← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 289

Sashe 122

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nace a'a nagode nayi da safe idan naje inda zani. kallona yake aransa yace zai dana . nagane hkn ne sbd yanayinsa danagani yana kallona yana lasar lips yace nayi kwanciyata. har yafita ya dawo ya tmbyi sunana nace salema ....yace suna me dadi yadace da me sunan nayi dan murmushin wanda bai kai zuci. byn ya fita na bude akwatin kayana inda jakata take na dauko diary din prof taufeek yabani nasoma dubawa ahankali full address dinsa da numbobin waya har guda uku na bude wani shafin abinda nagani ne yasa gabana faduwa da sauri na gyara zama ina sake dubawa ga abinda nagani arubuce.. _yau 3 ga watan mach shekara ta dubu biyu da dari hudu dana sadu dake saduwa ta karshe daman tunda na fara saduwa dake ban taba yin realize ajikinki ba, amman yau dana sadu dake na zuba miki spam dina ajikinki km sai dana daidaici lokacin period dinki yayi sauran 14 days km adaidai wannan lokacin na tabbatar inda ba Allah ne ya kiyaye ba zaki iya samun ciki sbd kwayenyen haihuwarki sun fara farfashewa a wannan lokacin daidai mace zata iya daukar ciki so inafatan na dasa miki kwaina acikin mahaifarki sbd ina son ki haifa min "da" ko "ya"wanda zaki dinga kalla kina jin dadi a cikin ranki sannan yasa kiji nishadi acikin rayuwarki wanda kullun idan kika kalleshi zaki tuno dani killa sanadiyar hk ki biyoni kasata......_ ina kaiwa karshe rubutun hawayena suka sake balle min ahankali na furta gani cikin Nigeria taufeek burina layunkanka suyi saurin sadani da kai. na runtse idanuna ina kuka.... ina tunanin yan gidanmu.. dayake na tsargu da mutumin yayi masauki sai na kasa baci nayi shr na runtse idanuna kmr me bacci. cikin dare kawai naji ansoma lalubata na farka afirgice ina zare idanu mutumin nagani tsirara haihuwar uwarsa yana kokarin kai hannusa jikina na fashe da wani irin razananniyar kuka ina rokonsa tare da ce masa ni ba yar isaka bace sai yace ai yasani kawai taimaka masa zanyi yace tunda ya daura idanuna akanka naji bazan iya hakura ba ina jin hk na miki tsaye jikina na rawa nace wallahi wannan jikin yafi karfinka... yasoma motsani ina ja da baya matso yayi sosai yana lumshe ido kmr wani tsohon maye . ina kokarin tutturesa yayinda firgici da tsoro yasani sakar wani rikitatccen kuka nan fa muka fara kokuwa dashi daga karshe Allah yabani nasara akansa na ingizasa baya da iyakacin larfina wanda hkn yayi sanadiyar bayana ya amsa da karfi. yayi baya kafafunsa sukayi sama tmkr me shirin yin dungure garin ya dawo da kafafunsa ya buge min ciki take naji marata ta daure ban tsaya wata wata ba na dauki jakata na rataya wanda diary din taufeek ke ciki na bar gidan aguje shima yabiyo byna yana ihun kiran sunana gudun bala'i nake a saman titi batare dana san inda zani ba ina kuka ina kiran sunan mahaifiyata gbdy tsoron abinda mutumin yayi yunkurin yi dani yasa tsoron daren ya kaurace acikin idanuna . burina alokacin nasamu inda zan fake ko mataimaki daidai wata youtown na hango wata kwana wace haske wuta ya haskaka gurin nayi saurin bin hanyar tare da shigewa inda naga hasken ina adduar neman tsari har bakin gurin mutumin yaxo yana kiran sunana salema ki tsaya na fasa abinda nayi niyyar miki ina kallon ya tsaya yana waige waige ta inda zai ganni bai gani ba ya juya ni km na dinga jan ajiyar zuciya ina saukewa sannan na durkushe kasa ina wani irin kuka sai alokacin nasan inda nashigo ashe church ne sakamakon ganin ganguna da kujeru jere da cross. ranar ban iya na runtsa ba tunda sanyi safiya na fito atsorace kar masu gurin suzo na samu guri bakin titi na zauna har garin allah yawaye ina zaune na saka wancan na kwance wancan ina tunani ta ina zansoma neman taufeek har kusan shabiyu ina gurin zaune tun bana jin yunwa da kishirwa har nazo nasoma ji daga inda nake zaune na hango tsayuwar wani mutun da baro gabansa wanda ke cike da kayan marmari ahankali na mike jikina babu kwari na isa gurinsa na gaishe shi cikin harshen tsadadden frach ya nuna min baya ji nayi masa turanci na ma dai the same sai kawai nayi masa mgn da gauranci hausata dabata gama bin bakina ba. ka taimaki ne dan Allah kabani lemo ko guda daya ne yunwa nake ji ni bakuwace agarin nan.. mutumin ya tsura min ido yana kallona yadda yake kallona din ne na tabbatar da tausayina ne ke shigar jikinsa. amadadin yabani lemun dana tmby sai naga ya nufi gurin wata me tsaida abinci ya siyo har da ruwa wanda banyi tunanin ko ni zai bawa ba amman ga mamakina yana karasowa ya mike min plet din abinci ungo kici jikina na rawa na amsa ina masa godiya nasoma ci hannu baka hannu kwarya dan bazan iya cewa ga tun lokacin dana ci abinci irin hk byn nagama ci na sha ruwa yabani lemu guda uku cikin bakar leda sosai nayi masa godiya na tmbayesa masa inda zan samu massallaci ya nuna min sannan nakoma inda nake zaune tun farko . shi km yacigaba da kasuwancinsa ina zaune gurin har yamma babu wani cigaba domin banda yadda za'a yi nasamu waya . " shi km wanna mutumi yagama kasuwancinsa yayi min sallama ya wuce. a massallaci danayi salolina na kwana ina kuka lagos ba kmr sauran garuruwa bane. Gari ne wanda basa amsar bako ko tausayawa bako washegari na sake zuwa gurin mutumin jiya nan na wuni byn na tmbyeshi aron waya yabani na kira numbobin da taufeek ya rubuta min . kiran duniya nayiwa layikun taufeek amman ba'a dagaba. nashiga matsananci damuwa gabadaya na sake birkicewa nafita haiyacina bani kaina ba hatta cikin dake jikina yana cikin damuwa sbd yadda nake jin marata na daure min atakaice miki su'ad sai dana kwana uku ina neman layinsa daren kwana uku ne ya waiwaiyi kiran danayi masa. ya kira mutumin danayi amfani da wayarsa ya dauka ya gaisheshi yake fada masa wata yarinya ce keson waya dashi. misalin karfe 11 mutumin ya zo har indanake zaune kafin mutane sugama watsewa nashiga cikin masallaci na kwana ya mika min waya yace number danake takira ce takira . jikina har rawa yake gurin amsar wayar nasoma Bin layinsa kira daya ya dauka ina jin saurin muryarsa bansan sanda hawaye yasom gangaro min ba na kasa mgn shima tunda yace hello.. hello yayi shr bai sake cewa komai ba yana jira daga gareni . "sai dana numfasa na sauka naunauyen ajiyar zuciya da karfi nace he... llo... kawai naji yace my loulooooooo... ya furta da karfi daga jin yanayin yadda yayi mgnr kasan atsorace yayita na amsa cikin kuka na'am taufeek ...ina ka'ajiye wayoyinka tun shekarajiya nake neman layinka da garari cikin gari ? wayyohlly Allah nah.... kiyu hkr my louloooo.. yanzu kina ina ai tunda mutumin ya tabbatar min da macece takira wannan number jikina ya tabbatar wani abu .yace yanzu a ina kike? muryarta cikin kuka nace bansa inda nake ba amman bari nabawa mutumin daya taimaka min . nakarasa gurin mutumin na mika masa wayar nace dan Allah ka gaya masa sunan gurin nan. karba yayi tare da sanar masa inda muke kai tsaye ya katse kiran batare da ya sake dawowa min da wayar ba. muka tsaya zaman jiran isowarsa. tun karfe 11 dana kira taufeek banga yazo ba. hankalina ya tashi sosai yayinda mutumin yaki barina ya wuce sai ma sake neman layin taufeek din yayi ina jinsu suna waya yace ya hanzarta zuwa sbd area babu lafiya za'a yi (etutu) taufeek najin hk yace dan Allah ka taimakeni ka tsaysa min daita ina kan hanyar zuwa ne hoodup ne ya rike. ni Allah ya yarda zan karaso kafin llokacin da zasu fara kasan woman develoment center? mutumin yace eh ok idan ma zaka wuce ne ka taimaka ka kaimin ita can tajirani yace to . e'tutu wani tsafi ne da mutane lagos suka meidashi tmkr ibada ko al'ada kusan sunayinsa ne domin zaman lafiyar garinsu acewarsu tsafin yafi son ya'ya mata domin idan suka hadu da mace zasu mata tsirara haihuwar uwarta sannan su yankata yankan rago su tsiyaye jininta ,acikin kwaryar tsafinsu . idan km namiji ne zasu masa dukan mutuwa da bulalar tsafi wani ya rayu wani km sai yayi doguwar jinya sannan ya dawo yasamu lfy . suna fara wannan tsafin nasu ne da kmr misalin karfe daya saura . ina jin mgnr da mutumin ke fada hankalina ya sake tashi jikina ya dauki rawa muka soma tafiya. tafiya muke a kafa yana sake bani labarin yadda ake (e'tutun ho'ro) har muka kawo menegement yana cigaba da bani lbari wanda sai alokacin na tmbyi sunansa yace min hasan muna tsaye gaban get din woman development center muka tsaya daga gefe titi muna tsaye wani gang na yoroba people's suka zo suna hayaninya da iwace iwace daga karshe suka ja birki sai muka zage zage da tsine can km fada ya kaure tsakaninsu suka shiga bata kashi . ban da fashe fashen kwallabe babu abinda suke sauran tsirarrun mutane dake bakin titin suka soma darewa lokacin da aka lumawa wani kwalba a gefen cikinsa ga hanjin mutun muraran kana gani ga jini na tsiyaya kmr ruwa ai nima bansan sanda na kwallara kara na kwasa da gudu nayi hanya me zuwa badagir shi km hasan bansa hanyar daya bi ba . gudun nayi sosai kmr zan bar garin daga karshe na tsaya ina sauke numfashin ganin nayi nisa da gurin banda numfashi da haki hmmmmmmm hmmmm babu abinda nake nasamu wani jikin wani table na jingina kaina sbd kasa tsayuwar nayi yayinda naji marata tayi wani irin daurewa tare da murdawa ina nan tsaye agurin har daya tayi bansani ba matsafa har sun fito sun soma abubuwan tsafinsu a wasu wuraren motsi nasoma jiyowa na sautin muryoyi mutane daban daban suna fadar wasu abubuwa cikin harshen yarobanci wanda ni alokacin bansa me suke cewa ba sai daga baya nasan maa'anar su. amman jin muryoyinsu kadai ya isa tsoratarwa tare da firgitar da zuciya, nayi saurin mikewa daga jinginar danayi nashige karkashin wani table na buya yayinda mutane
Chapter 122 · 0% Book details