Sashe 149
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koina ba. murmushin takaici yayi yana me cizan gefen lip's dinsa da karfi sannan ya lumshe mayattun idanunsa tare da cewa haba ammi wai meyasa gbdy yanzu kika canzamin ne? "halinka ne yaja hk ammi tabashi amsa atakaice tana sake meida hankalinta kan su'ad . " to ai na canza na dawo yadda kike so "Allah yasa ai nafi kowa bukatar naga ka canza . sai da ta numfasa ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "wai da gske ne zance danaji zeey tazo min dashi kabata kyauta motar da aka turo maka daga spain? ya girgiza kanshi ala'mun eh tare bude idanunsa ya tsurawa zara zaran yatsun kafafunsa ido yana kallonsu, "to ina na su'ad? "wace hk km ammi. "abdulkabir kashiga hankalinka dani ,wlh kafita idona fa idan ba kana bukatar rainka yabaci ba . " wace irin banza tmby ce wannan? " matar datake shirin zama mallakinka kake cewa wace hk? ganin yadda ammi tashiga balbaleshi da fada da masifa yasa su'ad saurin mikewa jikinta a matukar sanyaye zuciyar na harbawa ta nufi bathroom ba dan akwai abinda zakiyi aciki ba tayi hk ne kawai dan ta gujewa zuciyarta bacin rai . "kiyi hkr ammi amman dan Allah na rokeki ki daina min fada agaban yarinyar nan zata rainani ni km kinsa ba daukar raini zanyi ba dan zan iya karya yarinya wallahi . "idan ka fasa karyarta ban gode maka ba, km wallahi naga tata motar acikin gidan nan kafin ka hadu da fushina , runtse mayatattun idanunsa ya sake yi sosai tare da gyara zamansa ya kamo hannuwan ammi cikin nasa ,"kiyi hkr amminah banason ganin bacin ranki ,tunda kika furta akawo mata tata motar angama ai duk abinda kikace kina so shi zanyi . ta jinjina kai tare da cewa " sauran zance inda zata zauna shima naji kamin shiru sbd kayan daki tunda ita zainab nata sun dade acan gidan ka. shiru yayi na dan wani lokaci daga bisani muryarsa a kasalance yasoma motsa labbansa ahankali "me zai hana ta zauna a part dina na nan gidan ,sbd can gidan mutun daya ne . "kace dai baka son hadasu guri daya wannan tsarin naka ya daidai agurina gara zamanta kusadani , idan ba'a kwatanta adalci ba a hadu da bacin raina. shi dai duk abinda tace da eh ko a'a yake binta dan su rabu lfy dan yaga yanzu gbdy ammi ta maseefar sauya masa akan su'ad, da yayi mgn zata sauya masa . ahankali ya mike tsaye yana dubanta "ni zai wuce gida addur a sauka lfy tayi masa. ******** ammi takira commission akan zancesu ore "yace mata ai tun shekarajiya yasa aka sakesu godiya tayi masa sosai sbd yana matukar yimasu karamci da mutunci ,dan byn shi da yanzu su'ad na gurin police kasancewar tana da sanya hannu dumu dumu gurin bada gudumuwar yiwa onye fayde. ********* a yammacin yau ne ore taki kira su'ad inda take sanar mata zasu shigo gurinta zuwa anjima, tayi murna sosai da jin zasu kawo mata ziyara, duk da tarin damuwar datake ciki hkn bai hana wannan farincikin tasiri afuskata ba. taje da murnarta ta sanarwa ammi xuwan su ore sbd abinda zaije ya koma . ammi kanta bataji dadin wannan zuwan nasu ba ,dan tafi son kowa yakamata gabansa amman yadda taga su'ad din cikin tsantsar farinciki maramisaltuwa yasa tace mata babu matsala Allah ya kawosu lafiya bari zan yiwa hannutu mgn asa abinci dare dasu. da misalin karfe 7:00 daidai suka karaso gidan kusan su goma har da ganiya lokacin da suka iso bakin get din gidan securities din bakin get suka hanasu shigowa sai da suka kira wayar su'ad ita km ta gayawa ammi. eiman ammi ta tura tashigo dasu kai tsaye falon baki ta nufa dasu ita km juya. kafin su'ad takaraso har abinci da abin sha sun karaso kalolin abinci birjiki agabansu tare da kayan marmari, cike da natsuwa su'ad tasanyo kanta cikin parlour 'n suna ganinta suka mike tsaye suna ihu da kururuwa ganinta ol'orin o'won agba, gba tiya suka shiga bawa juna hannu suna tafawa daga bisa suka rungume juna da matan . ganinsu ore bakaramin sake faranta rain su'ad yayi ba kasancewar tagansu suma cikin natsuwa da kwanciyar hankali kmr yadda itama yanzu tasamu natsuwar zuciya ,kowanensu cikin shiga ta mutunci duk da shigar kananun kaya ne amman yafi na da da suke sakawa wanda alokacin sau tari gajeren wando ne iya gwiwa sai banzayen riguna na yan iska. yadda shigar matan take a mutunce hk ma maxan shigar take. sun ci abinci sunyi nak sai hirar yaushe gamo suke atsakaninsu suna kwashewa da dry inda ganiya da ore suke tmbyrta cigaban da aka samu a tsakaninta da AK. uhm numfashi da ajiyar zuciya su'ad ta sauke atare , take km yanayinta ya sauya sannan muryarta a sanyaye tace "babu wani sauyi jiya iya yau muna nan kmr yadda kuka sani, sannan ta kara da basu labarina halakar dake tsakaninta da AK dukkaninsu sun sha mamaki da jin hk . inda baba laye yace "ki bari zan yiwa wani mutumi mgn a unguwarsu,malami ne sosai ko zai taimaka miki ki mallakeshi. a matukar zabura su'ad ta zaro fararen idanunta waje tana dubansa kafin daga bisani tasoma girgiza masa kai "karka soma baba laye ,ai ni arayuwa na dauki darasi iri iri "bari ingaya maka malami kona addinin muslinci ne bazan sake kai kaina gareshi da sunan taimako ba, matsawar sai na kaiwa wani malami ziyara sai dai kar na mallake abdulkabir arayuwata. " wlh gara muyita zama hk nidashi zan cigaba da kaiwa allah kukana Allah yasan yadda zaiyi da lamarina, amman zance zuwa gurin wani malami sam karma ka sake kawo min zance shi. su ore suka hada baki gurin cewa kina da gsky wlh yaushe zaki tsaya ki karar da arayuwarki akan nmj, ni da zakiji shawarata wallahi da rabuwa kikayi dashi akwai maza dayawa a office inji cewar ore. "gaki da kalar yan birni one time kina rabuwa dashi zaki samu wanda yafishi . murmshi su'ad tayi kana tace "akwai matsala ne idan na rabu dashi , nan subar hirar AK suka shiga wata basu suka bar parlour 'n ba sai gurin takwas na dare . sannan dukkaninsu suka mike domin tafiya gida. su'ad na tsakiyarsu suna cigaba da hira kasa kasa har zuwa farfajiyar gidan inda suka ja birki suka tsaya suna sake cigaba da hira . shigowar hancin motar Ak dake kokarin sanyo kai cikin gidan shi yasa gaban su'ad bada wani irin rassssss sannan kirjinta ya amsa yasoma wani irin mahaukacin bugu da karfi ,take su ore suka sha jinin jikinsu gani yadda su'ad ta shiga tashin hankali da rudanin ganin motar data shigo yanzu wanda basu san ko motar waye ba. kai tsaye inda ya saba parking din motarsa ya nufa ya faka Batare daya fito daga cikin motar ba yayinda dukkaninsu hirarsu ta tsaya cak suka dawo yanayin su'ad. kusan minti goma yayi zaune cikin motar sannan ya bude murfin motar yasoma ziro kafafunsa masu matukar kyau da taushi waje daga bisani gangar jikinsa ya biyo baya ,ya fito gbdy daga cikin motar sanye cikin wasu haddaun riga da wando, rigar dake sanye ajikinsa fara ce sol me ratsin baki ajikita da wando baki kafafunsa sanye cikin canvers baki da da fari kanshi babu hula sai agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa duk da dare ne amman farfarjiyar gidan ta wadatu da hasken wutar lantarki hkn ne ya yabawa su'ad damar kare masa kallon tsab daga inda take tsaye shi km yana jikin motarsa tare Kokarin dannan key din dake rike a hannunsa. ahankali ya juyo da niyyar soma tafiya abinda yagani ne yasa kasa cigaba da daga kafafunsa dan hk ya tsaya cak tare da tsura mata mayatattun idanunsa yana kare mata kallo daga inda yake . sanye take cikin wasu haddaun wando da rigar body hook me maseefar kyau wace tayi mugun kama mata jiki sai wandon pencin jean shima ya matse Hip's dinta sosai wanda hkn ya fito da shep din halitar jikinta ta rufe kanta da hular sanyi tare da rungume hannuwanta duka akirji wanda hkn yasa ya kasa gane yanayin halin da dukiyar fulaninta suke ciki ,tayi wani irin azababben kyau na daukar hankali . ganinta tare tsinannun gang dinta yasa yaji ransa yayi mugu mugun baci yji wani irin masifafen kafirarran kishi ya caki kahon zuciyarsa yana neman barazana da rayuwarsa take yashiga antayo musu mugun kallo me hade da harara wanda yasa hantar cikin su'ad kadawa jikinta ya dauki rawa ,gbdy tsoro da firgici suka farmaki zuciyata tana kallonsa yasoma daga kafafunsa ahankali yana tafiya cike jin shi wani ne yayinda ita km bugun zuciyarta ya tsananta . duk daga kafafunsa daidai yake da bugun zuciyarta amman ta daure ta cije ganin wannan tsoron bai yi tasiri ajikinta ba ,. yana gama karasowa gurin tasoma hawayen xuci sbd tasan me zai iya faruwa alokacin, yanayin fuskarsa yagama bayana tsantsar rashin mutunci da zaiyi, ita kadai tasan yadda take ji cikin zuciyarta a halin datake tsaye a gurin jiyatayi kmr ta gudu ta barsu ore amman wani bangare na zuciyarta ya karfafa mata gwiwar tsaya wa. har ya kawo daidai inda suke tsaye cirkocirko cike da matsanancin tsoro kawai taga ya dauke kanshi akansu ya wucerwasa batare daya sake kallon inda suke ba . hanunta tasa ta goge gumin dataji yashiga tsatsafo mata a fuskarta wanda tsoro da firgici yasa ta kasa gogewa tare da sakin naunauyen ajiyar zuciya tashiga Allah Allah su bar gidan. basu wuce ba har AK ya fito ya wucesu a inda ya barsu tsaye yashiga motarsa ya figa da gudu bar gidan sai wuraren goma da rabi suka bar gidan. washegari hk yazo tara dasu sun cika farfajiyar gidan da hayaniyarsu ya wuce still kmr jiya batare da yace musu komai ita kanta su'ad bata bi ta kansa ba. rana ta uku AK ya sake zuwa gidan ya iske su baba laye da wasu maza su uku tsaye tare da su'ad ,nan fa ya kasa hakurin ganinsu kai tsaye ya nufo gurinta yana mazurai yadda taga yanayinsa yasa gabanta ya fara faduwa da sauri sauru "har gabanta yakaraso ya tsaya kyam yana kare mata kallo batare daya kalli inda su