← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 289

Sashe 126

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *Allah's messenger saw said fear Allah wherever you are* page 46 wani tafkeken jirgi naga an soma nunowa me dauke da tarin fasinjoji bil'adadi ,yayinda me gabatar da labarai tasoma gabatar wa kamar haka cikin harshen tsadadden turancinta . " take ni kuma dake zaune akan kujera na tasa TV gaba da ritsetsen cikina ina kallon abinda ke faruwa in banda faduwar gaba babu abinda gabana keyi. ahankali na fara karanta rubutun dake rubuce a k'asan TV abinda nagani ne a rubuce yasa naji cikina yayi wani irin azababben Murdawa da karfi, nan da nan jikina naji ya fara kirrrrrrma, gaban TV na isa na koma nayi zaman dirshan cikin matsanancin tashin hankali, tare da kafe TV da idanuna. jirgin daya taso daga k'asar Spain zai iso Nigeria a yau, sannan zai sauka a jahar Lagos, a murtala international airport dake Lagos . ya iso cikin garin Lagos amma bai samu damar qarasowa airport ba, a kasamu air Crash, jirgin ya fada wani babban filin kwallo ne dake ablegba. Life suka shiga nuna yadda abun ke faruwa ga dai jirgin zaune a k'asa ya sauka yayi tsaye, ma'aikatan cikin jirgin suna kai kawo acikinsa domin kokarin ganin murfin kofar jirgin ya bude. , sunyi sunyi k'ofar jirgi ya bud'u amma ina kofar taki buduwa, ga mutane nan ana hangowa muraransu. kuma mutanene cikin jirgin bil'adadi hankalinsu a mutuk'ar tashe yake, hannu suke sawa ta jikin window jirgi dayake glass ne sai faman ihu wasu daga cikinnsu sukeyi. yayinda musliman ciki suke salati suna neman dauki daga gurin Allah. amman fa duk sun rikice wasu ma kana gani sai faman kuka suke. "Wata mace na hango zaune cikin shigarta na kamala ta d'aga hannunta sama Wanda da gani kasan addu'a takeyi ga yaro a gefenta sai faman tsanyara ihu yake. " k'ara fiddo idanuna waje nayi domin k'ara tabbatar da abin nake gani aiko kamar gidan TV sunsan me nake son kara tabbatarwa, haskomin fuskar Matar sukayi da kyau aiko take na gane Matar taufeek ce shi km yana zaune a natse agefenta yana motsi da bakinsa bazaka taba cewa cikin maseefa da tashin hankali yake ba. sai dai hannusa rike da waya wanda bansa abinda yake daita ba . " kalmar innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nashiga furtawa ina maimaitawa jikina na sake daukar kirma. lokacin da naga matar taufeek ta matso gareshi ta rumgumeshi ajikinta tana kuka tare da danta, shima rungumeta yayi sosai tare da cire farin medical glss din dake manne da idonsa yasa hanky yana goge fuskarsa hannunsa daya abayanta yana rarrashinta. Jama'ar dake waje a ka shiga nunowa kowa kagani agurin ta kansa yake, sannan a rikice babu mai kokarin kusantar jirgi hatta ma aikatan da sukazo wuri ta kansu suke suna gudun ceton ransu , Sanadiyar ganin tanking jirgin ya bude diesel ya falle kamar an kunna fanfo sai faman tsiyaya yake . jirgi na nan tsaye kmr tun farko da'aka soma nunowa, yakai tsawun minti talatin diesel na zuba wanda a lokaci hankali mutane cikin jirgin gbdy yayi k'ololuwa tashi. Bayan diesel din yagama tsiyayewa tas, sannan wani irin kara me sauti ya karade gurin , bammmmmmm kakeji jirgi nan yakama da wuta kanajin ihun jama'a musliman dake cikin jirgin suna ta salati da salallami. "kafin kace me har gurin ya turnuke da hayaki ga namomin mutane nan muraran kana gani da k'asussuwansu. gaba daya jama'a dake cikin wannan jirgi babu wanda ya tsira da rayuwarsa, dan ko mutun daya ba'a samu ba, naman su yayi fatsafatsa. gidajen ko da suke da kusanci da football field din nan babu wanda be kone ba sai ta bangaren dama inda bata nan tankig jirgin yake ba ,gidajen da suka k'one gasu nan bazasu kirgu ba daga bangaren hagu. Wani irin razananniyar k'ara me sauti na saki lokacin danaga me afkuwa ya gama afkuwa daga nan ban sake sanin meke faruwa dani ba. umma taja numfashi tare da ajiyar zuciya ta sauke hawaye nabin kuncinta wanda ita kanta su'ad din kuka take wiwi har tafi umma shiga tashin hankali. "umma tacigaba a she a daidai wannan lokacin da abin ke faruwa doctor rak da ahlin taufeek suma sun ga komai daya faru . doctor rak bai tsaya gama kallon news din ba ya baro office dinsa hankalisa a tashe sbd yasan da dawowar abokinsa ranar dan shine ma zaije airport ya daukosu . direct motarsa yashiga aguje yakama hanyar zuwa gidana dan baya son naga abinda ya faru sbd condition din danake ciki. ya karaso daidai kofar dakina kenan yaji sautin ihuna cikin matsanancin tsoro take yashiga ihun kiran sunana yana murda handle din kofar ,sai dai kofar a rufe take kmr yadda taufeek yabani umarnin na dunga kulleta akoda yaushe . ta window yazagayo ya hangoni a sume a kasa ya koma ya nemo jama'a aka tayasa balle kofar ,ya daukeni raina hannun Allah sai asibintinsa.. aka shiga bani taimakon gaugauwa sai danayi kwana biyu a sume sannan na farfado bakina dauke da kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,cikin matsancin kuka ina kiran sunan taufeek .... sai lokacin nasan inda nake a she hospital din Doctor rak ne. iya tashin hankali nashigeshi nayi kuka har na galabaita hawaye ne kawai ke zuba daga cikin kwarnin idanuna dan ko iya matso hawaye daga idanuwana ban iyawa sannan an daina jin sautin kukana. tsawon sati daya ina kwance a hospital ana jinyata ,doctor rak ne tsaye akaina yana rarrashina da bani baki. kallon bakinsa kawai nake amman zuwa wannan lokacin bansan me yake cewa ba, gani yayi da ala'mun bana cikin hankalina yasa ya kai hannunsa ya taba fuskata yaji wani irin zafi, tashi yayi yaje ya hado min ruwan zafi daidai yadda bazai kune min baki ba. ya dawo yayi tsaye akaina ya miko min ko kallon inda yake banyi ba hawaye nacigaba tsiyaya. muryarsa a sanyaye naji ya kira sunana saleemat... kmr yadda taufeek ke kirana dashi, still ban waigo na dubi inda yake tsaye ba. "yace kiyi hkr da hukuncin da Allah ya zarta miki akan rashin abokina da kikayi. "hakika nasan duk wanda zaiji zafin mutuwarsa byn ke da mahaifiyarsa ne sai km yar'uwarsa. "amman ina son kiyiwa darajar Allah da darajar cikin masoyinki taufeek dake jikinki kici wani abu sbd kare lafiyar baby. "ki duba kiga yau tsawon sati daya kenan bakisawa cikinki komai ba ,idan wani abu yasamu cikin jikinki me zaki kalla amatsayin taufeek dinki? wannan mgnr da yayi shine ya dawo dani cikin haiyacina na waigo inda yake ina kallonsa. sannan jikina na rawa na mika masa hannuna. ya mika min kofin tea din, na amsa na kafa cup din abakina ban cire ba sai dana shanye tass, sannan na mika masa ina runtse idanuwana. aiko gama shan tea na ke da wuya "yar" cikina tayi wani murdawa da karfi daman tun lokacin dana riski kaina cikin tashin hankali, ban sake jin motsinta ba sai a wannan lokaci dana gama shan tea . bayana da marata ne suka rike alokaci daya , na dinga jin tmkr ana sara min bayana da gatari, ga wani azabar ciwo dana dinga ji from know where. ahankali na sake runtse idanuwana gam gumi na karyo min ta koina ajikina, doctor rak naganin hk yashiga tmbyta . ni kwata kwata na kasa mgn . sai sake maimaita kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nake jikina kuwa sai faman kirrrma yake wani tashin hankali ne ya sake ziyartata lokaci daya wanda yasa da kyar nake iya janyo numfashina . bell din jikin bango naga doctor rak ya danna sai ga likitoci maxa da mata akaina ya bawa wata doctor damar ta duba masa lfyta. cikin kwarewa likinta wacce tasan aikinta , ta gano na kudace ta kamani . ai ko take batare da bata lokacin ba ,akayi dakin haihuwa dani. byn uwar wahalar dana sha gurin nakudar haihuwarki sannan aka samu kikazo duniya .dan akalla sai dana shude sama da awa goma nasamu kaina . aka fita dake domin agyaraki nima akimtsani. wani dakin aka kaini domin hutu sannan aka kawo min ke, kina rike a hannuna na tsura miki ido ina kallon tsarin halitar da Allah yayi miki kyakkyawa ce tmkr mahaifinki yayi kaki komai irin nasa kika dauko babu abinda kika dauka nawa hatta yatsun kafafunki dana hannu irin nasa ne. hkn yasa lokacin dana daura idanuna akanki na dauki son duniya na daura Mike, naji duk duniya babu me rabani dake soyayyar danakewa mahaifinki na tattara na daurata akanki. ranar da muka cika sati daya Doctor rak ya tmbyeni wani suna za'a miki huduba dashi ? zance mahaifinki ne yashiga yawo cikin 'kwalkwaluta idan yace mace na haifa sunan mahaifiyarsa zai sa idan km nmj ne sunan mahaifina. ,dan hk nayi kokarin cika masa burinsa " ahankali nacewa doctor rak yayi miki huduba da sunan mahaifiyar taufeek su'adullahi . .. km a ranar ne doctor rak yake gaya min wai yaje gidansu taufeek ya iske mahaifiyarsa da yan'uwansa cikin halin damuwa . nan docto rak yashiga bani labarin halin da mahaifiyar taufeek ta riski kanta lokacin da labarin mutuwar taufeek ta risketa . kusan zaucewa tayi tana kuka . inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda hjy mahaifiyar taufeek ta dinga furtawa, jikinta sai faman rawa yake ,wani irin tashin hankali ne ya farmaki rayuwarta da kyar ta iya tashi zuwa inda tangameme hoton tilon d'anta yake ajikin bagon dakinta tashiga kallonsa. " Muhammad taufeek dina na yafe maka duniya da lahira baka min komai ba sbd kai yaro ne na gari me biyyaya wanda baka taba sabawa umarnina ba . a koda yaushe kana 'kokarin yi min biyayya,, "Allah ya gafarta maka yasa ka huta. "Allah yasa aljana ce makomarka kai da iyalinka. hk hjy tashiga yiwa taufeek addu'oi tare da yabawa da fadar kyawawan hallaiyansa. kwana biyu tsakani yayar taufeek din da suke uwa daya uba daya tazo nan fa kuka ya dawo sabo. doctor rak " yace min yana zaune agurin byn ya baro gurin zaman makoki lokacin da yayar taufeek ke sanarwa hjy labarin ai muna tare dashi bamu rabu ba. km har inda cikin wata bakwai . nan hklinta ya sake tashi ta dinga kuka
Chapter 126 · 0% Book details