← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 242 OF 289

Sashe 242

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH YA FATTAH THE REMOVER OF DIFFICULTIES AND GIVER OF DECISIONS page 77 ........sun tarar da ammi da eiman sai hannutu dukkaninsu suna zaune suna cigaba hirar *bonku* ammi da eiman suka mike da sauri domin yi masa barka da zuwa har lokacin sir mahbub cikin faduwar gaba yake. ak ya nuna masa mazauni da hannunsa sannan yayi saurin fita zuwa part din dady'nsa wanda suka dawo part din ammi tare ,wanda zuwa lokacin har eiman ta d'auko abin sha ta ajiye masa akan madaidacin stood . "dady ga sir mahbub me gidana kuma abokin alkalta ,"shine me mallakin airvioce yazo domin ya gaisheku. cike da tsananin farinciki ambasodor adam yakarasa tare da mikawa sir mahbub hannu shima sir mahbub ya d'an mike kad'an daga zaune dayake yana bashi hannu suka gaisa a mutunce daga ammi har dady da wannan shi ne karon na farko daya d'aura idanunsa akan me gidan yaron nasa ,sai dai lokacin daya sanya idanunasa cikin na wanda aka kira da sir mahbub din sai daya ji kirjinsa ya amsa take kuma gabansa yashiga dokawa, a d'an tsorace dady ke kallon ammi fuskarsa cike da mamaki , ita kuma alamu tayi masa daya zauna kawai shi kansa sir mahbub sai kansa ya juya lokacin da idanunsa suka ammi kirjinsa ya tsananta dokawa wanda yasashi sunkuyar da kanshi . "idon su'ad biyu kuma ta ji motsin shigowarsu sai dai takasa yunkurawa sbd wata irin bugawa da gabanta ke yi... sir mahbub yayi gyaran murya sannan ya fara magana atsanake wanda yasa umman su'ad barin abinda takeyi ta tsaya cak tare da yin shiru tana son taji mai muryar yasake furta wata kalma , ahankali taji sautin muryarsa ta sake fitowa cikin harshen tsadadden turancinsa "ya me jiki da lafiyar baby? " nan fa ta sake kidimewa a tsaye datake jikinta yasoma rawa rawa har zuwa sanda taji ammi da dady sun hada baki gurin amsa masa " "da sauki ai taji sauki sosai sai dai abinda baza'a rasa ba ,wanda wannan me d'anbanzan kafurun taurin kan ne ke haddasawa. dady ya numfasa sannan yacigaba magana "kaga wannan yaron naka sai ka dinga hakuri dashi saboda Allah yayisa da maseefar kafurun taurin kai wanda muka rasa inda ya d'auko wannan bod'ad'en halin irin nasa ... murmushin daya zamewa sir mahbub jiki ,shi yayi alokacin batare da yace komai ba, sai duban inda ak ke zaune dayayi wanda shi kuma yayi fuska tamkar bada shi dady'n yake magana ba. ammi tayi saurin amshe zance tana duban dady "ni dai babu dole cikin lamarin nan "idan yaji bazai iya ba, ka gayawa d'anka ya sawake mata kawai Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi ,duk da ak bai cikin hankalinsa sai da kirjinsa yabada rassss yashiga dokawa da sauri ya d'ago ya dubi ammi,, tayi saurin watsa masa hararar dayasa ya dukar da 'kansa 'kasa, wannan kalmar data fito daga bakin ammi tafi gigita zuciyar su'ad akan ak, dan gabadaya wata irin razana tayi daga kwance datake ta mike tsaye zaune yayinda kasan mararta ya murda da karfi, can kuma ya cure guri daya yasoma murd'wa yana mata ciwo, ahankali ta sauko daga kan gadon dafe da kasan mararta tasoma daga kafafonta da kyar tana zagaye dakin,tana tacigaba da jiyo sautin muryar ammi "abinda kake ganin kagaji dashi shi wani yake haukan so da bulayin nema kamar zai mutu, " tunda kagaji daita sai ka sauwake mata ka huta itama ta huta da jarabarka.. "da sauri su'ad ta nufi hanyar bayi sakamakon kasan mararta daya sake murdawa tashige bayi hade da cire pent dinta da niyyar tsugunnawa idanunta ya sauka akan jini da sauri ta zabura ta mike tsaye jikinta na rawa ta runtse idanunta tana kokuwa da numfashinta kafin kace me sai ruwan hawaye sharrrrrr.....sharrrrrr yashiga gangaromata cike da matsanancin rauni ta furta "wayyo Allah ammi kinga abinda kalmarki take kokarin haifarwa ko? "ammi zaki iya rasa abinda ke cikina da kaina muddin kina furta wannan kalmar , "nashagaya miki ina son mijina ba kuma zan iya rabuwa dashi ba ,"zuciyar su'ad dinki bazata iya daukar wannan tashin hankali ba," plz ammi ki daina . ... ta dawo dakin ta zauna agefen katifa tana had'a gumi tare da ciza lip's dinta. sake gyara murya sir mahbub yayi kana yacigaba da magana cikin tsadadden turancinsa " ambasodor da ammi hakuri zakuyi , dan kalmar da zan iya muku amfani daita kenan. " dan girman Allah kuyi hakuri da abdul ,ni kaina danaji abubuwan dake faruwa dashi na dade ina mamaki, kuyi masa hakuri bisa ga abubuwan da suka faru" ammi ki yafe masa kasancewarki mahaifiya gareshi ,duk da nasan cewa akwai zafi da radadin abinda yayiwa diyarki ,bisa banzatar da lamuranta dayayi, nima naji irin zafin da kukaji araina, domin na dauki su'adullahi matsayin diyata , kamar yadda na dauki abdul ,"ki kiyi hkr ki janye, zance neman saki daga gareshi dan bazanso yayi hasarar mata kamarta ba,itama bazan so tarasa miji kamar abdul ba. "d'anku abdulkabir jajirtacce namji ne me kima da dattako daraja a idanun duniya wanda samun kamar sa ke da matukar wuya a wannan lokacin. "wallahi nasan abdul dayana cikin natsuwarsa abubuwan da amininsa yagaya min yana aikawa bazaiyi ba.....dan haka kutaru har ita yarinyar kuyi hakuri sannan zan nemi alfarma abashi matarsa yanzu ya wuce daita gidansa, yakarasa mgnr yana lumshe kyakkyawan idanunsa tare da saukesu akan ammi da lokaci daya taji zuciyarta ta gigita. shima zuciyarsa taji abinda ammi taji dan haka ya sake sunkuyar da kanshi kasa yana kad'a kafafunsa. "tunda sir mahbub yasoma magana dady yayi mutuwar zaune agurin, yashiga kallon kallo tsakanin ammi da sir mahbub har sanda yadasa aya, anya babu abinda ke faruwa kuwa ya furtawa hakan ? "muryar can kasa kasa ammi tayi masa rad'a "babu abinda ke faruwa ba kuma wanda kake tunani bane, kama ce kawai... shi dai jinta kawai yayi amman ya rantse da mahaliccinsa wannan mutumin dan'uwan matarsa ne wato *TAUFEEK ABUBAKAR TAFIDA GULUNBE* shine zaune agabansa ba wani mutun daban ba, ko wata kama ba, komai nasu iri daya ne ,yanayin sarrafa harshen maganarsa murmushinsa kallonsa , yaren dayake magana dashi ne kawai ya bambantasu wato harshen turanci,wanda asanin dayayi masa babu wata kalar turancin da harshen taufeek bazai iya sarrafawata ba ... "kusan minti goma salema na tsaye ta kasa aiwatar da abinda take sannan ta kasa motsawa daga inda take tsaye. tana tariyo murya da take jin fitowarta daga parlour tana zuwa mata cikin dodon kunneta," tabbas wannan muryar babu tantama muryar wanda tasani ne "wannan muryar bazata ta'ba 'bace mata ba duk iya tsawon shekarun dazayi batare da tajita ba," wannan muryar tana da bambamci da sauran muryayoyi da bazata ta'ba mantata a iya tsawon arayuwarta ba, daga inda take tsaye takasa motsawa tayi mutuwar tsaye cikin tsananin tashin hankali da matsanancin gigita sai dai rawar da jikinta keyi ya sanya tayi saurin durkushewa agurin domin kafafunta sun tabbatar mata da bazasu iya cigaba Da d'aukar gangar jikinta ba, baya ga haka ga wani irin jiri dake neman jefar daita 'kasa wata irin bugawa kanta yasoma yi da karfi tamkar zai rabe gida biyu da kyar ta iya samun natsuwar zuciya soma karanto addua cikin ranta sakamakon zuciyarta data shiga aika mata sako , "ta yaya muryar datake tinani itace ,zatakasance agidan nan amman ahlin gidan su gagara sanar mata ? ",bugu da kari nata me muryar ya dade da mutuwa, mutuwar da idan anyita ba'a dawowa , watakilla muryar bakonce tayi irin wace tasani ,ta karfafawa zuciyar da haka ,sannan ta yunkura da kyar takarasa dama moli ta kunna gas ta d'aura tukunyar a saman gas tacigaba da tsayuwa jikinta still na kirrma .. tautaunawa ce tacigaba da wanzuwa tsakaninsu yayinda har lokacin ambasodor yakasa yarda da sir mahbub bashine taufeek ba . shi kuwa sir mahbub hakuri yabawa ammi sosai kafin ta yarda su'ad zata koma sai dai ba a wannan lokacin daya bukata ba sai zuwa gobe. su'ad kuwa komawa tayi kwanciya tana lumshe idanunta jin abar zance saki an shiga wata hirar daban . har bakin get din gidan dady da ak har ma da ammi suka rako sir mahbub,inda dady ya dinga d'auko masa zance abubuwan da suka gabata a can baya yana kawo masa domin son tabbatar zarginsa shi ne koko da gaske waninsa me kama dashi kamar yadda matarsa ta tabbar masa, amman babu wani karin haske da dady yasamu haka ya hakura sir mahbub yashige motarsa direbansa yaja suka bar gurin . bangaren umman su'ad kasa samun natsuwar zuciya tayi a game muryar dataji dan har ta koma gida zuciyarta bata barta ta huta da tinani muryar dataji yau abubuwa ne suka shiga wayo cikin 'kwal'kwaluwar a game da muryar da mamallakinta. daren ranar dai sai da su'ad ta dangana da ganin doctor dan ta canza pent yafi sau 5 kuma duk sanda zata duba sai taga jini dan haka ta sanarwa ammi, cikin tashin hankali suka tafi asibiti,byn doctor ya dubata tare da bata taimako " yace damuwa ce me tattare da faduwar gaba wanda idan bata yi kokarin cireta ba zata iya rasa cikin jikinta. kwananta biyu suka dawo aka soma shirin kaita gidan AK ammi da kanta takira ak akan ya gyara inda su'ad zata zauna "yace mata yaji, zeey bata gida yakira ma'aikatan dake tsaftace mahali, suka gyara mata daya daga cikin flat din 'kasa dake bangaren dama, har aka gama zeey batasani ba sannan bai gaya mata zance tarewar su'ad ba, kwasam tana zaune parlour'n taji hayaniyar shigowarsu ammi , a firgice ta tashi tsaye tashiga kallonsu daya bayan daya kafin daga baya tayi saurin durkushewa kasa tana gaida ammi "dakatar daita ammi tayi da hannuta sannan tace "rike gaisuwar Zainab banaso bana bukatar gaisuwarki .jiki a sanyaye ta Nike tana tsotsa jikinta dan tasha jinin jikinta akan yadda ammi tayi mata, inda alokacin ammi takira ak take tmbayarsa dakin da yace ya gyara, ya gaya mata yana me saukowa, kai tsaye ammi ta nufi dakin ta bude tana bawa william's umarni shigo mata da akwatinan kayan su'ad nan fa hankalin zeey ya tashi daidai lokacin AK ya sauko cikin d'ari d'ari zeey naganinsa ta takaraso gareshi
Chapter 242 · 0% Book details