← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 289

Sashe 68

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi baya sonta baya kaunarta km bazai taba kaunarta ba...... washegari wani irin matsanancin zazzabi ne ya rufeta sakamakon raunukan jikinta. gbdy ilahirin jikinta yayi mata tsami da kyar take iya bude kumburarrun idanunta dake like . ga jikinta dake kirma, umman su'ad wace ta dade da tashi har tasoma aikace aikacenta na yau da kullun tashigo dakin ta duba ko su'ad din tashi ta cire kayan jikinta domin ta wanke. turus tayi sakamakon yadda taga idanunta da goshinta yayi . kasa hakuri tayi takarasa zuwa kan gadon datake zaune hawaye na fita cikin idanunta ta rungume su'ad da sauri hawayen idanunwanta na saukowa cikin rawar muryar tace su'ad wace irin rayuwa kika zabawa kanki.? wannan rayuwar sam bata dace dake ba kiyiwa girman Allah ki tausayawa rayuwar ummanki ki dawo ta kwarai . duk duniya bani da kowa bani da komai sai ke kadai da Allah yabani....yanzu waye wanda bai da imani da tausayi yayi miki hk.? wani irin sanyi jikin su'ad yayi idanunta suka sake cikowa da ruwan hawaye ita kanta batason takasance cikin wannan rayuwar me cike da sarkakiyar da kaskanci. hakika wannan yanayin yakasance lokacin bakincikinta ne da rashin kwanciyar hankali gareta. waye wanda keson kashe min ke..? kiGaya min dan gidan ubawaye yayi miki wannan dukan? ahankali su'ad tasanya duka hannuta ta rungume mahaifiyarta dake rungume daita tana kuka. umma ta zare jikinta tana goge mata hawaye .kigaya min wanda yayi miki illa hk da ala'mun ma kasheki yake son yi... hannuta takai kan fuskar mahaifiyarta tana goge mata hawaye muryar a raunane cike da sanyi , ummana ko na gaya miki wanda yayi wannan duka babu abinda zaki iya yi akai.... afusace tace Ki gayamin yau me rabani da uwarsa sai Allah sai yagaya min dalilin dayasa zai aikata miki hk .. , dan gidan tsohon ambasodor kasar nan ne yayi min hk.... nagaya miki nasan babu abinda zaki iya akai.. domin kasancewrmu kaskantattu marasa gata da galihu. ummana ki sanar dani inda daginki ko na mahaifina suke idan km banida su na hakura. na sanyawa zuciyata salama da dangana narashin dangi.. hakika ina son insan inda yan'uwan mahaifina suke koda kuwa zasu dinga dibar namar jikina ne . ina kwadayin sakasu cikin idanuwana. nayi rayuwa tare dasu .tunda su'ad tasoma mgnr kirjin umma ke bugawa babu abinda tafi tsana arayuwarta sama taji wannan kalmar abakin tilon diyarta. domin bata shirya bata amsoshin tmbyoyinta ba. dan hk ta hade rai tmkr baitace yanzu take kuka da nuna kulawa me tattare da tausayawa ba .muryarta a kausashe tace idan kika sake tayar min da wannan zance ban yafe miki ba.. kina da gata tunda kina dani ... nice uwarki nice ubanki dama danginki gbdy . na dade da meye miki gurbinsu .. komawa su'ad tayi ta jingina bayanta da bangon dakin tana jin yadda numfashinta ke fita da zafi kasancewar zazzabi jikinta. ta runtse idanunta tana kissima abubuwa masu yawa cikin ranta.. wace irin rayuwa ce hk ? meyasa umma batason nayi mata zance mahaifina ko danginsa danata ? why why why ummana ki taimakawa rayuwar su'ad dinki ko zata ragejin radadin da nauyin da kirjinta ke mata a duk sanda hkn yataso..? ki sanar min idan ni din mara usuli ce nasani na dauki kaddarar ,irin wace ya'ya marasa galihu suka dauka.. da wannan tunanin ta wuni a daki ranar babu inda ta leka tana kwance tana jinyar kanta dan sai datakai umma ta kira mata nurse gida. tayi mata allura da karin ruwa duk wannan azabar datake ji ajikinta hkn bai sa ta manta ak acikin zuciyarta ba. tuninsa yaki barinta yana nan makale akirjinta. yayinda kawayenta maza da mata suka shiga kai kawo acikin gidan dubata sbd ore tasanar musu da batun rashin lfyrta ..aiko umma taga jama'a har dana wasu unguwanni. ita dai ido ne nata.. lokacin dasu babalaye suka zo sun iske an cire mata drip na uku ana shirin saka mata na 4 zama sukayi suna mata sannu da jiki. yayinda nurse ke kokarin tsira allura cikin robar ruwa. ta motsa labbanta ahankali ina son nayi fitsari.ok kawai nurse din tace. ore dake zaune abakin gado taja hannuta ta mikar daita tsaye sukayi toile tayi fitsari suka sake dawowa dakin. ta kwanta kan katifa tana jin jikinta kmr an daura mata dutse ne sbd tsamin da yayi mata. nurse ta meida allurar cikin drip. da zata wuce take nunawa ore yadda zasu cire allurar daga jikinta da zarar ruwan yakare. byn fitar nurse hira ta barke tsakainsu amman ban da su'ad dake kwance idanunta a runtse tunanin ak take. babalaye ne yayi gyaran murya tare da tmbyr su'ad garin yaya hk ta faru daita . wai waye banzar dayayi miki wannan illa hk? sai lokacin ta Dan bude kumburarrun idanunta kadan . murmushi tayi wanda bai bayyana sosai a saman fuskarta ba, sannan cikin sanyayiyar muryarta tace wannan dukan na cakwakiyar ce wace zazzafar soyayya ta haifar daita.. take ya gano bakin zaren .ya gyara zamansa sosai . byn mun rabu jiya ne yayi miki wannan dukan ko ya ? motsi tayi da bakinta kawai alamun eh . akwai shegen dan iskan mutun ,me idanun mage . stop.. babalaye ta katse shi a dan zafafe . dont acusing my Hrt I love him so much to the extend i can explain. baki kawai ya tabe tare da cigaba da mgn amman dai bai gane shirinmu ba ko? da kyar ta sake bude bakinta gsky bazance ya gane ba. " dan bai nuna min hkn ba. Allah yasa kiyi nasara akanshi dan kina shan wahala . ameen tace acikin kasan ranta. me zai hana kibamu dama da tuni wuya tasakashi amincewa da soyayyarki .. dariya take sonyi amman babu hali . baku san waye abdulkabir ba that's why ni nasan halin kayana ku barni dashi kawai tayi mgnr cikin ranta. zaune AK yake shida musty acikin a part dinsa mgn yasoma yi masa cike da natsuwa. akan lamarin mahaukaciyar yarinyar.musty wace ce wannan yarinyar .....?sbd al'amarinta yana kokarin tauye zuciyata da lamurana... ina son sani wacece ita.......... ? gsky ni kaina bansan kowacece ba.. jiya shine karo na 2 dana taba sanyata acikin idanuna sai dai ga dukkanin alamun tana mutuwar kaunarka.... zata iya komai akanka ciki har da sadaukar da raywarka me zai hana kasota ka aureta ka hadata da zeey.. shhiiii dakata mlm dan allah ba wannan banzanr shawarar nake bukata daga gareki ba..... who is she kawai na tmbyeka ba surutan iska ba. da zaka zauna kana karanto min robbishi me zanyi daita kana tunanin ko matan Duniya sun kare zan aureta ne... ? zaka iya shahada ka aureta ..domin banga illar aurenta ba. banza stupid kawai ai bazaka tabani ganin illar aurenta ba tunda kaima Dan'wana shashanci ne dan shaye shaye ban ma san dalilin abinda yasa na sakoka cikin lamarina ba ,amman me zai hana kai ka aureta tunda bata da illa..? sbd batace ni take so ba ...kai tace tana so yayi mgnr yana nuna kirkinsa da yatsan hannunsa amman wallahi azim ina tabbatar maka da ni tace tana so. zan aureta abdulkabir domin tausayawa rayuwarta. tabani tausayin sosai fiyye da tunaninka ..tsaki ak yaja da karfi yana mikewa tsaye tare da zube hannuwansa cikin aljihun wandonsa sai kayi tajin tausayin nata marasanin ciwon kansa kawai ,yayi shigewarsa bed room yabar musty zaune yana kallon bayansa cike da matsancin takaici. cikin wannan shige da ficen da kawayen su'ad keyi gidan . har tayi sati daya agidan batare da ta leka koina ba . hkn yasa takarayin kyau ta warke simul tayi fresh bakace itace tasha dukan mutuwa ba. ammi da Zainab har ma da iman ke kokarin shiga cikin harami kowanensu sanye cikin doguwar riga da hijab har kasa da safa. ahankali suka karasa gurin dawafi byn sun kamala da dawafi kowanensu addua yake cikin ransa . ammi na tsananta addurta akan tilon danta dan har dawafi tayi masa na musamman akan lamuransa . itama iman addua take akan lahirarta da samun miji na gari da samun nasara akan fine exam dinta dazata zana bana. yayinda uwar gayya zeey tarasa me zata roka agurin Allah. gbdy kunya rokon ubangijinta take sakamakon munanan halaiyenta gata dai gaban qaba amman tarasa me zata roka domin ko ta nemi tuba a halin yanzu ba tuban zatayi ba sanin datayi akwai aiki agabanta, sanan idan ma rokon ubangijinta zatayi akan soyayyarta da ak. gani take baza'a amsa mata ba. gbdy abin duniya ya taru yayi mata yawa,. dan hk tasanyawa ranta zata sake dawowa tayi aikin haji domin sauke farali da neman tuba . tunda daga ranar bata sake taka kafarta zuwa haram ba kullun sai dai ammi da iman suke zuwa ita km tana kwance. tafi maida hankali a bacci akan abinda yakawota . satinsu biyu sukayi dubai. zaune yake shida karuwarsa onye a Z&Z CHICKEN SPECIAL dake cikin ijeka in side su'ad dake maseefar sonshi amman shi kwata kwata bata gabansa sbd ji yake duk duniya babu macen daya tsana sama daita .itace tsaye agabansu tana kare musu kallo cike da wani mahaukacin azababben kishi ... nan zuciyarta tasoma dugunzuma nan zuciya ya debeta .. kirjijta na buguwa ta kai hannunta ta damki wuyanta ta matse hade da rigar jikinta.... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 68 · 0% Book details