Sashe 277
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*AYSHA A BAGUDO* dedicated to hauwa A Usman jiddar YA KHABIR THE AWARE page 87 ........jini yagani ajikin farar rigar baccinta dif 'kwal'kwaluwarsa ta d'auke wuta ,kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa ,nan take d'akin ya fara yawo dashi tmkr zai fad'i ,zuciyarsa kuwa tamkr zata fito waje saboda tsabar tashin hankali daya tsinci kanshi,ita kuwa sai runtse idanunta take tana murkususun ciwo ganin halin datake ciki ne yasa komai yashiga dawo masa .. "meyasa nayi abinda nayi? "Meyasa why why gashi zan rasa bby'na akaron banza " "oh my goodness God have mercy on me "kar kasa narasa abinda ke cikin yarinyar nan, da kyar yasamu yakaraso jikin gadon datake zaune ya zame k'asa tare da dafe kansa wanda yake barazanar faduwa . sautin muryarta ce ya an karar dashi daga duniyar tashin hankali dayake ciki. "abdul cikina ka taimakeni zan mutu, mararta ce tayi wani irin murd'awa wanda hkn yasa ta saki razananniyar k'ara... ai bai san sanda yayi wata irin zabura ya mike tsaye bisa kafafunsa jikinsa na kirrma ya tattarota jikinsa ya rungumeta tsam yana kuka "am really sorry hrt wallahi bansa zaki shiga cikin wannan halin ba ,kiyafe ni matata babu abinda zai sameki samabatu kawai ya dinga xubawa sannan yayi hanyar waje daita ,ita kuwa da kyar take janyo numfashi tana fitarwa. sauri sauri gudu gudu da hk ya fito daga cikin part dinsa yana k'wallawa direbansa kira "adekule adekule where are you? securities dake tsaye suna shawagi akan duty din'su daya daga cikinsu yayi saurin juyawa ya isa d'akin kule ya tasoshi cikin magagin bacci yatashi cikin sauri security yagaya masa kiran boss. afirgice yasoma kokarin isa inda ak da zuwa lokacin har ya sanya su'ad cikin mota . yashiga cikin motar yana kokarin tayarwa kule ya iso "sir dan Allah ka fito na tukaka "kaci kutumar ubanka dana fito bacci na kawoka kayi ko aiki ..? "kajira dawowata yana gama fad'ar hk ya fige motar aguje, dan tuni securities sun dade da bude masa get. fitarsa ke da wuya ammi da dady suka fito sakamakon jin sautin muryarsa cikin dare kai tsaye gurin securities suka nufa suna tmbyrsu batare da bata lokaci ba suka gaya musu iya Abind idanunsu yagane musu ai take hankslinsu ya tashi . suka shiga neman number sa tana ringin baa d'auka. gudu ya dinga shararawa akan titi da taimako Allah ya iso hospitar dinsu, cikin sauri aka turo gadon marasa lfy aka daurata aka nufi dakin doctor daita aka . da gudu gudu aka shiga dakin likita daita domin a samu a ceto lafiyarta da bby'n cikinta likitoci suka rufa akanta domin bata taimakon gaugauwa da binciken abinda ya haddasa masa blinding da kyar likitoci suka samu nasarar tsaida jini sannan suka d'aura mata drip. shi kuwa yana tsaye bakin kofar d'akin kuka yake kamar karamin yaro yana dayasanin abinda ya aikata ganin fitowar likitici yasa d'an tsagajta kukansa ya nufi gurinsa da sauri doctor yace shi xuwa office dinsa ya biyosa cikin hanzari yana shigowa doctor yace "zauna . "kaine mijinta? da sauri ya d'aga kai "eh ya akayi doctor ta mutu ne? doctor yace "aa bata mutu ba tasamu jijiga ne eclamisia sakamakon jinita dayayi mummanar hawa ya'akayi kabari hkn ya faru? "alhamdullahi tunda bata mutu ba. doctor yace "yanzu dai mun shawo kan matsalar ta hanyar zuba mata magani cikin drip saboda bby'n cikinta ya gicce mata ciki idan Allah ya taimaka zai koma daidai "idan bai koma ba zuwa safiya sai dai ayi mata cs aciro abinda ke cikin ak ya sauke wata zazzafar ajiyar zuciya game da share gumi dayake ta faman tsatsafo masa a goshi kai kace wanda ya hadiyi kunama sannan yace "doctor ko zan iya ganinta yanzu? "why not kana iya ganinta ya mike ya fito yashiga . d'akin datake kwance ya kwance take tana bacci numfashinta na fita ahankali wasu hawaye suka zubo masa " i love you so much my beatiful wife i din mean to hurt you like this it's mistske. kusan minti talatin ya d'auka sannan ya koma gida domin tahowa da ammi wad'an ya iske suna zariya sun kasa tsaye sun kasa zaune su kad'ai suka san tashin hankali da suke ciki saboda sun kira numbersa yafi sau ba adadi hatta asibinsu sun kira ance bai je ba suna ganinsa suka nufosa suna rige rigen tmbyrsa " abdul ina su'ad? "me ya faru daita suka shiga jera masa tmbyoyi, take yashiga gaya musu bayani doctor, tare suka juya suka koma asibitin. washegari tana bude idanunta dashi idanunta suka soma cin karo yana zaune agabanta akan kujera ya dukar da kansa ajikin karfen gadon hanunta na cikin nasa yana murzawa ahankali ko ba'a gaya mata ba tasan kuka yake yi saboda sound din yadda take jin murysrsa yana furta kalmar "i love you hrt i don't want to loose you "ahankali ta kai hannuta ta shafa cikin jikinta ,yana nan tmkr yadda yake "alhamdullahi ta furta akasan zuciyarta dan tasan basu rasa bynsu ba sannan tasoma motsi wanda hkn yasa ak yayi saurin dagowa, kawataccen murmushinta ta sakar masa wanda yasashi yin driya shima da kuka a had'e yana kallonta "am sorry hrt ki yafemin ta d'aura hannunta abakinsa ala'mun yayi shiru .. gbdy takasa mgn dan ko tace zatayi magana muryarta bazata fito ba shi kuwa wani irin farinciki ya tsinci kanshi ciki ya dinga jin kmr ana sake wura masa wutar kaunarta ne azuciyarsa, ya zaunar daita tana fuskantarshi ya dora hannunsa akan fuskarta yana shafawa tare da tsurawa kyakkyawan fuskarta idanu yana kallonta ,cikin dare daya ta zabge ta rame karamin tiren silve na wanke baki ya d'auko ya taimaka ya wanke mata baki yaje ajiye sannan ya dawo ya had'a mata ruwan tea me kauri ya dinga bata . da dadre musty yaxo tare da eiman domin duba jikinta cikin ikon Allah tasamu lfy domin ta daina zubda jinin datake ak yayi matukar murna har da hawayen dadi ,kullun anan ak yake kwana tare daita dan koyaje gida bazai iya runtsawa ba, ummanta da prof taufeek har ma da daman shema sunzo dubiya. kwanansu biyu asibiti aka basu sallama gurin doctor ya kara da bayani akan ak ya dan daga mata kafa kad'an gurin auretayya saboda lafiyar bby idan ba hk zai iya rasa abinda ke cikinta maganganun likita tsab suka dinga shiga kunne ammi duk da ba da ita yake ba. koda suka dawo gida part din ammi aka wuce daita bisa ga umarnin dady da ammi, tundaga lokacin da su'ad ta fito daga asibiti take baya baya dashi batason ke'bewarsu guri daya amman kuma ta wani fanni tana tausaya masa saboda yanayinsa tana jin tsoro kar ya jefa kansa cikin wani hali . a wani yammaci tana kwance akan 3seater cikin parlour'n ammi sanye cikin doguwar rigar baka, tuni ta rigada tayi nisa cikin kogon tunani halin da mijinta zai tsinci kansa na nisanta junansu dasuka samu, yashigo falon yayi tsaye ya tsura mata idanuwa yana kallonta sannan ya zauna daidai saitin fuskarta yana kiran "hrt beat " ahankali ta d'ago fararen idanunta suka dubi juna su'ad ta saki wata yar ajiyar zuciya ,ta dawo daga duniyar tunanin data dade da lulawa ya dafa kafafarta "meyasa kika cika yawon tunani bayan kinsa yanayin da kike ciki ,ba a son me juna biyu tana yawon zurfafa tunani ples ki daina bana bukatar hk. ta kalleshi tana murmushi "taso mu koma part dinmu wallahi bana jin dadin zamana ni kad'ai batare da kina kusa dani ba, yakai hannunsa ya d'agota ta fad'a kirjinsa tana murmushi jin takun tawowa yasa tayi saurin barin jikinsa tsayuwar minti biyu suna jiran suka ko waye, gani babu wanda yayi kokarin shigowa yasoma tafiya daita yana rungume daita ajikinsa yana rad'a mata zantuttukansa masu sanyi kicibis sukayi da ammi dake kokarin shigowa parlour'n suka ja baya cike da matsanancin kunya su'ad ta boye abayansa. ammi ta wurgawa ak wata harara hade da cewa "ina zuwa kuma? ak yasanya hannusa yana tsotsa keyarsa alamun rashin gsky atare dashi "ammi gyara min shimfid'a zatayi "ammi ta sake watsa masa wata hararar "banason rainin hankalinka daka saba yiwa mutane gyara shimfid'ar ne bazaka iya da kanka ba. "wai me yasa abdul baka da tausayi ne hk ? yayi murmushin yake dan ya lura kmr ammi bata fuskanci inda maganarsa ya dosa ba ,dan hk ya kamo hannun su'ad cikin nasa "zo muje kinji hrt dina kyale ammi batason ki dinga aiki byn wannan aikin zai sa ki dinga jinki garass . ammi tace "maza ki zauna muddin bazakaje Kayi gyaran da kanka ba ko kasa wani daga cikin ma'aikatan gidan nan su maka sai dai ka hakura" ina dalilin wannan jaraba hk mace da ciki baxa'a barta ta huta ba.. "sai kajawo mana yawon zuwa asibiti ,wallahi ni dai babu ruwana idan kayi sanadin rasa abinda ke cikinta, wata irin kunya ce takama su'ad kmr kasa ta tsage tashige ciki ak yayi murmushi yace "shikenan ammi tunda kin hanata amman fa ba abinda kike tunani bane.. ya fice daga parlour'n ammi da su'ad suka koma cikin parlour suka zauna nan ammi take nunawa su'ad had'arin abinda suke kokarin aikatawa.. duk tsawon wunin ranar ak sai wani shashshare su'ad yakeyi yana wani d'aure mata fuska wai shi a dole fushi yake daita domin aganinsa itama din batason kasancewa dashi shi yasa take baya baya dahi. tashigo parlour'n yana zaune rike da remut a hannunsa yana sauya tashoshi dake cikin receiver ya d'an saci kallonta yana ganin zasu had'a ido yayi saurin yanye idanunsa hkn ya bala'in bata dry. sautin dariyarta ya tsinkayo acikin kwalkwaluwarsa yasanyashi yayi saurin dubanta ba shiri ya sauke numfashi yana kallonta "dry me kike min? cikin yanayi na d'aure fuska yake mata mgn hkn yakara bata dry, amman sai tayi saurin sanya hannunta ta toshe bakinta ya taso daga gurin dayake ya nufota tare da riko hannunta ya matse da karfi yace "me kika gani ajikina kike dry? su'ad taji radadin matse mata yatsu dayayi ta saki wata siririyar k'ara mara sauti tace"wash Allah kayi hakuri bazan kuma ba "sai kin fada min sannan zan kyaleki . "wayyo Allah ammi zai karya mini hannu ki kawo agaji.. ya sakar mata hannu yana hararata ta fad'a