Sashe 228
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka dawo gareni ban cancaci wannan wulakancin daga gareka ba idan kabarni mutuwa zanyi ,kadawo ka dawo gareni dan Allah kayi min alqawari zaka rayu dani babu cin amanar soyayya tsakaninmu. bance karka dawo da zeey ba amman kajidani kabani kulawa ina sonka dayawa bazan iya rayuwa babu kai ka koyardani soyayyarka fiyye da lokacin dana tsinci kaina cikin saukinka . take gaban doctor saif yabada rasssss yashiga faduwa, Tari ne ya tsarketa sai km tashiga aman jini daidai lokacin da doctor saif yakaraso gareta cikin sauri yashiga bata taimakon gaugauwa da kyar aman ya tsaya yayi mata allurar bacci wanda a kalla zata kai har zuwa washegari tana bacci . koda yakoma gida kasa zaune yayi ya kai gwaro ya kai mari acikin tafkaken dakinsa ya dade yana tinani akan sambatun da yarinya ta dingayi , wanda hakan ke nuni da tana cikin shauki soyayya ne da wani har ya kaita ga kwanciya .to idan haka ne meyakamata shi yayi? "shi dai gasky yana sonta idan ya rasa zai iya mutuwa da kyar bacci barawo yasamu nasarar daukasa amman har lokacin jikinsa bai bar tsuma ba akan yarinyar da bai san kowacece ba... washrgari har gurin la'asar bata farka daga bacci ba , doctor saif dake kula daita ya tashi aiki amman sam ya kasa tafiya ya barta sai dai yana office dinsa zaune tinaninta yana fixgarsa byn kmr mint talati ya sake shigowa dakin da take kwance har lokacin bacci take ya gaida ammi da mahaifiyar su'ad cikin girmamawa dan duk yadda akayi su din jininta kodaga yanayin yadda yarinyar ke din ban kamani dasu. sai lokacin ammi tasamu damar tmbyrsa abinda yasa su'ad yin bata farka ba kamar yadda yace "ta farka wani allura na sake yi mata sbd damuwa tayi mata yawa tana bukatar hutu sosai idan ba'a dauki matakin daya dace komai zai iya faruwa daita ammi ta jinjina kai ita kuwa umman su'ad tagumi tayi tana yiwa diyarta adduar samun sauki doctor yacigaba da magana "amman ina ga zarar ta farka komai zaizo da sauki. atare ammi da umman su'ad suka amsa "allah yasa karasawa yayi gadon da su'ad ke kwance tmkr matacciya ya dubata ruwan dake daure da hannuta ma ya kusan karewa ya zubawa fuskarta ido take gabansa yashiga faduwa aransa yace "Allah yayi halitta kyau anan . tunda yake bai taba cin karo da fuskar data tsaya masa azuciya ba kmr fuskar dayake kallo yanzu agabansa . ya dan tsaya yana jiran ruwan yakarasa karewa ya zare mata gbdy sannan ya wuce kusan minti goma ya kai tsaye sannan ya kai hannunsa da niyar zare abun ruwan yaji wani irin zirrrrrrr ajikinsa tundaga taf karfarsa abinda yaji yashiga yawo ajikinsa da sauri yakarasa cirewa ya yi musu sallama ya fita . Kwananta uku kwance ba tasan a wani halin take ciki ba, ammi da mahaifiyarta da eiman ke faman dawainiyya daita wanda zuwa lokacin duk wanda yaganta sai ya xubar mata da hawayen tausayi ,ta zabge ta rame tayi fari sosai ta d'ashe . ta farka a bacci datake taga mahaifiyarta zaune agabanta ta dukar da kanta jikin karfen gadon ahankali takai hannunta ta daura bisa kanta tana furta "ummana ...... da sauri mahaifiyarta ta dago idanunta cike da ruwan hawaye dan ba bacci take ba tunanin duniya kawai ne ya addabi rayuwarta. mikewa tayi cikin sauri zata fita su'ad ta riko hannuta cikin nata "ina zaki tafi kibarni? "Zanje na kirawo doctor ne yace idan kin tashi azo akirasa, ta runtse idanunta gam tana me zame hannunta . Tare umman su'ad suka dawo da doctor har ammi dataje siyan magani suka shiga jero mata sannu bata amsa ba sai idanuwa data dinga binsu dashi, shi km likita yashiga aikinsa tare da duba lafiyar bp dinta daya hau sosai sannan yayi mata allura yaso ya tsaya amman ya kasa hakan adalilin tsayuwarsa zata iya fallasa sirrin dake boye a zuciyarsa dan kallonta na ta'ba masa zuciyarsa duk sanda yakusanci indatake yana jin wani iri ajikinsa gashi bai sani ba ko matar aure ce ko budurwa shi dai fatansa takasance budurwa ce jikinsa a sanyaye ya fita . byn fitar likita ta bude bakinta da kyar takira sunan ammi "Ammi ina Abdul dina ? "Bai xo ya dubani ba ko ? Ammi ta sake matsowa sosai ta rike hannuta cike da tsigar rarrashi tasoma magana "kiyi hakuri mamana da wannan iftilain daya samemu amman abinda nake so dake ki cire zance abdul azuciyarki har ki samu lafiya. Zare hannuta tayi cikin na ammi tare da kawar da fuskarta gefe tana kallon bangon daki hawaye na gangarowa akan pillow da kanta ke kwance . Ta yaya ammi zatace taciresa cikin xuciyarta alhalin tasan hakan ba abu ne me yiwu ba a gareta . yadda bazata iya cire numfashinta daga gangar jikinta ba haka bazata iya cire abdulkabir cikin xuciyarta dama rayuwarta gbdy , tasan lokacin mutuwar ce tayi kusa tunda tarasa abdul arayuwarta. ahankali tashiga kuka sosai dan ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta akan mijinta ummantace takaraso daidai kanta su'ad yanzu ba lokacin kuka bane, ba kuka zakiyi Ba abinda ya faru yaridaga ya faru ta lafityarki zakiyi Allah kiyaye gaba. duk da maganar da mahaifiyarta keyi yana shiga cikin kunnenta amman ko gezo batayi ba kuka take sosai har da shesheka.., idanunta ya sauka akan zoben silver dake makale da yatsan hannunta take tinanin abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu zuwa koria har zuwa sanda ya saceta batareda saninta ba ,da yadda ya dinga bata kulawar ta hanyar tsumata da tsumammiyar soyayyarsa me tsayawa arai ,ta tuna wani yammanci ana sauran kwana uku da faruwar komai garesu, ya sata ta tsuke cikin wasu hadaddun kananan kaya tayi rolling kanta da bakin mayafi shima kusan irin shigar jikinta yayi sunyi kyau sosai ya dauketa zuwa wani hadadden shopping mall dake spain ahankali suka jera hannunsu cikin juna ,da kansa ya dinga daukar mata abubuwan amafaninta batare daya d'aukarwa kansa komai ba ,ita km ganin haka yasa ta daukar masa wani zoben silver me shegen kyau me d'auke da harafin sunanta *S* ta kamo tsinsiyar hannusa tana kallon cikin kwayar idanunsa ta saka masa tare da kissing din hannu atake ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yayi kissing din goshinta yana jin dadin wannan kyautar tayi masa cikin kunnenta ya rada mata" dole nabada tukuicin wannan kyautar idan muje gida. tayi murmushi tana dukan kirjinsa tare da cewa "Allah banason wannan tukuicin. ya sake janyota jikinsa sosai shima ya d'auki zobe irin wanda tasaka masa, me harafin sunansa *A* ya saka mata yayi kising din hannuta har da kari dan sai da yayi kissing din lip's dinta sannan yajanyo hannuta suka sake jerowa hannunsu makale cikin juna ya zagayo ya bude mata kofar mota ita km ta tsaya rungume da hannuwanta duka akirji tana dubansa tana murmushi cike da jikin dadi . da hannusa yayi mata ala'mun tashiga ta koma ta tsaya bakin kofar motar taki shiga sai ma ta tsaya tacigaba da kallonsa cike da matsanancin kaunarsa. tsura mata mayatattu idanunsa yayi sosai sannan yace " kallon fa? "ina kallonka ne sbd tsabar son da nake maka sai km zance na gaba wannnan soyayyar da kake nuna min batayi yawa ba kuwa? "sbd me kika ce haka? yayi mgnr yana kashe mata idonsa daya hannunsa rike da murfin mota. ta ciza lips dinta na kasa tana me narkar da fuska ala'mun son yin shagwaba sannan tace "ni dai soyayarce ta min yawa ina jin tsoron fa. "tsoro fa kikace ..... ya furta hkn yana narkar da idanunsa cikin kwayar idanunta tare da kamo lip's dinsa na kasa yayita tsotsa yana kallonta . ta daga masa kai ala'mun haka take nufi, itama tana kallon cikin kwayar idanunsa a wannan lokaci tace "ina jin tsoro da fargaba sosai kada wata rana kazo ka juya min baya bansan yadda zanyi ba idan hakan ya faru... "bazan taba juya miki baya ba arayuwata , yanzu saboda kulawa da soyayyar danake baki ce ta sakijin haka? ta girgiza masa kai tare da kashe masa idanta daya . " to meye ne aciki kece fa sauraniyar zuciyata , ni km tmkr bawa ne gareki kinga kuwa dole bawa yabawa sarauniyarsa duk wata kulawar data dace duk abinda nasan zai sakaki farinciki zan miki shi matukar bai fi karfina ba sai abu naga bana son kina min zance juya baya .. .... Ammi ce ta katse mata tinaninta ta hanyar kira sunanta" mamana ki daure nasan abun da kamar wuya ki iya ciresa aranki ,amman ki daure kisawa zuciyarki hakuri duk girman alamari baifi karfin Allah ba kuma muna kan gaya masa . Tasoma yunkurin mikewa zaune ammi tayi saurin kamota ta zaunar daita hade da sanya mata pillow ta bayanta , hawaye ne suka shiga turereniyar fitowa daga kwarnin idanunta mgn take son yi amman ta kasa bude bakinta wanda koda ta bude bakin ma bai zama lallai maganar ta fito ba. dan haka ta jingina bayanta tashiga jan numfashi da kyar tana fitawar tana cigaba da zubda hawayen tausayin kanta. Ummanta ta hado mata tea me kwari ta karaso tare d mika mata cup din tea su'ad ta girgiza kai alamun bazata sha ba. Ammi ta amsa cup din daga hannunta ta kai daidai saitin bakinta "ki bude baki ki sha mamana tunda aka kawoki asibiti bakisa komai acikinki ba, dan Allah ki tausayamana ki duba kiga yadda nida mahaifiyarki muka dawo akan rashin lafiyarki, ki tausayamana muna bukatarki araye idan kika bari wata cutar takamaki akan abdul mu kika cuta sbd shi bai da hasara rayuwarsa zaicigaba yi .. Da kyar da rarrashi ammi tasamu tasha kadan ta kawar da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi mata nauyi kmr an dora mata dotse ,zamewa tayi takoma ta kwanta tana cigaba da tinanin mijinta tare da tsurawa zoben hannuta ido tana ji kmr alokacin yasanya mata shi . Acikin satin mutane kawai ke turereniyar zuwa duba jikin su'ad takowani bangare ciki kuwa har da musty wanda ya dawo kasar loakacin dayasamu labarin abinda ya faru yasha mamakin sosai dashi akacigaba da jinyarta. babu laifi su'ad ta ji sauki sosai sai dai har lokacin doctor saif yaki basu sallama kasancewar baya son rabuwa daita duk da