← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 289

Sashe 130

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita yarinyar da ake zargi wacece ita? " waye ubanta agarin nan da zaka dinga daure mata gindi ? "ko dole ne sai jikana ya aureta nace dole ne sai aureta, kai adamu hjy takira sunansa kafi idona tun wuri wlh banason jin ka sake cewa komai akan mgnr nan matsawar ba goyon baya zaka bamu. "cike da sanyi murya dady yace hjy kiyi hkr amman ni nasan abinda nakeyi , shiyasa nace abi lamarin nan ahankali ita kanta baraka ta kasa fahimtata ne kawai amman zanyi kmr yadda kikace din . "da dai yafiye maka muhawara ce ta barke tsakaninsu ta yadda za'a yi,cikin hk kiran police yashigo wayar ak ,yana dauka suka sanar masa da sun gano inda zeey take yanzu hk suna tare da su'ad din domin ta su shiga inda ta boyeta ,AK ya zabura ya mike tsaye yana cigaba da receive din cal ,yana duban iyayensa dake zaune tsuru tsuru sannan "yace ok idan anga zeey din kuzo min daita gida kai tsaye ita km yarinyar da gang dinta ayi aresting dinsu ok sir. hmmmm...! dady ya sake naunayen ajiyar zuciya tare da numfasawa sannan ya fara mgn "hakika abdulkabir kana son biyewa son ran mahaifiyarka domin sake aikata babban kuskuren, wanda ita kanta zata iya shiga matsala daga baya. kuskuren da suka tafka a baya nake gudar mata sake faruwarsa ,amman taki fahimatata ,ke kanki hjy da ke ma, ya nuna maman zeey babu abinda bakusani ba ni kaina bawai ina bawa abdulkabir goyon bayan auren yarinyar bane dole, abinda zai je ya dawo din nake gudun afkuwarsa, amman babu komai tashi kaje. uhm dady ka daina kokarin hada yarona da maseefun da suka faru abaya da yarda allah babu abinda zai sameshi sai alkhari km muddin ina raye...... datse harshenta tayi da sauri sbd wani irin kallo da dady ya wurgama sannan yace "ki karasa man ai kinsan illar abinda hkn ya jawo wanda daga baya nadama ce zalla mara amfani. dady naga fadar hk yayi daidai da jiniyar police ya karade unguwar suka karaso gidan. gbdynsu suka mike tsaye sukayi waje ranga ranga AK yaga an fito da zeey dinsa rai hannun Allah rege regen karasawa gareta suke gbdynsu, yayinda mutane dake cikin part din ammi dana baki suka firfito harabar gidan. cikin sauri AK ya isa gareta yana fadin "zeey me suka miki, ina ke miki ciwo ? gbdy AK ya rude sai jera mata tmbayoyin yakeyi ya ma rasa me yakamata ya farayi mata zeey kuwa cikin tamboyinsa babu wanda ta samu damar amsawa illa wani irin nishi da take fiddawa da sallati samakon jin jiki datayi dan bakaramar azaba taci agurinsu ore ba. ga babu ci babu sha a kwana dayan datayi agurinsu babu irin azabar da basu gana mata ba. gani irin juyi datake tana rike ciki ai ak bai san sanda ya mike cikin gigicwa ya nufi dakinsa a guje dan dauko makulin . dube dube yake yi cikin dakin nashi yama rasa inda key din yake dan gbdy a rude yake. can ya hangoshi saman mirrow da sauri ya dauko ya fito dakin ya dawo da gudu inda jama'a ke tsaye cirkocirko suna kuka ita km zeey sai murkususu take ajikin ammi tana rike ciki da sauri yakaraso ya amsheta daidai lokacin da numfashinta ya dauke cak ... durkursawa yayi kasa yana kiran sunanta zainab... Zainab.... tare taba kumatunta amman ina babu numfashi atare daita dangi suka taru akansa suna kuka tare da tmbyr ta mutuko? hk ma police din dake tsaye sukayi kansu suna kallonta take suka gane suma tayi ,daman tunda suka dauko a sume take sai da suka yayyafa mata ruwa ta farka sun so wucewa hospital daita amman jin yace suzo masa daita yasa, hada baki police sukayi gurin cewa suma tayi ba mutuwa tayi ba. ai AK najin hk daukarta yayi da sauri, ammi na masa mgnr yabi ahankali ya tsaya wani ya tukasu amman ina hankalinsa kwata kwata baya jikinsa dan ko jinta bai yi, inda motarsa ke pake ya nufa , yakarsa ya bude kofar baya ya kwantar daita aunty bilkisu kanwar mahaifin zeey da aunty malika suka shiga motar hankalinsu a tashe shima cikin hanzari ya zagaya yashiga mazaunin direba , me gadin na ganin hk yayi saurin wangeme masa get din gidan. aguje AK ya fige motar kai tsaye asibitinsu ya nufa daita. likitoci suka amsheta cikin gaugauwa suka nufi imagecy room daita tsawon lokaci suna kanta suna kokarin dawo da numfashinta . zeey kuwa sai farkawa tayi ta ganta a gadon hospital, ta fahimci hkn ne ta hanyar ganin wata nurse a tsaye akanta ,dan tana bude idonta daita ta fara cin karo. tana kokarin sanya mata karin ruwa tayi saurin hanzarin mikewa zaune tana rarraba ido tare da tunanin abinda daya haddasa mata zuwa hospital, aunty bilki ce takaraso gareta jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya tayi mata abinda ya faru yashiga dawowa cikin kwanyarta, idanunta kmr gauta al'amar taci uwar wahalar da kuka ta koshi, km har lokacin kuka take. ta rike cikinta tana murkususu yunwa ga makoshinta ya bushe, nurse tasoma yunkurin rike hannuta zeey ta fizge hannuta daga rikon da nurse tayi mata ta kamkame jikinta waje daya tana mgn ahankali "wayyohhly Allah mutuwa zanyi yunwa nake ji kubani abinci naci sabatun yunwa take amman babu wanda yaji sbd muryarta a dace take. sai km tayi luuu! ta zame kan gadon ta sume daga aunty bilki har nurse suka gigice har aka rasa wanda zaiyi wani abu akai . aunty bilki tayo kanta tana girgizata cike da matsanancin tashin hankali da kiran sunanta cikin karaji, yayinda kukan datake rikewa tun dazu ya kwace mata. ita kuwa nurse da gudu ta fice daga dakin zuwa kiran doctor atare suka dawo dakin da doctor a wannan karon har da ammi da maman zeey da AK suka biyo bayansu. da likita da nures suka shiga yayyafa mata ruwa ai kuwa ta bude idaunta tare da sakin wata ajiyar zuciya ahankali danunta ya dauro akan AK dake tsaye kusa daita hannunta cikin nasa ,yayinda fuskarsa take tattare cikin yanayin na rudani. doctor naga dubata ya juya tare da cewa yana son ganin ak zuwa office dinsa. koda daya shiga office din likinta, kujerar dake facing ta likitan yaja ya zauna suna fuskantar juna yana tmbyrsa meye matsalar zeey ,ahankali doctor yasoma bayani atsanake. " bata tare da wata matsala byn raunukan dake jikinta sai km yunwa dake dawainiya daita, amman ka kwantar da hankalinka Inshaallahu zata samu sauki zamuyi duk abinda yakamata,amman yanzu a hanzarta kawo mata abinci da ruwan zafi. AK ya mike tsaye tare da cewa " yanzu kuwa za'a kawo mata yayi sallami da doctor tare da kiran aunty bilki ya damka mata wasu kudi a hannunta koda za'a bukaci wani abu sannan yagayawa ammi abinda ake bukata, tare da ammi da aunty malika suka baro hospital din ya saukesu agida shi km ya wuce xuwa police station. kai tsaye office din commissionier ya zarce yana cika yana batsewa yana shiga ya iske su'ad tsaye tare da commission suna zantawa a tsakaninsu shi kuwa AK ko kallon inda take tsaye baiyi ba yasamu guri ya zauna yana watsa mata kallon baza, itama abanzace take kallonsa kmr yadda yake aiko mata da nashi kallo zuciyarta na tafasa. rainshi yayi maseefar baci ganin kallon banza da take masa. " hkn yasa bai san sanda yace dan ubanki ni kikewa wannan banza kallo? dakata mlm ta katseshi tare da daga masa hannu karka sake zagin ubana idan kai baka san ciwon naka uban ba ,ni nasan ciwon nawa takarasa mgnr tana harararsa... " ance ubanki waye shi uban naki da baza'a zageshi ba ? "kai ma dan uban...atsawace ya dakatar daita ta hanyar daga hannunsa zai zabga mata Mari ,yaji sautin wata muryar ta doki dodon kunnensa daga bayansa kar ka sake ka fara taba lafiyarta, karkayi kuskuren aikata hk domin ba yarda zanyi da hkn ba ..ahankali ya sauke hannuna yayi saurin waiwayowa ahankali yaga kowaye ya katse masa hanzari . wata kyakkyawar mata yagani zaune tana kallonsa a wulakance, matsowa yayi sosai ya tsaya agaban umman yana kallonta tsab ,kawai rasa abinyi AK yayi sbd yadda yaga fuskar matar har lokacin tana watsa masa matsiyacin kallo sannan tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa, ko daganin hk sai shima ya xuba mata ido kmr yadda tayi masa yana kallonta sai daya gama kallonta tsab " muryarsa a fusace yace wace ke....? "sannan me ruwanki da marin da zan mata da har zaki dakatar dani ? da ruwana sbd nice nan na kawota duniya tayi mgnr tana nuna kanta kakiye dan ban haifi jaka ba balle ka mayar min da "ya" abin wulakantawa ta bashi amsa da hk. "ohh kice kece uwar wannan tantiriya shugaban yan jagaliyar data addabi al'umma? ya juyo inda su'ad ke tsaye yana kallonta atsiyace lallai kin cika uwa aike ba uwa yakama akiraki ba.... dau.. yaji saukar wani gigitaccen mari a fuskarsa wanda yasashi yin shock atsaye tare da zaro idanunsa a matukar tsorace yana kallonta eye's to eye's ita ce maresa ko km wani ne da ban? yayiwa kansa tmbyr acikin zuciyarsa . "tsaki ta ja tana kallon kwaryar idanunsa kul.. ka iya bakinka kasan me zaka gayawa mahaifiyata ita din ba kmr kowace uwa bace, ina sonta fiyye da komai, ina girmamata km ina son a girmama min ita duk rashin mutuncina bazan kalli tsabar idanun uwarka nace zan zageta dan hk kasan abinda za fada mata.... hannusa ya daga a zafafafe zai zabga mata mari tayi saurin dukawa kasa tare da matsawa baya,aiko ya dauketa da kafafunsa tayi sama ta dawo kasa tim ..yashiga dukanta , umma naganin hk tashiga kururuwa tare matsowa ta rike hannunsa gam tana yiwa commissionier nuni da idan yayi diyarta illa bazata yarda ba... .. a wulakance AK "yace ki sakar min hannu tun ban hada dake ba yanzu bazan saki hannuka ba sai ka sakar min "ya" tunda ba jakar ubanka bace take office din commissionier ya hargitse da hayaniyarsu har sai da wasu police guda biyu suka shigo suka shiga tsakanin AK da su'ad datake rike a hannunsa ,da kyar commission yasamu ya shawo kansa ya hakura ya
Chapter 130 · 0% Book details