Sashe 102
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallahu alaihi wa salam :la yadkulul mala'ikatu baitan fiy kalbu wala tasa'awiru* *Allah 's messenger saw said :angels do not enter a house wherein a dog or photographs* page 39 jikinsa na tsuma ya fito yakaraso gareta ya tattarota ya rungumota a jikinsa . " yasoma k'iran sunanta yana girgiza fuskarta Zainab zainab yaji shiru ya sake tattarota jikinsa ya kai hannunsa daidai tsaitin hancinta yaji bata numfashi take ya gane suma tayi da sauri Williams yakarso ya taimaka masa suka cicccibeta ya sanyata abayan motarsa ya zagayo ya bude mazaunin direba yashiga aguje ya fige motar ya bar gidan ya nufi wani babban asibiti daita, yana isa yaja burki da karfi kiiiiiiiii yayi parking motar ya fito. ko tsayawa rufe motar bai yi ba ya sake ciccibarta ya nufi cikin reception daita. yana kiran likitoci help.. help.. abinda yake iya furtawa kenan hankalinsa a mutukar tashe kafin kace me tuni doctor's sun taru akansa suka karbi zeey a hannusa . akayi cikin Immagecy room aka soma bata taimakon gaugauwa sai data dawo haiyacinta sannan aka soma treatment din raununka jikinta tunda ta farfado take zubda haway wahala da tausayin kanta yayinda goshinta har lokacin tsiyaya jini yake. " kuka take sosai tmkr ranta zai fita tare da sambatu yanxu abinda abdulkabir zai min kenan wani irin mahaukacin kishinsa ne ya dinga taso mata tare da bugar mata da zuciya yanxu yazatayi da rayuwarta hada saurayi da yar'daba mara kamun kai da natsuwa .? wayyohhly Allah nah .. sambatu kawai take xubawa sai da doctor yace tabar kukan hk dan asamu ayi mata dinki gurin. byn angama yi mata treatment aka kaita wani dakin . ak ya shigo dakin da aka kwantar daita, ta tsura masa ido kawai tana kallonsa idanunta cike da ruwan hawaye tana jin yadda kishinsa ke tasawa yana rike mata makoshi. yasamu guri ya zauna tare da kamo hannuta daya cikin nasa tun kafin yace wani abu tasoma mgn cikin muryar kuka da zafin rai my life yanxu abinda zaka min kenan ashe kana tare da wata budurwar amman banida masaniya sbd yanxu ka daina sona ko? karki ce hk zeey ki dai yi hkr ni kaina bansa yadda zanyi daita bane. , ta addabe ne ta damu rayuwata amman dai yanzu kibar zance har ki samu sauki zan miki bayani komai akan yarinyar. " wani irin banza bayani zaka min akan lamarin yarinyar da zan fahimta kawai kace kai ma kasoma rage lokaci da yan'mata, da alamun ma kasoma son yariyar amman wlh kaji karasa wace zakayi tarayya daita sai wannan, har km tana ikirarin tana sonka bazata iya rayuwa babu kai ba. wlh ina tabbatar maka da zan iya rayuwa babu kai wallah da yau na barka bari kuwa na har abada dan wlh bazan iya shearing dinka da wata mara mutunci ba. surutai kawai take xuba masa marasa kan gado wanda shi kansa yasan bata cikin natsuwarta dan hk yayi mata uxiri dan yasan ba halinta bane ranta ne ya baci dan hk yayi murmushi yasoma kokarin shawo kanta da kyar yasamu ya rarrasheta tace taji amman a sallamesu . daga hospital suka wuce gida. har suka isa gida babu wanda yace da dan'uwansa komai tana fitowa daga motar ko kallon inda yake zaune batayi ba dan har lokacin haushinsa take ji a zuciyarta . da sauri ta juyar da kanta gefe dan kar dady daya fito yanxu ya ganta . ai kuwa ya ganta cike da tashin hankali dady yak'araso wajen da take tsaye zainab meya sameki? waye yayi miki wannan illar? juyowa tayi ahankali ta kalli ak dake kokarin fitowa daga cikin mota fuskarsa dauke da ala'mun tsoro tace dady a sabon gidan yaya danaje gani ne muka samu matsala da wata yarinya tayi min hk. wace yarinya ce kenan dady ya juyo yana fuskantar ak . shiru yayi ya kasa cewa komai ba da kai nake mgn ba kana jin mutane.. ganin dady yasoma daukar zafi yasanya ta bar gurin tayi shigewarta ciki. zuciyarta sai faman k'una take dakinsu ta nufa ta fada kan gado ta kwanta tana kuka wiwi wannan bakincikin da me yayi kama? kodai zata hakura da ak ne duk da irin son da take masa ta hutawa rayuwarta. dady ya sake tsare shi da ido sannan ya sake tmbyrsa da kai nake mgn wace yarinya ce ta aikatawa zainab hk? a dan tsorace ya bude bakinsa da kyar yace yarinyar nan ce..... kaga irinta ko ? kaga irin abinda nake gudar maka bakaji ko ina tabbatar maka matsawar baka kulle wannan matsalar dake kokarin kunno kai cikin rayuwarka ba ,ba kai babu kwanciyar hankali . well duk abinda kagama kayi rayuwarka ce. " inda kayi yadda nace ka zauna lfy akasin hk km kai kasani. yana gama fadar hk ya juya ya wuce. cike da sanyi jiki AK ya nufi hanyar part dinsa zuciyarsa tmkr zatayi bunduga kwanciya yayi akan makeke gadonsa tare da runtse mayatattun idanunsa wanda suka canza kala zuwa ja duk wani tunaninsa ya koma kan mgnr dady . anya kuwa zan iya daukar shawarar dady kuwa? yayi kanshi tmbyr ina bazan taba iyawa ba wallahi ai gara na mutu babu aure da dai na auri yarinyar nan to yanxu me solution ? ya sake tbmyr kanshi akaro na biyu take zuciyarsa tabashi amsa kawai da zarar an daura auranka da zeey ka dauki matar ka kabar kasar . da wannan amsar yassamu natsuwar zuciya ,har kuzarin jikinsa ya dan dawo yasamu yashiga wanka. zeey kuwa har lokacin kwance take tana tana kuka da tunani mafuta ta janyo daya daga cikin pillow 's dake kan gado ta rungume ajikinta anya kuwa zata iya rabuwa AK tacigaba da rayuwarta? ta wani bangaren na cikin zuciya ne yake me mata wannan tuni ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye masu dumi suka ringa tsiyoyawa daga cikin idanunta. tabbas ta kara yarda da mgnr mutane da ke cewa son maso wani take tarasa wani irin so ne takewa ak wanda yasanya ta kasa fitar dashi aranta duk da halin ko inkula dayake nuna mata . ta girgiza kai so bai yi ba arayuwa . tasamu tsayin lokaci a kwance akan gado tana murkususu babu abinda yake cin xuciyarta sai son ak da matsanancin kishinsa dole ne ko ta wani hali tarabashi da yarinyar zatayi hkr zuwa lokacin data tare agidansa amatsayin matarsa.. zatayi magani abu da kanta dan dole tabar mata AK. koda ammi ta dawo ta ga yadda goshin zeey da bakinta suka suntume taji abinda ya faru fada ta dingayi gbdy ta daura laifin akan ak inda take cewa idan ma son yarinyar yake tun wuri ya daina dan baza taba barinsa ya aureta ba. Matashin saurayi ne, me cike da tsantsar kyau da kamala mara iyaka, had'e da cikar zati da nagarta acikin hadaddiyar motarsa kira henessey akan titin police mess yana tbmyr gidansu su'ad duk wanda yagani ya tbmy daya kira sunan su'ad sai suce basu santa ba alhalin km sun santa . har dai ya hadu da wata mata yace ina wuni ta amsa masa cike da sakin fuska . yace dan Allah gidansu su'ad nake tmby ? tace wace su'ad din ba dai wannan tsinanniyar yarinyar me fadan tsiya da jaraba a unguwa ba ? kai ko ina kai ina wannan tsinanniyar yarinyar daga ganinka dan mutunci ne . hade rai saurayin yayi sosai yace dan Allah tsohuwa ki daina zaginta dan wace nake nema ba mafadaciya ba nutsatsiya yariya ce me kamun kai . kai ni yi min shr wanann dai dana sani yar banza yarinya ce amman ga gidansu can da ka karya wacce kwanar karshe gida na hudu daga hannun dama nan ne gida part dinsu shine na farko daka shiga. ok na gode sosai. kai tsaye gidan da akayi masa kwatance ya nufa yayi parking motarsa akofar gidan ya fito ya nufi cikin gidan. tsaye yake abakin kofar part dinsu yana nocking din k'ofar d'akin kusan minti goma tsakani yana tsaye hannushi d'aya zube cikin aljihun wandonsa yana k'arewa yanayin compound d'in gidan kallo. Umma wacce gabanta ya bada ras ras a tun sanda taji sautin kwankwasa k'ofar part din nata, a hankali ta shiga karanto addu'ar neman tsari tun kafin ta kai ga mik'ewa tsaye ta k'arasa gurin k'ofar, ta d'aura hannuta kan handle ta bud'e k'ofar jikinta na wani irin rawa da kirma..... tana gama bud'e k'ofar d'akin idanunta ya sauka akan wannan matashin saurayin dake sanye cikin wani hadadden suit riga da wando ash colour da yar cikinta white sai cover shoe d'insa dake sanye da kafafunsa suna zuba kyalli da d'aukar ido . kallo daya zakayi masa ka dauka ma'aikacin banki ne ko wani officesa babba me zaman kansa. take gabanta ya yanke ya shiga dukan uku uku zuciyarta ta shiga dokawa tana tsalle sbd tasan halin fitinsnniyar d'iyarta bakinta na kirma gurin ce masa lfy, wa kake nema? Murmushi yayi wanda ya sake fito da ainihin siffar kyawunsa fili . "muryarsa a hankali ta fito cike da sauti mai dad'i gurin cewa lfy lau Mama ni abokin Su'ad ne tare mukayi karatu daita a unilag nazo gaishe ta ne ... Umma ta zaro idanunta waje tana sake karewa wannnan kamilallan yaron kallo wanda daga ganinsa kasan dan gidan mutunci ne me tarbiya da natsuwa. amman wai yazo gaishe da su'ad ne.. jikinta na rawa tace wace su'ad din? Take yasoma zayyano mata kamanninta tun bai karasa ba ta katse shi ta hanyar cewa shigo daga ciki tana nuna masa gurin zama, sakamakon ganowa datayi d'iyarta dai yazo nema da gaske, sai daya rusuna ya gaida ita kana ya zauna on expecting yaji sautin muryar umma ta soma mgn cikin yanayi nason yin kuka tare da soma zayyano masa munanan halayen su'ad din . Ai su'ad bataji magana kullum cikin fad'a da mutane take kullun cikin shan taba da giya da fashefashen kwalabai take ga case's dinta da yansanda bazasu lisafu ba. kullum sai ankaita police station sbd jarabarta da finita had'i da mugun halin irin nata takarasa mgnr tana me fashe masa da wani irin gigitaccen kuka me tab'a zuciya. , yayi shr tare da gyara zamansa yana duban umma