Sashe 269
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dade zaune tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sani madafa, yadda take hango rawar kansa akanta kad'ai yake d'aga mata hankali domin abubuwa yake kmr wani sabon matashin ango, abu me mahinmmaci datake hangowa atattare dashi bai wuce tsagwaron kauna dayake mata ba, musamman soyayyarta datake hangowa a yanzu acikin kwayar idanunsa. yashigo d'akin bayan yayi wanka sanye cikin wata haddiyar jallabiya ruwan coffee colour yana baza kamshi me sanyi dadi ya jingina bynsa da jikin murfin k'ofar shigowa d'akin yana kallonta cikin hadadden shirinta dan sanye take cikin laulausar rigar bacci cike da matsanancin farinciki bakinsa ya kasa rufuwa yacigaba da kallonta "a yau bazei iya kwantata tarin murna da farinciki zuwan wannan ranar ba wannan lokacin, lokacine dayake cike da tsantsar nishadi da farinciki,tsawon lokaci yana tsaye agurin yana kallonta ,sihirtaccen kamshin turarenta na bugar masa da zuciya kafin ahankali yasoma takowa zuwa inda take itama ahankali ta taso suka rungume junansu suna murna kasancen ma'urata "cikin kunneta yayi mata rad'a "kina nan kamar yadda nasanki da wannan kamshi naki dake zautar dani," muje akwai tanadi me mahimmanci danayi mana daga yanzu mun shiga duniyar farinciki babu mu babu bak'inciki arayuwarmu . yasoma tafiya daita har suka k'arasa atare suka zauna a bakin gado tare da riko tafin hannuta wani irin lumshe idanu yayi domin shi kad'ai yasan irin farincikin daya tsincin kansa saboda zamowarta mallakinsa, kallonsa tayi tare da sakin laulausan murmushi domin tasan tunanin dayake bai wuce kasan cewarsu tare cikin inuwa daya ba. ta shafi gefen fuskarsa tare da bud'e bakinta tace "abban su'ad .. ya bude kyakkyawa idanunsa ya zuba mata yana kallonta batare da yace komai ba "muje muyi alwala muyi sallah domin godiya ga mahalinmu daya nuna mana zuwan wannan rana.. yayi murmushi "ranar da muka so ganinta tun ganinyar kurciya ba Allah bai yin ba sai yanzu" tashi muje d'an ala hakikanin gaskiya jina nake tamkar sabon matashi "kai abban su'ad kafa tsufa.. "tsufa fa kikace ai namiji baya tsufa most especial agurin macen dayake tsantsar so," duk wani kulawa da gatan da kika rasa a shekarun baya zan tabbatar dana baki shi a yau.. "ni dai babu ruwana ni yanzu na girma nabarwa yara ,yayi laulausar murmushinsa bayi suka shiga sukayi alwala suka fito rike da hannun juna kamar zasu hadiye junansu yana gaya mata kalamai masu sanyi bayan sun idar da sallah ta kasa motsi tana zaune akan sallaya tana dubansa dan oredy shi ya rigada ya mik'e tsaye har ya isa kan gado maganganunsa kunya suke bata hannunsa ya yafitota ala'mun tazo sun dad'e suna bawa junansu kulawa daga k'arshe suka sake shiga bayi domin yin wanka tsarki ranar baccin barawo kasa dcaukarsu yayi da zarar sun runtsa idanunsu da zumar yin bacci sai subud'e domin ganinsu suke kamar zasu nemi juna su rasa acikin kwanaki wata irin kulawa Prof taufeek ke bawa Umman su'ad wadan hkn ke sake tabbatar mata da taufeek dinta daban yake acikin mazajen duniya, har take da yakinin bakowani nmj ne ke wulakanta mace ba byn ya amshi budurcinta a waje, su kaddara ce haka kmr yadda nata kaddarar yakasance tare dashi. shema ta kawo mata ziyara inda ta bar gidan batare da tashiryawa hkn ba saboda ganin yadda taufeeq ke nuna kulawarsa akan umman su'ad. bayan tafiyar shemah umman su'ad ta hararesa tare da cewa "kai ko .. "menayi umman su'ad? "dan Allah meyasa kakeyin hk ? "Ko bakasan ka girma bane kai fa kaka ne yanzu? ya janyo hannunta ta fada jikinsa "gsky ne amman yazanyi kurciyata nake son gyarawa a soyayya babu wani zance tsufa yakarasa mgnr yana lumshe mata idanu ta mike ta nufi kitchen "bazan iya da rashin kunyarka ba Allah. "ya girgiza kai yacigaba da karanta jaridar daily trust yana murmushi wata irin soyayaya suka gudanar atsakaninsu, ji yake kmr yacinyeta duk inda tayi yana biye daita ko wajen aura tayya baya gajiya da ita kafin sati d'ayan da zai yi agurinta ya koma gurin shemah umman su'ad tagaji matuka, a cikon daren na bakwai suna lullube cikin bargo ya manneta ajikinsa gbdy ya hanata saka umman su'ad "tace kai wai menene haka...? "yanzu fa ka girma amman sai naji kamar karfi kak'ara, "amu'amularmu a lokacin baya baka wuce kayi sau biyu amman yanzu daya kamata karage malam shine kuzarinka ke sake karuwa..? murmushi yayi yana dubanta sannan yace "da menayi? "ai yanzu ne nake jina a d'an shila na, gani ga sahibar rayuwata, jina nake kamar matashi d'an 30yrs tayi murmushi ba ita tasamu kanta ba sai daya koma gurin shema wanda komawarsa bai sa ya barta ta huta ba, dan kiran safe daban na rana daban na dare daban shemah duk abinda zaiyi da idanun take binsa, abun ma baya damunta dan bai rageta da komai ba daman kuma a soyayya dole tasirin wata zai fi nawata ita dai burinta su kasance tare muddin rai. ************ har lokacin Ak bai hakura da neman su'ad gbdy yagama haukacewa tuburan ne kawai baiyi ba kowa yagansa sai ya tausaya masa, sanin inda su'ad take ne yasa Ammi da Dady sake janyosa cikin lamarinsu, sukayita rarrashisa da bashi baki tare da bashi shawarar ya koma bakin aikinsa dan ma musty na tsaye akan komai da abubuwan sun sake tabarbarewa. alokacin haushin kowa yake ji cikin zuciyarsa most especial iyayenta da sukayi buris da lamarinta suka sanyawa zuciyarsu salama babu abinda suke sai cin duniyarsu da tsinke. hakika idan kaga Ak bazaka ce wannan matashin mutumin bane me ji da kansa da izza tare da nuna iko da isa. yayi wani irin baki ya rame ga kasunba ya tara, yaki yin aski da kyar Dady yasamu ya shawo kansa akan zai koma bakin aikinsa. Ranar da zai koma Dady da kanshi ya tasa shi gaba zuwa gurin aski aka masa aski suka dawo gida amman duk da hk Bai jin zai cigaba da zuwa office alhalin bai san inda matarsa take ba. umman su'ad tayiwa Ammi magana akan yaka mata Abdul yasan inda su'ad take tunda har yanzu matsayin matarsa take "eh nima nayi tunanin haka amman dady'nsa yace "kar a sanar masa yanzu sai zuwa wani lokaci, dan ta haka ne zai sake sani mahimmancita a duk sanda ta dawo hannunsa. umman su'ad tayi murmushi "nidai dan Allah kuyi hkr kubashi matarsa ya daina jin haushinmu atare sukayi dry sannan umman su'ad ta katse kiran takira mahaifiyarta suka gaisa har su'ad din sun dade suna hira. tsaye yake a cikin tafkeken office dinsa wanda rabonshi da shigowa cikinsa tunda abin ya faru bai sake waiwaiyar komai nashi ba, yanzu da taimakon Ammi da Dady ne yasamu yazo gashi zuwan nasa bashida wani amfani ,tunda gashi ya kasa aiwatar da komai sai zariya yake acikin office din goye da hannunsa yana tunaninta ahankali ya waiwaiyo ya kalli hotonta da shine ya dauketa a koria "yace kingani ko hrt beat komai na rayuwata ya canza tunda kika tafi kika barni bana son jin dadi komai banason ayi min abinda zaisani naji dadi har nayi dariya saboda banason nayi dariya matukar bakece kika bani shi ba. " murmushinki fuskarki da komai naki kawai nake son gani duk inda zanje nemanki naje ki taimakawa rayuwar mijinki ki dawo gareshi .. "mijinki na cikin mawuyacin hali na rashinki . ya zagayo ya zauna tare da tsurawa system dinsa idanun yana cigaba da kallonta wanda hakan ya ke sake hargitsa masa kwakwalwa yashiga nemo sauran hotunanta . zuciyarsa na dokawa tashiga yi masa gezo tana masa murmushi yana nan zaune yana kallonta har sanda sectary dinsa yashigo ya ajiye masa coffee ya juya ya fita awuni uku suka shud'e yana zaune babu abinda yayi sai aikin tunaninta yaji motsin shigowa office din. ahankali ya bude mayatattun idanunsa da suke a runtse ya d'aurasu akan fuskar Musty yasoma kokarin k'arasowa inda Ak yake, tashi yayi daga zaune dayake ya dayo yana layi tamkar wani mashayi ya zauna akan doguwar kujerar gefenshi Musty ya zauna tun awa daya data wuce Ak suna tare da Musty ,musty ya kalleshi yace " haba abokina dan girman Allah ka saki ranka kalli yadda ka dawo a dan kwanaki da basu wuce wata daya ba? "Na san abu da ciwo amman daurewa zakayi wani irin kallo yayi masa me had'e da harara "ka saki jikinka dan Allah kayi lamurar gabanka akwai abubuwa dayawa agabanmu wanda dole sai da taimakonka komai zai tafi daidai dan girman Allah ka daina fito da damuwar ka a gane. Ak ya kalleshi ya girgiza kai "fito da damuwa yazama dole yanzu zaka had'a damuwata data iyayenta ? "Musty kalli yadda na damu akanta kalli yadda nabi na k'are akan su'ad banida lokacin kaina wallahi bana runtsawa yadda naga dare hk nake ganin rana. Musty yayi murmushin takaici sannan yace " kaima kadamu daita ne saboda Allah Allah kakeyi kaga danka dake jikinta "kadamu da su'ad saboda cikin jikinta, zance iyayenta a kullun bazan daina fad'a maka bakafisu damuwa daita ba kai kanka yazakaji idan karasa cikin jikinta? ya runtse mayatattun idanunsa yana jin zafin kalmar musty "wai meyasa musty bazai fahimce sa ba? "meyasa bazai gane zahirin damuwarsa akan matarsa ba? "shi yasan yana Allah Allah ya mallaki cikin jikinta amman wallahi yafi bukatarta akan duk abinda zata haifar masa, ita ya fara samu kafin yasamu cikin jikinta saboda idan tana kusa dashi shi kadai yasan irin farinciki dayake," yanzu bai san yadda zai misalta yadda yake ji ba sannan yace masa saboda cikin jikinta ya damu daita cikin da bai sani ba rayayye ne ko akasin hk? ahankali ya furta "musty ansani nayi hasarar sosai ,ina matukar son matata aka gurbata min tunani akantan" ina son su'ad ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan misalta maka ba ina jinta acikin nama jikina ban san haka so yake ba sai a yanzu dana rasa abinda nake so da muradi . "kullun na tuna abubuwa da zeey tayi min alokacin baya sai naji wani iri daci ya tsaya min amakoshi ,tundaga lokacin dana waye gari banganta tare dani ba ban sake jin test din komai abakina ba why zaka dinga ganin ban damu daita "ka duba kaga yadda iyayenta ke rayuwarsu daya ne da yadda nike a rayuwata ayanzu? " musty