← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 287 OF 289

Sashe 287

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH YA GHAFUR THE ALL FORGIVING page 90 ....... motar ta d'auki shiru kowanensu da abinda yake tunani acikin zuciyarsa, musty na tsananin mamakin halaiyan abokinsa na rashin da'a "to ko dan an haifeshi cikin turawa ne ya girma cikinsu yasa yake da ikidar rashin girmama mutane matukar ba iyayensa ba.? "shi gbdy lamarinsa na d'aure masa kai bai ta'ba ganin bahagon mutun irinsa ba ,komai cikin zafin rai . shi kuwa ak ji yake kmr ana diga masa ruwan dalma ne a cikin zuciyarsa ,wani irin tuttukin bakinciki ne ke tasomasa from know where yana mamaye ilahirin sansar jikinsa ,a yanxu dayake zaune kokarin cireta daga cikin zuciyarsa yake amman zuciyarsa taki aminta da haka, dan duk inda ya motsa yana jinta acikin tsokar dake makale akirjinsa tana tafiya da bugun zuciyarsa, har suka iso gidan ak bai daina tunanita ba. tun daga harabar gidan yasoma jiyo sautin kukan fitinanun yaransa ,da hanzarisa yashigo parlour'n farhan ne ke jibgar emran kmr Allah ya aikosa akan ball, shi kuma emran sai ihu yake tsallarawa tamkar ana zaran ransa, da sauri ak yakarasa yashiga tsakaninsu tare da kwace ball din da suke kokarin kashe kansu akai ya d'auki emran ,a daidai lokacin da eiman ta fito parlour'n wace fitowarta kenan daga wanka ko kimtsa kanta bata tsaya yi ba ta zira hajibi saboda hayaniyarsu, tsayawa kawai tayi dafe da goshinta ganin uwar gumi da suka had'a duk da sanyi AC parlour'n aranta tace "yaran nan ba dai fitina ba, ita kanta tunda sukazo gidan tarasa sukuni ga barna, da jarabar fad'a barin ma kar farhan yaji labari ,duk yafisu jarabar maseefa da zuciya, gsky uwarsu na kokari . muryarsa a kasalance yace "haba babana meyasa kake cin zalin kanika ?"kai fa big brother ne daga yau kar na sake ganin kayi fad'a da emran ko ihsan, kuka farhan ya fashe dashi tare da cewa "ni ba big brother bane sai dai ko emran. gbdy suka kwashe da dry har eiman shi kuwa ak haushin dake tattare dashi bai barsa ya dara ba yace " shikenan tun da bakason zama big brother babu ruwana da kai, mamana ita tazama big sis ko? da sauri ihsan tashiga girgiza masa kai "allah nima dady banason big sis ni sunana baraka.. wata dryr suka sakeyi sannan suka nemi gurin zama daga musty har ak byn mkr minti talatin eiman tagama shirya dining taxo tagayawa musty "aboki muje muci abinci table ya kammala "kaje kaci kawai babu muhalin abinci acikina, ya karasa fadar hk yana runtse mayatattun idanunsa "dan girman allah ka sausautawa kanka abdul ya fad'a mgnr muryarta a sanyaye "karkayi abinda zaka dawo kana dakasani "wannan fad'an rashin gsky kake kokarin yi. ak ya bude mayatattun idanunsa ya xuba masa "eh man fad'an rashin gsky kakeyi ya zaka daketa sannan ka hanata kuka "musty... ak ya kira sunansa a sayaye "ina jinka "stop tell me all this nonsense. "ni ne nake gaya maka nonsense akan ina fad'a maka gsky to kajira ranar da zan sake maka mgn akan matarka "better yace atakaice sannan ya mike tsaye ransa a bace yana kiran sunan eiman "ke eiman ta fito da sauri "gani yaya "had'o min kayan yaran nan "lfy yaya zaka wuce dasu na d'auka sai sun gama hutu damu? "uhm da nayi tunanin hk amman yanzu na fasa. jikinta a sanyaye ta juya takoma ciki tana tunanin abinda ke damunsa duk kwanakin hk take ganinsa "yanzu dan wannan mganr dana maka shine zaka tafi dasu wai meyasa kake irin hk ne ? "dakata dan Allah malam nace maka akan maganar daka min ne ? "dan Allah karka k'ara min damuwa akan wancce nake ciki . eiman ta sake dawo parlour'n hannunta janye da karamar turolly dinsu, ya tasa yaransa gaba suka bar gidan batare da yayi musu sallama . eiman takaraso kusa da musty da d'an hanzarinta "honey lfy naga yanayin yaya hk? "ina fa lfy tun last week suka samu sa'bani da matarsa nan yashiga koro mata komai daya faru, "ni dai nayi iya bakin kokarina akan lamarin amman abun ya cutura dan itama su'ad din ta hau dokin fushi yakarasa maganar yana soma cin abinci shiru tayi tan tunani "to ko shiyasa take neman layinta shiru . ? tunda ya koma gida ya k'asa zaune ya k'asa tsaye acikin d'akinsa, ya kai gwaro ya kai mari babu abinda ke cin zuciyarsa kmr irin wulakacin da su'ad tayi masa , ranar baiyi isashen bacci ba, ga tsananin ciwon abinda tayi masa ga kuma jarabar kewarta daya addabi ruhinsa,juyi kawai yake akan gado rungume da yaransa ,gbdy tunani yashigayi akan lamarinsa daita , wanda har yake neman tarwatsa masa kwalkwaluwa "wai har shi zata sa a wulakanka ta hanyar kin bada izinin shigowarsa gidansu .. ? "me yasa bazan iya barin rayuwata ba kmr yadda ta bukata ? ya fad'a yana kallon cilling d'akin da mayattun idanunsa wad'an da suka gama kad'awa suka soye tsabar baccin dake cinkinsu . "kana sonta shine dalilin dayasa ka k'asa rabuwa daita" "ina sonta amman bashi zai sa nabarta tayi yadda tagadama ni nake aurenta baita take aurena ba, yaran da ake tashin hankali akansu ya'yana ne why da za'a takurani akansu ya tambayar kansa yana cinza lip's dinsa can ahankali ya motsa labbansa "oh my God.. Allah narokeka ka ciremin son yarinyar nan araina," ka mantar dani lamarinta duk abinda ya dangancita ,kasanya min hakurin rashinta har karfe biyun dare ak na kwance yakasa runtsawa gbdy ki burbushin bacci yaki zuwan masa, wani tunani yazo masa ya yunkura ya tashi ya sauko daga gadonsa ya gyarawa yaransa kwanciya yashiga bathroom ya d'auro alwala yazo ya tayar da sallah nafilfili ya dinga jerawa wanda bazai ce ga adadin wanda yayi ba daga karshe bacci ya d'aukeshi anan inda ya idar da sallah. washegari tun gurin kula da yara yasoma raina kansa da kyar yasamu yayi musu wanka yashiryasu ya kwashesu sukaje gidan abinci sukaci daga nan ya kaisu shopping sannan suka dawo gida, ya k'asa barinsu yaje aiki gashi gbdy sun hargitsa gidan da kayan ciye ciyen daya siyo musu hk wuni ranar zurr yayisa a bautar yaya har dayasani d'auko su yayi daga gidan eiman. dare yayi tunanin uwarsu ya addabi ruhinsa duk yadda yaso yakiceta abun ya tura dan hk ya yarda ya sallama tagama da zuciyarsa, daga safiya har daren duniya a kiran layinta yake karewa amman bai shiga yanxu haka kiran layinta yake akaro na sau ba adadi amman kalma daya ake gaya masa is not respond ya dafe goshinsa dayan hannunsa na saman ruwan cikinsa ahankali ya zamo daga kan kujerar dayake zaune, yaransa gbdy suka zagayeshi suna kuka "dady momy'nmu "ka kai mu gurin momy gbdy abun duniya ya taru yayi masa yawa ya janyosu ya rungumesu gbdy ajikinsa, duk ta inda ya juya babu dadi acikin kwanaki goman da bar gidansa, komai ya tsaya masa cak hatta iskar duniya daya yake shaka baya jinta yadda yake bukata kallo daya zaka masa kasan yana cikin damuwa da tashin hankali . tuni yasoma nadamar abinda ya aikata ,banci hk da yanzu yana tare da matarsa uwar ya'yansa me son farincikinsa, daya yanzu suna tare ko suna hira ko suna kwance acikin bargo daya, ya matse pillow dake rungume akirjinsa "i love you my beautiful wife plz come back to me don't live me, i can't do without you "yanzu na gane sai dake zan iya cigaba da rayuwa amman zuciyarsa na kwabarsa kar yayi saurin zuwa zata dawo da kanta idan tagama fushinta . ammi bata tashi jin abinda ya faru ba sai da lamarin ya kara girmama, dan kimani wata biyu kenan ak bai taka inda su'ad take ba da sunan biko ,haka itama tabangarenta babu wanda yayi kokarin nemansa. eiman tasanarwa ammi dan musty yayi rantsuwar bazai sake tuntu'brsa da zance ba matsawar ba shine yayi masa ba ,ammi nagama jin abinda yayi ,take ta rufeshi da fad'a, ta inda take shiga bata nan take fito ba, "ta yaya zaka hana yara zuwa gurin kakaninsu ? "ni kaina ina bukatar yaran nan su dinga zuwanmana ko da week end amman kabi ka kanai naye komai ,kmr kai kad'ai kayi silar zuwansu duniya ,ai wallahi mamana tayi maseefar birgeni, ya dinga bawa ammi hakuri cause har gurin dady "yace babu ruwansa kuma baihje ko nan da can ba, kar ma wanda ya sake zuwa masa matukar akan zancesa ne, da kyar yasamu ya shawo kan ammi ta amince zata je masa, dan itama cewa tayi bazata je masa bikon matarsa ba ,idan yagaji da zama hk, yaje ya dawo daita da kansa . tare dashi da ammi da yaran gbdy sukaje bawa Umman su'ad hakuri .suka shigo parlour'n da sallama anan suka iske umman su'ad tare da su'ad zaune a parlour'n suna hira tana cin farar k'asa tayi wani irin mugun fari kmr ka ta'bata jini ya fito, sai dai ta d'an rame kad'an, kallo daya yayi mata ya fahimci tana d'auke da shigar cikinsa , dan duk lokacin da kaganta da farar k'asa,to ciki gareta da zarar ta haihu kuma shikenan . cike da girmamawa su'ad ta risina ta gaida ammi tana me Mikewa tsaye yaranta suka isa gareta suka rungumeta gbdynsu suna murnar ganinta ak yabita da wani irin mayataccen kallo har ammi tasoma mgn akan abinda ya kawosu hankalinsa bai jikinsa, tunda ya d'aura idanunsa akanta ya nemi natsuwarsa ya rasa,sai da ammi ta take masa sannan ya dawo haiyacinsa kana ya sunkuyar da kanshi kasa yasoma bawa umma hakuri tare da tabbacin bazai sake maimaita abinda ya faru, bawar Allah ita kam daman bata kulluce shi aranta ba, tuni ta share da abinda ya faru ,da zasu wuce ammi tace ya bar yaran gurin uwarsu suji duminta, bashiri ya barsu dan gudun kar wani sabon tashin hankali ya faru. Umman su'ad tace "a'a aunty ku barshi yaje da yaransa karki matsa masa "ai wallahi bai isa ba haifarsa mukayi bashine ya haifemu ba kuma ko abar masa yaran me zai iya yi musu,"dubi yadda yaran nan suka dawo, idan kuma kin hana abarsu kenan kema baki hakura da abinda ya faru ba , wannan mgnr tasa umman su'ad yin shiru
Chapter 287 · 0% Book details