ga iya girki toh mezesa namiji ya nemi wata mace inhr yanada ke.. .dry Zeey tayi tace "Hmmm iman kenan shiyasa nace Ki tsaida daya cikin masu neman aureki da alamu kema fa aure kike so. tab aunty bar wannan zance ba yanzu ba.. Murmushi Zeey tayi tace "ba zncen wasa ba fa kiyiwa ki Allah kibada himma if possible ayi danamu. aa ku dai kiyu naku ni yarinya ce wlh sannan ta daga ruwa tasha tace "Alhamdulillahi... Na koshi itama Zeey ta cire hannuta iman ta kwashe kwanonin takai kitchin . sai da ta wankesu sannan ta dawo parlour . daidai lokacin da ammi tashigo parlour'n tana zaune alokacin ita km Zeey. bata parlour'n. tana bedroom ta fada toilet ta dauro alwala alokacin anyi sallar magrib dan haka ta tada sallah Iman na shigowa ta ga tana sallah dan haka takwanta a gado takunna wayarta tahau online. Zeey tana idarwa tasa kayan barci ta kwanta kusa da iman. yayinda ita man ba tama sani da ta kwanta ba tariga datayi nisa aduniyar yanar getso . rikici ne ya barke atsakanin ak da onye a xiyaran data kawo
Chapter 87 · 0% Book details