Sashe 258
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
one day for the owner, so yau dubunki ya cika daga nan ma kiyi hospital kije kisan matsayinki agurin doctor saboda ni tuni nasan matsayina ina dauke da cutar HIV ...yayi shiru yacigaba da saka kayansa zuciyarsa na harbawa saboda idanun Ak daya ji suna yawo a gaba d'aya ilahirin jikinsa. Shi kuwa Ak shiru yayi yana tunani zufa ne ke keto masa duk sanyi AC dake aiki dakin gabadaya ilahirin jikinsa rawa suke so yake ya sake yin magana amman kuma yakasa sarrafa harshensa sai da ya dinga jinsa tamkar anyaye masa tarin damuwar dake damunsa da rufewar zuciya akayi masa akanta uwa uba matsananci tsoronta dake dawainiya dashi duk yane mesu yarasa amman fa har lokacin jikinsa kirrrma yake yayi mugu mugun gigita da ganin abinda yagani da kyar yasamu ya sanyawa jikinsa jarumta bakinsa na rawa yace. "irin cutar da kike mana kenan? " da aurena dakanki kike bin maza iri iri har da Akil da kika tabbatar min da babu komai tsakaninku har kikace min shine ke bibiyarki...... "ya ma akayi na aureki har kika kasance mata agareni bansani ba? "bansa lokacin dana sake meidake gidana ba amatsayin matata ba... cikin rawar muryar tace "no no kayi hakuri wallahi ba haka bane duk maganganun akil karya yayi min wannan kuma da kagani wallahi sharrin sheidan ne yau ne kawai y ...kafin takarasa fadar abinda take son fad'a har AK ya isa gareta tamkar guguwa dan itama sai ganinsa tayi agabanta yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya cafki wuyanta daidai makoshinta ya matseta da bango d'akin daidai lokacin da Akil yasa kai yasoma k'ok'ari barin d'akin, kafin yagama da Zeey yayo kansa, dan a irin matsar dayaga ak yayiwa wuyanta bana wasa bane dan har tasoma fita haiyacinta . yana kaiwa bakin kofar nan ya iske wani sabon tashin hankali sakamakon iske dandazon mopol dayayi fiyye da goma kowanensu rike da bindigunsu sun saita kansa ,musty dake tsaye "yace gashi nan ku wuce dashi har sanda muka nemeku . daya daga cikin police din yace "you are under arrest, wani ya matso kusa dashi da sauri ya dama masa handcop a duka hannunwansa suka tasa keyarsa . kakarin mutuwa Zeey take tana nishi a rikon daya da ak yayi mata batare da ya sake cewa komai ba idanunsa sun kada sunyi jazur wani tiriri zafin ne ke fita daga jikinsa. yayinda numfashi ke k'ok'ari barin gangar jikin Zeey ya buga kanta da bango d'aki tayi luuuuuuuu akasa sai ga jini yashiga tsiyaya ta hancinta da gefen kanta bata sake motsi ba, shi kuma bai bar dukanta ba sai daya farkar daita da duka , yaki barinta kafin kace me tuni kamaninta sun sauya hawaye take matso daga kumburarrun idanunta muryarta a dashe tace "plz my l... "kika sake kika furta min wannan kalmar sai nayi gunduwa gunduwa da na manki la'ananniya "kin cucemu kinci amanar mutane da suka amince miki suka baki yardarsu dari bisa,sai Allah ya had'aki da masefu iri iri arayuwarki," ina miki fatan mugayen al, kaba'i a sauran shafuffukan rayuwarki " banta ganin mace me nirin halinki ba kinci amanar iyayenmu barin irin irinku a duniya tamkar barin fasadi ne a doron 'kasa gara na aunaki lahira yayi kwallo daita tayi sama ta dawo ta zube 'kasa tare sakin wata razananniyar kara cak numfashinta ya dauke ya fashe da wani gigitaccen kuka tare da matse mata wuya "kin amanar mutanen da suka yarda dake ashe karya ce muguwar dabba acikin dababbi kuka yake sosai yana buga kanta da tayis ta sake numfashawa "wayyo Allah dan Allah karka kasheni sonka ne sanadi wallahi zazzafar soyayyarka ce ta haifar min da muguwar sha'awar datasa na kasa rike kaina ya mike tsaye yana huci tare da kai kafarsa daya ya buge mata baki take bakin ya kunbure wanda ya haddasawa rashin maganarta fitowa sosai kuka yacigaba dayi yana yarfe hannu "meyasa Zainab ...? "why why why Zainab kika zabawar kanki irin wannan kaskanci ? yakarasa fadar hk yana naushin bango da buga 'kansa bango kin taurari mutumin daya amince miki nabaki dukkanin yardata banta tinanin hk daga gareki ba ko lokacin dana kusanceki najiki a bude ba kamar yadda na samu su'ad ba zargi nayi sai gashi yau naganki da idanuna kina kan akil kina cinsa har da neman kari.. tasoma girgiza kai tana jan gindi zuwa inda yake a matukar harzuke yace "stop there don't don't ever close to me kin cucrni kin cuci kanki Allah yasa dan bansa sanda na sake meidoki gidana ba.. musty na son shigowa amman bai san awani yanayi zai iske Zeey ba, dan haka yaciga da tsayuwa agurin har zuwa lokacin da ma'aikatan hotel din suka iso ya hanasu shiga. " Sir," kabar mushiga kar'ayi mana kisan Kai acikin hotel kufito daita ku tafi daita duk inda zaku daita idan ma zaku kasheta ne ku kasheta amman ba anan ba.. can daki kuwa bugun mutuwa AK yacigaba da mata sannan ya barta yana furta mata "Zainab natsaneki me kyan d'an maciji karya me fuska biyu na datse sauran igiyar aurena dake kanki nasake ki saki biyu. daidai ma'aikatan hotel din suka karaso cikin d'akin dukkaninsu babu wanda baiyi shock va akan irin dukan da AK dayayi mata domin ko motsi kirki batayi ,daya daga cikin maikaciyar hotel din ce tayi saurin karasawa ga zeey tasoma kokarin taimaka mata ganinta tsirara ta zira mata doguwar rigarta sannan suka tattarota kamar kayan wanki zuwa bayan motar musty wanda ak yace Allah ya kasheshi bazai shiga motar ba matukar tana ciki . maganganun ma'aikatan hotel din dana Ak ne ke shiga kunneta daya byn daya dan zuwa lokacin tasoma farfadowa tana gama farkawa tukunyar tsafintace tasoma fadowa zuciyarta tukunyar tsafinta shine kawai last opportunity dinta akansa ,dan ahankali sanyawa jikinta kuzari ta bude idanunta tun kafin a rufe motar ta fito tana nishi da kyar tana dingisa kafa musty yaso cafkota AK yace" yabarta kawai musty ta tafi duk inda zata, ai kuwa musty ya kyaleta dan abun nata ya zarce tinaninsa dan tsamaninsa mutuwa tayi suna tsaye cikin hotel din suna sake tautaunawaa game da abinda zeey tayi har manager hotel yace dashi kashe ita da kwarton zaiyi . ita kuwa zeey cikin sauri sauri ta dauki machin ta isa gida jikinta na rawa ta isa d'akinta ta dauko tukunyar tsafinta tashiga zabga kirarin sunan Ak da iyayensa ruwan na fitowa daga cikin kunburaran idanunta. bangaren su Ak suma hanyar gida suka nufo har suka iso tunkunyar tsafinta na hannuta jin motsin shigowarsu yasa tasoma k'ok'ari maida tukunyar inda take, aikuwa cikin rashin sa'a kamar an jona mata wutar lantarki jikinta ya kama rawa kar kar kar sai ga tukunyar tsafi a k'asa ta fad'i ta tarwatse take hayaki ya turnuke d'akin tamkar anyi gobara da sauri suka karaso atare suka shiga d'akin ko kafin su shigo tuni tasa'ka wata razananniyar k'ara can kuma tasoma fizgar gashin attaciment din kanta ta yaga doguwar rigar jikinta har 'kasa tana zuba sambatu "hhhhhhhhhhhhhhhhh nice nice ta dinga fadar abinda tayi da abubuwan daya faru ai wani irin mutuwar tsaye Ak da Musty sukayi agurin nan take Ak yashiga ganin juwa daga baya Musty ya dafashi yace "lafiya Abdul menene ke damunka? Can kamar minti goma Ak ya wastake yana dubanta zeey dake hauka tuburan tana sambatu duk sambatunta nashiga kunnenshi daya bayan daya kai tsaye igiya yasamo zai d'aureta musty yashiga girgiza masa kai ala'mun kar yayi amman ina yaki yarda muryarsa na rawa rawa "Musty bansa yaya akayi na sake dawowa da Zeey gidana ba , asanina bana sonta tun asali ashe tabi wata hanyar daban gurin mallakata nayi danasani kasancewarta yar'uwa gareni ... yana magana yana kuka yana k'ok'ari daureta da igiya har ya daureta tamau yasa plesta ya manne bakinta sannan yashiga dauketa da wasu gigitattun maruka ," meyasa kika za'bi bin wannan hanyar gurin mallakata har na aureki ? Ya tambayeta yana sake marinta , duk da daureta cikin yanayin hauka amman taji zafin marin dan sai fezge fezge take tana zare ido waje ... ya juyo ya fuskanci musty yana kuka musty "musty na aureta batare dasani ba wallahi bansa lokacin dana aureta ba...... rungumeshi Musty yayi ajikinsa yana jin wani irin dad'i ya mamaye zuciyarsa aransa yace daman wannan lokacin zai yi kusa haka? hawayen farin cikin Musty yake zubdawa yana kiran Alhamdullahi Alhamdullahi Allah mun gode maka.. kusan minti goma suna rungume da juna Zeey na daure tana mazurai da ido sannan suka saki junansu Ak yayo hanyar parlour Musty yabiyosa ya dafa kafadarsa yana rarrashinsa da bashi hak'uri yana sake gaya masa abubuwan daya faru dashi da abinda ya d'inga yiwa su'ad da halin data tsinci kanta a watanin baya da irin wulakancin daya d'inga yiwa matar shi da shigar cikin jikinta, nan take kansa yashiga sarawa ahankali ya dinga zagaye parlour'n yana sake zurfafa tinaninsa bazai iya tuna wasu abubuwan ba,abu biyu ne ya tsaya masa arai har yake ganin kamar a yanzu suke faruwa ,sakin suad da tace yayi da kusantarta dabaiyi ba, yasan tabbas bai saki matarsa ba sannan bai kusanci zeey ba sai dole yaje agwada shi da su'ad domin inganta lafiyarsu dan bai sani ba ko akaron su na farko ya dauki cuta... . daki daki maganar musty ke shiga kunnensa akan wulakanci zeey gareshi da sanyi idanunsa " Yanzu irin abinda ya faru dani kenan? yayiwa kansa tambayar " sannan yasoma neman layin su'ad kansa na cigaba da sarawa ahankali ya koma ya zauna a daya daga cikin kujerun parlour'n gumi na karyo masa cigaba yayi da kiran number su'ad sai dai amsa daya ake bashi wayar akashe take "oh my Godness have mercy on me "kar saka zuciyata shiga wani tashin hankali akan wanda nake ciki.. "idan wani abu yasamu yarinyar nan ni kaina zanshiga tashin hankali. "wannan tsinanniyar yarinyar ce tasa abubuwa suka dinga faruwa dani gashi komai yayi min tsanani Allah kasaka min abinda tayi min. Musty yak'ara so garesa yana sake godewa Allah kan wannan abun daya faru, ko babu komai abokinsa ya dawo haiyacinsa, kuka Ak yake sosai "Musty Zeey ta cuceni tacuci rayuwata tunda taraba ni da matata mafi soyuwa gareni yanzu ina zanga su'ad da cikin jikinta Musty..? " taimaka kagaya