Sashe 227
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tafin hannun zeey cikin nasa ya zauna gefenta yana mata magana kasa kasa ta yadda babu me jin abinda yake cewa sai ita kadai. "Kiyi hakuri kinji my zeey kiyi yafemin nayi nadamar abinda na aikata miki kibani damar na gyara kuskurena . Ahankali itama tayi mgana "abdul takira sunansa ya amsa da" ina jinki my zeey. "Bakayi nadama ba tunda har yanzu banganka durkushe agabana ba . "Dan wannan ai me sauki ne wallahi zan durkusa har birgima idan kina so zanyi miki nifa yanzu ko cewa kikayi na rabu da kowa akanki zanyi ,ya Mike tsaye hannunsa cikin nata yana murzawa daidai lokacin da su'ad takaraso dan ita taji duk abinda suke tautaunawa kasancewar gbdy hankalinta na garesu sabanin jama'ar parlour'n da hankalinsu ya tafi akan tautaunawa . Ak yasoma kokarin zai durkusa su'ad ta katse masa hanzari ta hanyar raba tsakaninsu ya Mike tsaye tare da dagowa yana dubanta ta kai hannunta garesa ta dafa kadarsa wannan Karon taji wani irin zirrrrrrrr tundaga kanta har zuwa babban d'an yatsanta ga wani irin kallo dayake jifanta dashi wanda ke bugar mata da zuciya amman haka ta daure tace "bazan taba yarda ka durkusa mata ba Abdul in har sai ka durkusa mata sai dai karta koma gidanka . "Abdul ka dubi cikin idanuna nice su'ad din da kayiwa alkawarirruka dayawa arayuwa tare da alkwarin zaka rikeni amana gashi tun ba'aje koina ba kana neman juya min baya dan Allah mijina ka dawo cikin tinaninka bancancaci irin wannan tsanar daga gareka ba . dayarasa yasa abinda yakama yayi kawai yashiga yaryarfa mata mari tare da ingizata tayi baya taga taga zata fadi sannan ta tsaya yakarso har inda take tsaye tana dubansa ya rufeta da duka ta saki wata uwar razananniyar kara wanda ya hankalta da ammi a haukace ta mike tayi kansa bata tsaya wata wata ba ta kafa masa hakori "sakita dan ubanka zaka kashe min ita ne ? "da me kake son taji da wananan maseefar ko kuma da wulakanci daka tsiro mata dashi yana dukan su'ad ammi na dukansa da cizo da yakushi dady da maman zeey suka yakarso atare banda hjy dake zaune dan ita dadin dukan da ak yayiwa su'ad taji haba ina dalili wannan jaraba ta fada aranta da kyar dady ya amshi su'ad ahannun ak . ammi ta rungumeta ajikinta tana kuka ganin har kamanin fuskarta ta sauya "abdul baka da imani abdul baka da tausayi kasamu yar mutane kana duka haka kamar kasamu jakar ubanka ,wallahi sai Allah yasakamata , ta sake rungume su'ad ajikinta tana kuka tana shafa bayanta ,"yi shiru mamana sai Allah yasaka miki matsawar akwai zalinci acikin wannan lamarin ,bakida kowa kuma baki dogara da kowa sai Allah km shi zai tsaya miki yabi miki hakin zalintarki da'akayi . "kai kuma idan namaka baki sai yabika, wallahi kaji na rantse akan su'ad zan iya 'batawa da kowa ciki har da mahaifinka dan haka idan ma akwai abinda ke cikin 'kwal'kwartaka ka ciresa tun wuri tun raina baiga karasa baci ba takarasa maganar tana duban fusakar su'ad mamana , "Ki masa Allah ya isa ko kiyi karasa gurin Allah akan tozarcin da yayi miki ... take Su'ad tashiga girgiza mata kai alamun baxata iya abinda tasata ba . "Ni saki nace ki gayawa Allah ta hanyar kai karasa gareshi ,ki kalli sama ki gayawa Allah, Allah na amsar adduar wanda aka zalinta shi kadai ne zai saka miki . a fusace ak ya duban ammi kafin daga baya yace "Wai meye haka ne ammi ? "Me kike kokarin yi ? "Ubanka nake kokarin yi mara imani wallahi yau ace ni ba uwa bace sai na maka mummunar addua akan wannan wulakanci daka mata, amman akwai Allah kuma zamu gaya masa zamu kai kukanmu gareshi .. Ya furzar da iska ta bakinsa me zafi yana duban su'ad dake kwance ajikin ammi tana numfashi sama sama. a fusace ak ya nunata da yatsansa "kika sake yunkurin hanani abinda nayi niyya abakacin aurena dake............. zuuuuuuuuuu su'ad ta zame ajikin ammi tashiga fixgo numfashi da kyar tana fitarwa ammi tabita ta rungumota jikinta tana kiran sunanta idan ka saketa mutuwa zatayi bazata ta mutu saima tasamu wanda yafika ta aura shasha wanda bai san ciwon kansa ba . Shi kuwa ak juyawa yayi ya nufi gurin zeey ya durkusa har kasa bisa gwiwowinsa yashiga rokonta yana bata hakuri wannan al'amarin ya tabbatarwa su'ad tabbas zainab tayi wani abu akan mijinta sbd mijinta ba lusarin namijj bane mijinta ba irin nmj dazai durkusuwa mace bane, mijinta ba mijin tace ba tsayayyen namiji ne wanda baya daukar iskanci sai gashi yau ana fama dashi akan abinda tasan inda yana cikin hankalinsa bazai taba aikatawa ba . "wannan abu ya gigitata ya girgiza zuciyrta wanda take taji numfashinta yasoma kokarin barin gangar jikinta ammi bata ankara ba tana can ga zagin ak " taji numfashinta ya fara tsarkewa tmkr me shakuwa ,can km ta hau tari ba 'kau'kautawa lokaci daya ta hau aman jini jikinta ya soma sakewa take numfashinta ya tsaya cak kmr ance ammi ta meida idanunta kanta taga jini nan fa hankalinta ya tashi tashiga jijigata shiru aiko ta saki ihu. "shikenan Abdul kayi nasarar kashe min ita wallahi idan su'ad ta mutu kaima kasan dasanin mutuwa zakayi dan wallahi bazan barka araye ba, da hannuna zan kasheka kowa ya huta tana kuka soma kokarin daukarta dady yakarso agigice ya amsheta daga hannun yana kallonta tabbas bata numfashi . "ta mutu ko inji cewar ammi? "haba baraka ki natsu mana bata mutu ba, shi dai dady bashi da tabbas din ta mutu ne ko tana raye ,shi dai ya fadi haka ne dan kawai ya kwantar mata da hankali. wannan al'amari yasa jikin ak yayi magu mugun sanyi ,take zuciyarsa tashiga bugawa da karfi karfi ya juyo cike da mutuwar jiki zai isa garesu zeey tayi saurin kamo tafin hannunsa cikin nata "my life ina kuma zaka? ya tsotsa keyarsa domin rasa abinda zai ce mata suna tsaye suna kallo dady yayi hanyar waje da su'ad ammi tabi bayansa tana kuka mama ce tayi karfin halin binsu hjy kam ko ajikinta . zeey ta d'an saci kallonsa taga kamar reaction dinsa ya canza muryarta a sarke tace "sai naga kamar hankalinka ya tashi ko zaka busu ne? ya girgiza mata kai ala'mun aa " yauwa ka rabudasu kawai su karata yanxu kaje kasan yadda za'ayi a meida aurenmu . "ok ok my zeey duk abinda kika ce shi za'a yi. shine zance inji cewar hjy, zeey tayi murmushin jin dadi tare da cewa "da ala'mun fa hjy kema bakiyi da wannan yariya. "ko daya zainab amman kinsa so sone amman sonkai yafi bakiga itama baraka goyon bayan diyar dan'uwanta takeyi ba . nan suka zauna sukayita zagin mami agaban AK amman ko ajikinsa asalima ji yayi kansa na jujjuyawa dan haka ya zame ya kwanta flat tare da d'aura hannusa ya dafe goshinsa dayan hannunsa kuma ya d'aura saman ruwan cikinsa. Kai tsaye mota aka nufa da su'ad. general hospital din dake kusa dasu suka nufa daita . suna parking a harbar hospital ammi ta fito aguje tayi cikin hospital tana dictor wani matashin likita tacikaro dashi tashiga karo masa bayanin matsalar da suke ciki "ku taimaka min zata mutu yarinyar tace zata mutu aman jini take.. take doctor saifullahi wanda mutane suka saninsa da dr saif yabada umarni turo gadon marasa lfy aka daurata aka nufi dakin doctor daita likitoci suka soma aiki akanta da kyar likitoci suka samu aman jinin ya tsaya numfashinta ya dawo daidai kowa yafita aka bar doctor saif shi kadai yana kallon kyakkyawar fuskarta me d'auke da annurin kyau gsky yarinyar nan tashiga ransa matuka wani abu ya dinga ji akanta har tsakiyar kansa haka kawai tunda d'aura idanunsa akanta yaji zuciyarsa ta amsa ya dade zaune yana kallonnta kafin daga bisani ya fita. ammi da dady zaune a office din Doctor saif yana musu bayani a game da rashin lafiyar su'ad "damuwa ce ta haifar mata da buguwar zuciya wanda ya haddasawa jinita hawa sosai fiyye da yadda ake bukata ,yakamata a dinga kiyaye bacin ranta idan ba haka za'a iya rasata zata tashi amman sai zuwa la'asar godiya suka masa suka fito zuwa dakin da aka kwantar da su'ad . ammi taci kuka sosai har ta godewa Allah gabadaya ta zabge alokaci daya tayi wata irin rama, sako ta tura umman su'ad tazo suna asibiti da su'ad, tura sakon baifi da minti goma ba sai gata ta iso ammi bata boye mata komai ba domin ta taya diyarta da addua . muryarta a sanyaye umman su'ad tace "yanzu wani hali take ciki? "likita yace sai zuwa la'asar zata farfado, shiru tayi tare da karasawa jikin gadon ta dubata, yaushe rabon data d'aura idanunta akan diyarta mafi soyuwa cikin ranta. kusan minti goma ta dauka tsaye akanta tana kallonta har yanzu kamaninta da mahaifinta na nan, abubuwan data nata basu dayawa tana maseefar kaunar fiyye da kaunar data nuna wa mahaifinta bata kaunar ganinta cikin tashin hankali ta gwamaci maseefa ta fad'a mata akan diyarta kuka ne ya subuce mata aiko tashiga rare kuka abubuwa dayawa suka shiga dawo mata batasan yaushe ne zasu samu hutun rayuwa ita da diyarta, duk fa wannan maseefar dake bibiyarsu itace silar komai datayi hakuri bata biyewa sharrin soyayya ba yanxu tana tare da dangita cikin gatatan . ammi takaraso ta dafa kafadarta tace "dan Allah salema kibar kuka haka kiyi mata addua samun lafiya jinki. la'asar har ta wuce amman su'ad bata farfado ba doctor saif ya sake shigowa dakin lokacin ammi kadai ce umman su'ad taje gida ta dawo ,ammi nagani shigowarsa tace" yauwa likita tunda kashigo bari naje nayi sallah kafin kagama dubata. "badamuwa kawai yace kasancewarsa shi mutun ne miskili bai fiyye son hayaniya ba. ya koma ya jingina bynsa da bango daki ya tsura mata idanunsa yana kallonta yana jin wani irin sanyi dadi ajikinsa burinsa a halin yanzu ya mallaketa matsayin matar aurensa, hannuwansa duka ya rungume akirjisa yana cigaba da dubanta . fitar ammi da minti biyu ta fara motsi har ta farfado sai dai ta farka ne cikin matukar razana nan ta hau kuka tana cewa ...abdulkabir karka min haka