Sashe 66
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam :assaburu nisful iman* *Allah's messenger (s a.w) said patience is haif the faith* page 25 wani abu ne me kama da dalma yaji yana masa yawo a dukkanin ilahirin sansar jikinsa. ,tun daga tsintsiyar kafafunsa har zuwa tsakiyar kanshi yake jin wannan radadin . "mgnrta ba iya sansar jikinsa kadai ta tsaya ba har cikin zuciyarsa yake jin dacin kalmar datayi amfani dashi. babu wata mace datasamu wannan damar ta cin zarafinsa da tsohon ciwon jikinsa. yau shine karo na farko da hkn ta faru dashi. ko lokacin dayake cikin ganiyar ciwonsa bai samu wanda ya zageshi dashi ba sai yanzu daya tabbatarwa kansa babu sauran burbudin wannan ciwon ajikinsa . hakika zai ganar daita kuskurenta na shigowa cikin rayuwarsa datayi. ayau ne zai nuna mata shi din wanene da true colour dinsa . zai wujijjiga rayuwarta tasan shi ba sa'an yinta bane .. ya juyo a harzuke jikinsa na tsuma yasoma takowa ahankali zuwa inda take tsaye. fararen idanunta masu kalar madara ta sanyasu akansa tana kallonsa. kirjinta ne yayi wani irin mahaukacin buguwa da karfi . take km zuciyarta tashiga shawagi da girgiza tare da harbawa. lokacin daya fargaba tattare da matsanancin tsoronsa ya kaiwa zuciyarta bakunta. daidai ya kusan karasowa gurinta tasoma ja da baya da baya sbd matsanancin firgita datayi da ganin yanayinsa. wayyohhly Allah ta furta acikin zuciyarta .... ya Allah ka taimakeni ka taimakeni kar yayi min komai... matsota yacigaba da yi a matukar fusace tana ja da baya . jitake tmkr kasa ta tsage tasamu gurin buya acikinta batare daya cimmata ba . bata ankara ba kawai tajita ta zube jikin saman wata mota wanda kadan ya rage hannunsa bai kai jikinta ba tsabar tsuma da jikinsa ke yi . tmkr wani mayunwacin zaki yakaraso gareta zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu me tattare da muguwar tsanarta da takaicinta . ya rankwafo samanta . kirjinsa na bugawa yana kallon yadda nata kirjin dake sama da kasa ala'mun atsorace take. sannan km numfashinta nafita sama sama. ahankali numfashinsu yasoma gyaraya guri 1 zuwa wani shauki na daban. " yayinda nata numshinta tare da kamshin turarenta dake kaiwa hancinsa farmaki suka shiga circulating cikin kwalkwaluwarsa . ganin abunda ke faruwa yasa musty kamewa guri daya yana kallon ikon Allah da abun mamaki tamkar wasu sumammun masoya wayanda suka shahara cikin duniyar shauki juna. mayatattun idanunsa ya tsura mata yana mata kallon da bai san lokacin dayakeyi aikata hkn ba, tayi saurin runtse fararen idanunta, Dan jin wani abu na tsarga mata har cikin kasanta da kirjinta . tsawon lokaci ya dauka yana kallon kyakkyawar fuskarta kafin daga bisani ya tuno abinda yakawoshi gareta . wanda yake shirin aikata mata . take ya dawo abdulkabir dinsa sak... tare da murtuke fuskar nan tasa tmkr kumurcin maciji. hannusa dake rawa ya kai ya damki makoshin wuyanta muryarsa na rawa yace ni.. ni kike cewa tsohon me cutar farfadiya....? take idanunta suka birkice suka soma raina fata sbd yadda ya shakar mata wuya. tashiga girgiza masa kai . musty dake tsaye tmkr picture yakaraso gurin da sauri. ak kabar yarinyar mutane karka mata illa ....... wai meyasa kake daukar komai da zafi ? wannan abun da zaka aikata kuskure ne .hannusa daya yasa ya hankade musty baya . batare da yace masa komai ba .. yashiga zuba mata wasu gigitattun maruka masu fitar da mutun cikin haiyacinsa . wanda yasa take jinta da ganinta yasoma daukewa . ya mikar daita tsaye bisa kafafunta yasoma janta sai jikin wani bango gida yana kaiwa bai tsaya wata wata ba ya buga kanta da bango.. ta saki wata razananniyar kara tare da fashewa da marayar kuka..... zaki sake furta min wannan bazanr kalmar taki mara ma'ana .? tayi saurin giriza masa kai ala'mun aa . cikin muryarta dake nuna sanyinta tace Dan girman Allah kayi hkr bazan sake ba amman ina son kasan wani abu raba zuciyarta da sonka bakaramin tashin hankali bane, na fada sonka batare da nasan sanda hkn takasance dani ba. wasu maruka ya sake zuba mata take bakinta ya balle da jini..... matsawar bazaki daina furta wannan banzar kalmar gareni ba . zan rabaki da numfashinki ...zaki bar duniya batare kinyi nasarar cikar burinki ba. zan la'antaki na la'anta rayuwarki ...yana karasa fadar hk ya sake buga kanta da bago ginin...ta km sakin kara tana furta kalmar pls.. da kyar musty dake washe gefe guda yasamu ya mike tsaye ya tattaro dukkan wani karfi yasanyawa gangar jikinsa tare da shiga tsakaninsu yana kokarin kwatarta . ,da kyar musty yasamu ya kwace su'ad a hannunsa wace ta zube kasa tmkr wata sumammiya kafin daga baya tasoma fidda numfashi sama sama tana kallon cikin idanun ak hawayen tausayin kanta dana tsagwaron kaunar datake masa yashiga ganganrowa daga cikin kwarnin fareren idanunta. ak yashiga nunata da dan yatsan hannushi wallahi matsawar baki rabudani ba kadan kikaga zan shayar dake guba da zata la'antaki ... hannusa dake rawa ya miko mata bani littafin sirrina..... tashiga girgiza masa kai bazaki bani ba? ya tmbyeta nan ma sake girgiza masa kai tayi tana kokarin boye jakar hannuta. motsota yayi sosai tare da saka kafarsa dake saye da takarmi ya take hannunta 1 yana mutsutsukawa....... ta saki wata azababben kara . ya fixge jakar ya bude. idanunsa ne suka sauka akan littafin sirrinsa wanda ya nema yarasa tsawon lokaci. yaciro yana turawa cikin aljijun wandonsa sannan ya maka mata jakar a fuskarta. a matukar fusace yashiga janta yana marin fuskarta har sai daya kaita tsakiyar unguwar sannan yayi filinging daita yana tsare zan baki shawarar ki tsaya iyakarki........ kana ya juya fuuuuuu yasoma takawa cike da izza zuwa gidansu . rakiyar da baiwa musty ba kenan. da sauri musty yakaraso gurinta tunaninsa ko ta suma ne amman sai isketa tana fidda numfashi hawaye na ganganrowa daga cikin idanunta . nan yayita bata hkr da bata baki akan ta hakura ta rabu dashi tunda yace bai sonta . nasan halin abokina tunda abdulkabir ya furta bai sonki bafa zai taba kaunarki ba har abada .. ta mike da kyar tana shafa wunyata datake jinsa kmr ya dan soma tasawa alamun kunbura. wani irin radadin azabar ciwon gurin take ji sannan tace wannan karon zai yi abinda bai tabayi ba a tsawon rayuwarsa .. sbd zai soni koda kuwa shine abu na karshe da zai aikata ya bar duniya... amman matsawar ina numfashi sai na mallaki zuciyarsa da gangar jikinsa ........ kallon tababbiya mara hankali musty yake mata tare da jinjinawa karfin halinta. yarinya bazaki taba gane waye abdulkabir ba sai yayi miki illar da bazaki taba mantawa dashi ba yayi mgnr cikin ranshi. da hannu musty yayi mata nuni tashiga mota. muje na kaiki hospital a dubaki... bata tsaya yin musu dashi ba sbd ita kanta tasan jikinta na bukatar hk . duba da yanayin yadda goshinta da bakinta ke fidda jin . shiga gaban motar tayi suka nufi wani karamin hospital . byn an yi mata treatiment din gurin ya dauki hanyar gidansu a motarsa da kwatance data masa. tafiyar da suka yita suna tautaunawa. musty na sake sanar daita akan tsautsauran ra'ayin ak da rayuwarsa. byn ya sauketa yabata kudi masu yawa ta kula da kanta. " amman furrrr taki amsa sai ma godiya kawai data masa tare da shigewa cikin gidansu dafe da goshinta. ak nashiga gida kai tsaye part dinsa ya nufa yasoma balballe boturan gaban rigarsa, gumi ne ke tsatsafo masa takoina a ilahirin jikinsa surutu kawai yake tare da ciro litafin sirrinsa yana dubawa tabbas litafinsa ne.. to a ina tasamesa...? yayiwa kansa tmbyr. ranar hk ya wuni yana juyi da tunaninta da gaske sonshi take ko tausayin abinda takaranta acikin litafin sirrinsa take. Amman zai so ya zauna tare da musty domin zantawa dashi akanta akaro na farko. hakika yana son sani wani abu game daita kafin ya sake daura idanunsa akanta . wayarsa dake gefensa ne ta dauki karar sauti alamun ana kiransa runtse mayatattun idanunsa yayi sannan ya bude idanunsa ahankali ya kai dubasa ga inda wayar take . ganin wace ke kiran ne yasa shi sakin dan gajeren tsaki yana furzar da iska kafin ya dauka.. Hello yayi mgnr a kasalance tare da sake runtse mayatattun idanunsa . abangaren zeey kuwa sanyin dadi ne yakamata daga ina da take zaune akan gado ,ko babu komai taji muryarsa mai sakata jin kasala da samun natsuwa cikin ranta. tunowa datayi da abinda yasa ta kirasa, yasa tayi saurin janye murmushin dake saman fuskarta. a sanyaye tace an wuni lfy my life ? lfy yabata amsa ataikace yana cixan lip's dinsa na kasa kadan, shr tayi cikin rashin jin dadin yadda ya amsa mata. kusan tunda ta baro kasar Nigeria lamuranta suka sauya suke neman tabarbarewa ta kasa gane kasan. wanda tasan ba komai bane ya haifar da hk illa aikinta dayayi sanyi yake bukatar tishi ,duk da hkn bai sa tafasa mgnr datayi niyya ba, dan hk muryarta ahankali tace yaya abdulkabir ........daman najika shr baka nemi ne ba tunda muka baro nigeria ,gashi ina son. mgn me mahimanci dakai shiyasa nakiraka yanzu. "dan dakatawa tayi taji me zaice . shiru yayi batare da yace komai ba a tunanin zeey ko bayajinta ne ko km layin ne ya tsinke .. dan hk tasoma fadin hello ..hello.. hello ..my life kanajina. dan numfashi yaja ya sauke da kyar.... kinga zeey ina wani abu ne yanzu ba km nason takura ko damuwa we will talk later ok.. batare da yajira abinda zatace ba yakashe wayar . shiru yayi yana sake jin kirjinsa na rawa da bugawa akan tunanin su'ad da tunanin irin dukan da yayi mata . sosai tunaninta yashiga yamutsa kwalkwaluwarsa. ya matsu su kasance tare da musty yaji ina ya kaita sanda ya dauketa ,dan yaga lokacin datashiga cikin motarsa. wayarsa da sake daukar sauti ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula amman yaki dauka.. duk da yaga kiran dady ne. tunda ya katse kiran take rike da wayar a hannuta cike da matsanancin damuwa ta rafka uban tagumi allah yasani tana matukar kaunar abdulkabir so wanda bazata iya misaltashi ba. tun kafin tasan kanta take faman wahala da