← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 289

Sashe 141

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *Allah messenger saw said convey of me even only an ayah of the Quran* page 52 muryar ammi na rawa "tace dan girman allah karki ce hk. "shi irin wannan al'amarin ahankali ake bin komai domin ba'a san abinda Allah ya boye acikinsa ba. minister yayiwa AK tatasssss hk ma commission wanda jikinsa yafi na kowa yin sanyi ,hatta maman zainab labarin su'ad yayi mugun taba mata zuciya sannan ta tausayawa rayuwar yarinyar km har cikin ranta take son abdulkabir ya aureta . gabdy jama'ar dake gurin babu wanda bai sa baki ba akan umman su'ad ta janye lafazinta . sosai ammi tashiga gayawa umman su'ad Kalamai masu sanyi masu kama da nasiha wanda yasa ta gagara daga kafafunta daga inda take tsaye niyyar barin parlour 'n. yayinda shi km AK yashiga tunani akan lamarin dake faruwa yanzu dayake zaune a parlour, duk cikin lamarin babu wanda yafi daga masa hankali da neman tarwatsa masa 'kwal'kwaluwa kmr umarnin amminsa garesa . "gbdy yakasa gane abinda amminsa take nufi dashi. " tana nufin shine zai aure yarinyar datayi zaman gidan yari na tsawon shekaru 3? "sannan yar shaye shaye me tada tarzoma acikin gari ,wayasani ma ko tagama rabawa gayun gari jikinta? yayiwa kansa tmbyr can km a fili ya furta sam bazan iya aurenta ba wlh ... atare ammi da dady suka waigo zuwa inda yake zaune, dady ya zabga masa wata uwar harara "tare da cewa *sai ka aureta dole dan ubanka* kana nufin duk uwar wahalar data sha akanka zata tafi abazan ne "ko me makake nufi? AK yayi zumbur ya mike tsaye jikinsa na wani rawa yace. "dady ni zan auri su'ad? dady yace "kwarai kuwa kai zaka aureta har ma kuyi rayuwa tare . ak ya fara girgiza kansa yana tafiya da baya da baya a cikin parlour 'n, yace "haba dady wai me yasa kuke son takurawa rayuwata tunda nake ban taba jin koda digon son auren su'ad acikin raina ba amman sai kuce na aureta dole ? "nifa bazan taba iya hada soyayyar zeey da wata ya mace ba.. ammi ta fusata dan jin wadan nan miyagun kalaman da suke fitowa daga bakin AK " "kai min shiru shashashan banza wanda bai san inda yake masa ciwo ba km ka rike aranka aure tsakaninka da su'ad kmr anyi angama muddin ina raye. ak yatako ahankali har zuwa inda hjy kakarsa ke zaune ya zube gabanta ya rike kafar hjy. "pls hjy ki ceci rayuwata, zeey tana da matukar kishi a kaina. kafin hjy tace wani abu dady ya mayar da numfashi yace "taje tayi duk abinda zatayi, ai kai mijin mace hudu ne, domin ko addininmu ya halasta maka yin hk.. eiman ta amshe zance wallahi wallahi yaya ka bani mamaki, kasani jin kunya a yanzu danake tsaye acikin parlour 'n nan a iya tsawon rayuwata baka taba yin abinda naji na tsanake ba kmr yau.. "ka zauna kayi tunani da kyau idan mafarki kake yakamata ace zuwa yanzu ka farka kasan abinda kake. " wannan yarinyar ta cancaci komai agurinka wallahi ko rayuwarka tace tana so yaci ace ka cire kabata ... "yazakaji aranka yaya ace nice nake cikin halin data tsinci kanta a sanadiyarka? takarasa mgnr tana rushewa da wani kuka, wanda mgnrta bakaramin tsayawa yayi a zukatan mutanen dake gurin yayi ba. "yanzu shikenan hk rayuwarta zata kare babu sausauci kenan? "ita baga lafiyar jikinta bada samun aurenka ba. "ko alokacin da abun ya faru tafini shiga damuwa da tashin hankali ban mance komai daya faru ba alokacin wallahi su'ad masoyiyace ta hakika wanda samun irinsu zai yi matukar wuya a wannan zamani . "bari tabbatar maka da wani abu ni yar uwarkace uwa daya uba daya amman wallahi yaya bazan iya kasadar datayi akanka ba ... "pls yaya ka taimaki rayuwarta ka aureta shine kawai abinda zakayi kasaka mata da kasadar saida rayuwarta datayi. jikin ak yayi mugun sanyi da jin kalaman kanwarsa. sam ya kasa gane inda kalaman dukkaninsu ya dosa shi fa abinda ke bashi hsushi da hassalashi kenan asa shi yin abinda zuciyarsa bataso dan hk a matukar fusata AK ya bar parlour 'n zuwa part dinsa. lokacin da AK ya bar parlour, muhawara ce tashiga tsakanin yan'uwa yayinda ammi taki yarda umman su'ad ta wuce ta kasa ta tsare sai gumi ne ke tsatsafo mata agabadaya ilahirin sansar jikinta. adaidai wannan lokacin AK ya dawo parlour 'n hannunsa rike da takadar cheek ahankali yakaraso har inda su'ad ke tsaye wace tasa hakorinta tana cinzan lips dinta ahankali hawaye na gangarowa bisa kuncinta, hannunsa yasa ya kamo tafin hannuta yasanya takadar cheek din yana share mata hawayen dake bin kuncinta alokacin dayake tsaye gabanta ji yayi kmr ya rungumeta ajikinsa amman bazai iya aikata hkn ba. sautin zazzakar muryarsa ce ta doki dodon kunnenta "ahalin yanzu bana jin haushinki ko tsanarki cikin zuciyata sbd karamcinki gareni . "na yarda na amince ke din masoyiyace ta hakika kmr yadda kowa ke fada zan iya sadaukar miki da komsi nawa ban aurenki sbd shi kadai ne bazan iya yi ba ,amman ga wannan cheek din ki rike na ninka miki abinda nace zanbaki pls &pls ki bar rayuwata kije kiyi sabuwar rayuwa. ya karasa fadar hk yana me tsura mata mayattun idanunsa yana kallonta wadan da kallon cikinsu kadai ke haddasawa mutun shiga wani yanayi mara misaltuwa. cike da sanyin jiki ta dago fararen idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa masu bugar mata da zuciya a duk sanda ta kalli cikinsu gabanta na bada wani irin sauti na tashin hankali ,shima mayatattun idanunsa ya tsura mata yana kallon cikin fararen idanunta wanda zuwa yanxu sun sake canzawa sbd tsabar hawayen dake tsiyaya acikinsu ,sunyi luhu luhu dasu. yana kallonta har sanda ta dauke idanunta acikin nasa ta meida shi kan check din dake rike da hannunta. zuciyarta ke wani irin harbawa yayinda tsoro da firgice sukayiwa kirjinta dirar makiya jitake kmr ta daura hannuwanta duka bisa kanta ta kurma ihu kozata ragewa zuciyarta radadin datake ji ayanzu datake tsaye agabansa. wani irin dukan tara tara kirjinta kemata, duk wata gaba dake cikin halitar jikinta rawa takeyi, yayinda kallo daya zaka mata kagane hankalinta a matukar tashe yake hannuta 1 dake karkarwa tasa ta rike cheek din hanunta sosai tana sake duba check din daya bata amadadin 10 million din dayace zai bata a farko 20m tagani arubuce, cike da matsanancin takaicin da tashin hankali ta dago idanunta dake tsiyayar hawaye tana kallonsa kana tasoma yaga check din hannuta still tana kallon cikin kwayar idanunsa sai datayiwa check din kuci kuci sannan ta daga hannunta saman kansa tasoma tsiyaya masa piece's check din tundaga kansa yashiga bin gangar jikinsa. "ka taba zuciyata abdulkabir kaji yadda take bugawa akanka . "a duk lokacin dana yi tunanin cewa kana guduna, bugun zuciyata yana sake karuwa da karfi da karfi sai naji kmr kirjina zai tsage zuciyata ya fado kasa. "a yanzu danake gabanka tsaye zuciyata tafi ko yaushe hautsinewa da shiga tashin hankali mara iyaka. "hakika nasani nasan hk zuciyata zata kasance tunda zan rasaka a rayuwata. nasan numfashina yana daf da katsewa . abdulkabir tsawon rayuwata nayita ne cikin tunaninka da damuwa da yadda zanbi naga na malakeka hatta da gangar jikina yana tausaya min akanka, ni kaina nasan a yanzu narasaka har abada.. nan take hawayen idanunta yashiga gangarowa tashga kuka babu kaukautawa . tare da sa hannunta ta dafe daidai inda zuciyarta take bugawa. " daga yau daga rana me kmr ta yau, yau uku ga watan tara ka rubuta ka'ajiye a inda bazai goge ba su'ad tabar cikin rayuwarka bari km na har abada. "abdulkabir koda dagani sai kai zamu rage cikin duniyar nan na hakura da aurenka km a yau zan daina sonka har duniya ta nade. "ga tsiyar ka nan banaso domin 20m dinka babu abinda zasu min. " ni kaina inada kadarar data zarta 100m so mezanyi da 20m dinka? "zan tafi kmr yadda kace na fita rayuwarka naje nayi sabuwar rayuwa har sanda mutuwata zata riskeni naje na iske mahaifina.. tana gama fadar ta hk juya ahankali zuwa gurin ummanta. "muje ummana daga yau baki sake kukan bakin ciki ba domin zan dawo miki su'ad dinki ta da har abada bazan sake komawa rayuwar danayi ada ba tunda komai yarigada yazo karshe cutar farfadiya km zan roki Allah ya yaye min ita. umma najin hk ta rike hannunta gam cikin nata suka soma tafiya. da wani irin sauri ammi da minister suka sha gabansu atare "kibar min su'ad na inganta rayuwarta tare da nemo mata maganin ciwon jikinta inji cewar ammi. shi kuwa minister cewa yayi "saleema ki tsaya asan yadda za'a yi karki sake tafiya ki barmu dan girman allah karki ce zaki tafi baki san wahalar da muka akanki ba. wani irin duba umman su'ad tayi masa sanan muryarta a hassale tace "wace salema nace maka ni ba saleema bace ni rafiya sunana.. "nafa san kece saleema domin babu ta yadda za'a yi ki bace min . "haba saleema meyasa bazaki kasance me tausayi da ya fiya ba? "nace maka ba sunana saleema ba meyasa kake son kara min damuwa akan wace nake ciki? tanakarasa fadar hk tasanya kanta tare da su'ad suka fice daga gidan suna fita ammi ta sulale kasa tana wani irin kuka minister kar kabari ta wuce dan Allah minister nifa jikina yagama bani wallahi itace salimar taufeek dina... ka.. kace ta. .. take mgnr data keson yi ta makale tasoma wani irin tari idanunta na kakkafewa wanda zuwa lokacin tuni su'ad da ummanta sun bar gidan. gbdy su dady sukayo kanta suna kiran sunanta amman ina numfashinta ya dauke ashe zaune bata kare ba hankali ya sake tashi byn basu gama da wata matsalar ba ga wata ta kunno kai. da sauri minister ya nufi waje inda escort dinsa ke zaune zaman jiransa ya nufa tare da bawa daya daga cikinsu umarnin bin bayansu umman su'ad sannan ya sake dawowa parlour . kusan awa biyu ammi bata farfado ba dan har sun fara tunanin ko ta mutu ne domin babu wani gurin a jikinta dayake aiki hankalinsu ya tashi sosai dan babu wanda yayi tunanin wani hospital
Chapter 141 · 0% Book details