Sashe 154
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yake ya ajiye shi yazo yanzu tana nemansa. koda suka iso gidan gbdy hayaniya ce tacika koina a gidan kasancewar sauran dagin wadan da basu samu damar hallatar biki da farko ba wannan karon sun samu damar karasowa. jikin ammi da su'ad a matukar sanyaye suka dinga rasa jama'a suna gaigaisawa tare da yi musu sannu da zuwa har suka samu suka karasa dakin ammi , a dakin suka tadda AK tsaye jikin window hannusa akan glss din window yayinda dayan hannunsa ke cikin aljihun wandonsa na dan jujjuya jikinsa. ammi ta dubi inda yake tsaye tana kallonsa cike da matsanancin rauni bata san sanda hawaye suka shiga zubo mata ba, su'ad naganinsa tsaye ya wani hade rai kmr an aiko masa da sakon mutuwa ta juya da sauri ta bar dakin zuwa nasu eiman ,nan ma dakin cike yake makil da kawayen zeey da yan'uwa . juyawa tayi ahankali ta nufi bayan part din AK na gidan zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu da karfi sai lokacin hawayen datake kokarin makalewa acikin kwarnin idanunta yasamu nasarar zubowa ta durkushe agurin tana kuka me cin rai ita kai tasan yadda take jin zuciyarta tare da tasani mara iyaka. shi kuwa AK ganin yadda ammi ke kallonsa hawayen idanunta na tsiyaya wasu na sake zubowa ,yayi saurin karasawa gareta tare da rikota hankalinsa a matukar tashe "lfy ammi? "me km ya faru dake waye yayi miki wani abu? "ni ne ko ammi? "nasan ma ni ne nayi miki wani abu, ammi dan girman Allah ammi ki daina zubar da hawayenki akaina kukanki bakaramin tashin hankali da maseefa bane gareni.. jikinsa na rawa ya zaunar da ammi akan gado shima ya dan dosana agefen gadon kusa daita ya zauna wanda har lokacin hawaye ammi yaki tsayawa, yasa duka hannuwansa yana goge mata hawayen "kiyi hkr ki daina kuka ki gaya min laifina gareki wanda yasa har kike zubar da hawayenki hk. sautin muryar ammi yaji ya doki cikin dodon kunnuwansa "baka min komai ba sai dai ina kukan bakinciki ne, ina kuka ne adalilin wani abu da yataso min me mahaminci nan tashiga koro masa abinda mlm yace takarasa mgnr tare da cewa nasan bazaka taba min amfanin ba ta wannan fanin......... . naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana me dafe goshinsa sbd jin dayayi kansa yayi mugun sarawa "yanzu ammi dan wannan matsalar kawai kike hasarar hawayenki? "dole nayi kuka abdul wannan matsalar ba kawai bace sbd nasan bazaka taba kasancewa virgin ba . sake sauke wani naunauyen ajiyar zuciya yayi tare da kiran sunanta a sanyaye..... ammi ta dago idanunta tana kallonsa batare da tace masa komai ba "ammi ya sake kiran sunanta a karo na biyu wallahi tallahi Bil'lahilazi kinji rantsuwar dan muslimi kenan ban taba kusantar wata "ya" mace ba arayuwata da suna zina byn romacing, duk iskancina a iya romacing kadai na tsaya. a mutukar firgice ammi ke kallonsa cike da matsanancin mamaki jin abinda ya fada "hk ne ammi matsawar kin amince da rantsuwar dana miki ,, ko alqurni aka bani zan rantse dashi akan bantaba taka diyar kowa ba,. "sai dai ita su'ad din da kike mgnr akanta kina Da tabbacin babu wanda ya taba kusantatarta? bakaramin dade ammi taji ba duk da har lokacin zuciyarta na cikin damuwa," karka min karya abdul Allah iya gskyta na gaya miki ammi" ammin da kike zargina ita su'ad din fa? babu ruwanka da mgnr su'ad "babu ruwana kam tunda kowa yasan yar jagaliya bazata taba samun wannan martaba ni yanzu bakincikina daya ta yaddda ita zan fara kusanta ba zainab ba shi yasa ni gaky sai dai muje ayi mata gwajin HIV ammi ta zaro ido waje, da wa kenan za'a yi gwajin HIV? "da su'ad man idan na dauki kasadar aurenta ai bazan dauki kasadar daukar cuta ba, take ammi ta birkice masa wallahi babu inda zata wani gwanjin HIV idan km ka matsa sai anje zan bata maka rai . "shikenan ammi nabar mgnr sbd banida ja da mgnrki Duk abinda kika ce shi zanyi banida mafita , bana son su'ad bana son aurenta amman kika tirsasani kisawa ranki matsawar na auri su'ad ,ki tabbatar da zaki dauki kasadar rasamu wata rana yana gama fadar hk ya mike a matukar fusace ya nufi kofar fita daga dakin tare da nadamar xuwansa. zaune su'ad take gaban ammi tayi shr tana kallonta itama ammi kallonta take tare da nazarin yanayin da ta shiga tun lokacin da suke gaban mlm , sai data gama nazarinta tsab sannan ta soma mgn cikin sanyi murya "mamana nasan kin rasa budurcinki ko? su'ad dake zaune taji zance daga sama yayiwa kirjinta darar makiya saurin kallon ammi tayi zuciyarta na wani irin tsalle ki sanar min gsky idan kin rasa budurcinki a gurin wahalallun rayuwar da kika shiga . cikin matsanancin tsoro su'ad tashiga girgizawa ammi kai sannan bakinta na rawa tace "Allah ammi banta aika wani abu makamanci hk ba take ammi ta saki fuska cike da farinciki mara misaltuwa kafin tacigaba mgn "mamana da gaske kike kina tare da budurcinki har yanzu ko km dai kina son yi min wasa da tunani ne? tsuru su'ad tayi mata ido tana kallon ammi tare da jinjina mata kai rikota ammi tayi da sauri ta mannata da kirjinta sbd tsabar farinciki "kai kai Allah dai yayi miki albarka Allah jikan mahaifinki Allah yayi miki albarka Allah yasa ki gama lfy "daman duk wannan tashin hankali da maseefun bai saka kin zubar da mutuncinki ba kai naji dadi sosai wallahi banyi tunani kin tsira da budrcinki ba ammi takarasa mgnr tare da riko hannun su'ad cikin tana murmushin jin dadi . yadda maman zeey ke fakaicewa tana dirkawa diyarta magunguna mata a boye hk ma ammi take bawa su'ad maganin mata wanda ita su'ad din har ta soma gundura da shan wadan nan magunguna da'ake banka mata kullum. kmr wancan lokacin data daukowa zeey me gyaran jiki hk ma wannan karon ma yakasance ta daukowa su'ad sai dai wata mata ce daban sabanin wace tayiwa zeey. inda me gyaran jiki tashiga aikin daya kawota cikin kwana biyu har fatar su'ad ta sauya tayi wani irin azababben kyau ga wani sihirtaccen kamshin turaren amare na musamman dake tashi ailahirin ajikinta duk inda ta wulga sai tabar kamshin turarenta me matukar kama jiki kana ganinta kaga amarya sak, tayi haske fatar jikinta tayi luwai luwai sai sheki take da daukar hankali kmr ka tabata jini ya fito jikinta yayi wani haske na ban mamaki asalin farinta na ainihi ya sake bayyana idan kaganta sai kaji kmr ka sureta ka gudu. musamman ammi take ware lokaci sosai ta sake shirya su'ad da kanta tana sake dirka mata maganin mata, dan karta zama baura agurin mijinta sbd lura datayi da maman zeey ta diyarta kadai take musamman zata saka Zeey gaba babu kunya balle tsoron allah tana bata hakin maye. tun bayanin da ammin tayi masa akan zance mlm , ya dauki tsanar duniya ya daurawa su'ad ko kallonta baya kaunarki yi balle ya daura idanunsa akanta ya sake canzawa tare da jin mugun tsanar su'ad din cikin zuciyarsa, gbdy duk wani salon iskancinsa daya soma ajiyewa ya dawo shi sabo fil.. babu abinda ke shiga tsakaninsu sai mugun kallo da harara wulakacin da musgunawa hade da zagi marasa dadi ,tare da sake jaddada mata kalmar karuwanci . wani sa'in ma har da gayya yake hadawa gurin yiwa zeey wasu abubuwan da wasu salon iskanci yayinda gefe guda km tunani su'ad na nan makale cikin zuciyarsa. sosai aka shiga hidamar auren,, umman su'ad batazo ba amman ta wakilta wasu daga cikin mutan unguwarsu wadan take mutunci dasu suzo su wakilceta, sun hallarra domin dasu ake ta duk wani shige da fice acikin gidan . kuka sosai ta kwana tana yi har waye washegarin daurin aure wanda hkn yasa ta tashi batajin dadin jikinta dan gbdy ko kwakwarar motsin takasa yi sakamakon tuzarcin da cin mutuncin da ak yayi mata a daren jiya agaban zeey . ita din auren saurayi da buduwar zasuyi ba'a auren saurayi da bazawara ba sweet baby ki daina taba hankalinki akan wannan har kiyi kishi daita, kin zartata a komai sosai su'ad ke kuka lokacin da komai ke dawo mata eiman ce ke rarrashina dan Allah aunty ki share hawayenki ki daina kuka yau ranar farinciki ce gareki ki kwantar da hankalinki wata killa daga yau kinyi bankwana da bakincikin yaya sai dai farinciki akwai lokacin da zaki nemi wannan tsanar tasa ki rasa ina tabbatar miki wata rana sai kinyi alfahari da kasancewarki matarsa . su'ad ta tsurawa eiman idanunta cikin muryar kuka tace wai me nayiwa abdulkabir da zafi hk yake min wannan zazzafar kiyayyar? wayyohhhly Allah nashiga uku bani da sa'a aray....eiman tayi saurin rufe mata baki barki ce hk pls babu abinda kika masa zallar iskanci ne darashin tunani ke damunsa amman da sannu zai gane mahimmanciki gareshi da kyar eiman tasamu ta lallabata ta tashi sukayi sallah sannan sukayi wanka. misalin karfe tara da minti goma jama'a an hallara a kofar gidan ambasodor adam kofar gidan ya cika makil da tarin jama'a kama daga manyan attajirai zuwa kososhin gwanati kanan ma'aikata zuwa talakawa ta fanin ambasodor adam, data bangaren dagin mahaifin Zainab dagin mahaifin su'ad suma sun hallarar ta bangaren ummanta ne dai ba'a samu ko mutun daya ba. auran Zainab aka soma daurawa , sannan aka daura na su'ad wanda minister dr Mubarak ne yabada aurenta akan sadaki dubu dari biyar kmr yadda aminin dady km mahaifin musty wato alhj jafar ya bada a auren auren zeey . jin ihun kururuwar an daura auren yasa hankalin su'ad mugun tashi ta dinga jin kmr ana kwara mata ruwan sanyi ne ajiki barin ma dataji haniyar shigowar AK tare abokansa suna biye dashi abaya, sanye yake cikin wata hadaddiyar farar shadda gezner babbar riga me hannun link's da malulun a samun rigar wanda tasha aiki ajikinta sai hula me dauke da kalar aikin dake jikin shaddar sai agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa kafafunsa rufe cikin takalmai disigner suna zuba kyalli fuskar nan tasa sai sheki taki zubawa sbd gyaran fuskar da yayi , wani irin azababben kamshi turare ne me gauraye da sanyi dadi da bata