← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 289

Sashe 120

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

nakaraso na zauna gefen gado. itama guri tasamu ta zauna gefen gadon kusadani tana me taba wuyana taji ko har lokacin jikina da zafi. zafin daya ratsa tafin hanunta kmr garwashin wuta yasa ta kamoni ta kwantar dani . mike tashiga bayina taje ta dibo ruwa acikin yar karamar robo da towel ciki wanda ni har ina gadona kwance lamo makale da tunanin taufeek tasoma matse towel din byn taciremin yar rigar shimin dake jikina ta dinga goge min towel din tana meida shi cikin ruwan tsayi kafin kace min har zafin jikina ya ragu. ******* ranar daurin aurena tashi nayi jikina a sanyaye ji nake kmr narasa komai na rayuwata ne. yayinda hklina gbdy baya gangar jikina banda kuka babu abinda nake . bakaramin tashin hankali mamma tashiga ba ita da sauran yan'uwana taki yarda tayi nisa dani tana dakina takasa barina sai da wasu daga cikin daginta suka zo sannan taje gurinsu . ni kuwa tattare da kololon bakin ciki wanda ya hanani walwala da sakin fuska balle na damar fitowa tsakar gidanmu. " yayinda gbdy dagina na nesa dana kusa sun hallara . duk da ansa bana son auren amman hkn bai hana wasu daga cikin dagina bayyana farincikinsu ba. ina zaune cikin matsanancin tashin hankali mamma takirani a waya tace nazo dakinta alokacin tana son ganina. na mike da kyar jikina na rawa na fito daga dakina ina fitowa babban parlour gidanmu ina da iske mutane makil suna ganina gurin ya kaure da ihun ga amarya..ga amarya ..take zuciyata tashiga tsalle tasoma harbawa da sauri sauri kenan da gaske ne aurena za'a daura.. take jikina ya sake daukar kirrma sbd hango yakub danayi cikin wando da riga da yar samanta komai na dake sanye ajikinsa fari ne ga annuri bayyane akan fuskarsa yana gyara malunlun rigarsa wani irin kyau yayi wanda bai taba yin irinsa ba . sai faman wage bakinsa yake yana murmushi yayinda take mutanen dake gurin suka shiga ihun ga ango na salema....... ga ango na salema yayinda wasu daga cikin yan dakin hjy harira suka dinga hadawa da hailbaici ango na salema ko taki ko taso kaine dai zaka kasance uban ya'yanta sannan ka mallaki wannan hadaddiyar surar jikin nata. andaura auren ne? naji wata daga cikin yar'uwarmu ta furta hkn alokacin da numfashin ke daf da daukewa ya bude baki yana murmushinsa me karamin bakinciki yace ai... tun kafin ya furta abinda zai fada wanda ni alokacin na tabbatar da abinda yake son fada kenan nasoma mgn kasa kasa narasa taufeek.....narasa taufeek kafin kace me tuni na xube kasa sumammiya.....parlour 'n ne yakarade da ihun mutane wanda ya hankaltar da sauran jama'a firfitowa daga sauran dakuna. saukar ruwa naji ajikina wanda bansa wanda ya kelaya min shi ba na farfado sai dai numfashina bai dawo daidai ba dan hk aka wuce dani hospital... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 120 · 0% Book details