← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 289

Sashe 59

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mom . suka sa dry gabadaya iman wace ta fito aguje ta rungumeshi tana mishi sannu da zuwa i real miss you bros ya sharfa kanta murnar ganin amminsa bai sa ya lura da zeey bata gidan ba . wani irin farinciki yake hangowa kwance a fuskar amminsa wanda bai taba ganin irin hk atare daita ba . hannushi ammi ta rike sannan ta nufi part dinsa dashi iman na rike da dayan hannushi kallon amminsa yake kawai yana sakar mata murmushi suna isa dakinsa da aka gyara aka zuba komai sabbi yadda aka san yana so da duk sauran abubwan amfaninsa . koina tsab yake adakin tmkr yana kasar komai tsab tsab sai kamshi turaren airfreshiner ke tashi ammi ta shafa sumar kanshi tare sake bashi kiss a goshi kayi wanka ka sauya kaya kasamemu a dining i hav prepare you fevoting food dinka dakafi so tayi mgnr cike da matsanancin farinciki murya ashagwabe yace no..... ammina ki dawo bangaji da kallonki ba ..cike nake da matsanancin kewarki Yanayin yadda yayi mgnr yasa ammi ta dawowa ta zauna kan kujera dake dakin shi km ya zauna daga bakin gado yana rike da hannuta cikin nasa ammI taba umarnin akawo abinci dakinsa dan ta lura bayason tayi nisa dashi ,sosai farinciki y wanzu acikin wannan family daga ammi har dady da Iman anan part dinsa suka kasance suna chapter da murnar ganinsa cikin koshin lfy. tunda ya dawo yaketa son daura idanunshi akan zeey amman bai samu damar hkn ba kasancewar taje ogbomosho. " gabadaya hakurinsa yasoma karewa ya kudiri aniyar dole ne yasamu mafita wa kanshi domin matsanancin soyayyar zeey ta hanashi sakat kowani bugu na zuciyarsa da tarin kaunarta yake tafiya . A yau ne ya yanke shawarar yasamu ammi kawai ya tmbyeta ko zaiji sanyi a cikin ranshi ya fito daga part dinsa jikinsa sanye da wando da riga na farin yadi wanda ya bayyana white singlet dinsa yayinda gabadaya ilahirin jikinsa ke fidda wani sihirtaccen kamshi na fitina da tada hankalin wanda ya shaka . Ahankali yake daga Zara zaran yatsun kafafunsa har yaso part din ammi . A babban parlour'nta ya sameta tana kallo africa magic yaroba ya zauna a kasa gabanta can nesa kadan daita kmr me neman gafara ya fara kame kame uhm am ammi nace ba,wai ina zeey taje ne dan banganta ba tunda na dawo kusan sati kenan km naje gida mama bansamu kowa ba da alamun ma kmr tafiya sukayi yakarasa mgnr kmr wani maroki ammi ta kalleshi Ta gano abinda ke tattare da dan nata Yayi saurin sunkuyar da kanshi yana shafa kwantaccen sumar kansa tare da sosa keyarsa ammi tagama dagon nazarinta akanshi kafin daga baya ta tabe bakinta byn ta numfasa tace yau nake ganin sabon salo . naga dai koda yaushe kuna tare daita awaya ko akan system zakace bata gayamaka inda taje ba zaka wani fito min da sabon salo wai ina zeey take takarasa mgnr cikin fada sbd yanzu wannan halin zakewar da yake nunawa akan Zeey bakaramin haushi da damunta yakeyi ba shi mutun ne da babu ruwansa da zakewa akan komai amman zakewarsa akan zeey yayi yawa .. Ya dan kara sadda kanshi kasa yasoma rarrashin ammi ammi ganin kmr yanayinta ya sauya ammina kiyi hakuri idan na bata miki rai yanayin yadda nake jin zeey din azuciyata ni kaina bansan meke damun zuciyata akan lamarinta ba . tabishi da wani irin kallo me tattare da tsantsar tausayi ahankali ya matso kusa daita yana me daura kansa akan ciyarta yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa yanaganin kmr yayiwa amminsa laifi ne yana ganin duk wautarsa ne dayake nuna zakewersa akan zeey da bata mahimmanci akan komai nan take komai ya sauyawa mata wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyar ammi dan ta dade tana mafarkin wannan rana ta dade tana rokon allah ya dawo mata da d'anta hk ya sake gyara kanshi akan ciyar mahaifiyarsa amminah ki yafe min ko zan samu sausaucin abinda nakeji araina kar zuciyata ta buga ammi....tayi saurin saka hannu ta rufe masa bakinshi batason ma yacigaba da cewa komai tana sharfa sumar kanshi tana jin son danta har cikin bargon zuciyarta wanda a halin yanzu shine danta nmj tilo daya datake dashi ,a yanzu bata da kmr sa . Abdulkabeer ni baka min komai ba yadda kake nuna zakewarka akan zainab fiyye da komai damu kanmu iyayenka shi yafi damun zuciyata bance karka damu daita ba . amman yadda kake kokarin meida kanka tmkr bawanta ne ke damun zuciyata . zeey tasan da zance dawowarka amman takama hanya tabi mahaifiyarta baki har ogbomosho yayinda tasan dole idan ka dawo zaka bukace ganinta. muryarsa a raunane yace ammi kimin addua kullun addua nake maka dana sai dai abun ya fara damuna ,abu nagaba danake son sanar maka abdul kayi aure ina son kayi aure ko kana son mutu banga jikokina ba kullun adduar mata tagari nake maka zainab mace ta gari ce wace ta cancanci kowani da Nmj yasota idan yasameta amman dan allah ka dinga kamanta adalci atsakanin soyayyarta datamu mu iyayenka ne ita km abokiyar rayuwarka ce allah yagani ina sonka da zainab sakamakon kyawawan halaiyenta wanda kowace uwa zatayi alfahari danta yasameta .. Ya dago da mayatattun idanunshi yana kallonta sannan yasaka hannuwansa duk ya rike kunuwansa ammi i promise you i will chage inshaallahu zan rage soyayyar da nake nunawa zainab very soon km zaayi mgnr aurenmu da zainab wanda nasan zakiyi farinciki da hk yakarasa mgnr yana murmushi itama ammi tayi smile tanajin wani irin dadi me tattare da sanyi cikin ranta at the sametime tana tunani azuciyarta dama adduar iyaye bata faduwa kasa banza allah me amsa adduar iyaye ne akan lamarin ya'yansu tagodewa allah daya amsa mata adduarta . Dady yayi sallama yashigo parloun yana kare musu kallo yana hango farincikin dake kwance akan fukar kowanensu shima wit a smile yana godewa allah daya bashi family dinsa da km hada masa kansu guri daya tare da tsantsar kaunar juna wanda yasan wannan soyayyar tasoma asali ne daga salahar matarsa km nagartacciya ahankali yakaraso zuwa inda suke yace ahh ana momy and son soywyyar ce hk nima bari inzo ayi dani shikenan sai yazama lokacin momy dady and son..dukkansu suka kwashe da dry cike da tsansar farinciki mara misaltuwa da kwanciyar hankali ammi takasa hakurin boye farincikinta da rike mgnr bakinta ta mike taje ta rike Hannun dady . dady'nsu albishirinka km dole kabani goron albishiri tana mgn tana murmushi dady yace goro fari tassas. son yace very son zaayi mgnr aurensa da zeey ..zaiyi aure naga yan jikokina yadda take mgnr kmr wata karamar yariya hkn yasa dady tuna lokacin daya aureta alokacin tana tsaka da ganiyar kuruciyarta . kusan duk sanda zatakasance cikin farinciki hk zakaga yanayinta ya koma tmkr na yara shima dady biye mata yayi sunata dry suna mgn yayinda ak kuwa kmr kasa ta tsage ya nutse ciki hk kawai yanzu dayake tare da iyayensa ana zance aurensa yake jin wani irin matsananciyar kunya dan hk ya mike da sauri ya barmusu parloun su dady da ammi sai faman tsokana sukeyi. Byn kwana biyu tsakani zeey ta dawo daga ogbomosho da murnarta ta isa inda ak yake zaune a parlou'n ammi kadan yarage bata rungumeshi ba tsabar farincikin datake ciki shi kam yaso shareta amman ya kasa dan har lokacin asirin bokan na kan dutse nacinsa shi kansa ji yayi kmr yayi hungin dinta. zama tayi kusa dashi ,face dinsa cike da annuri ya kamo hannuta cikin nasa yasoma murzawa ahankali yana kallon face dinta , wani irin shock taji from know where ya tsagar mata a dukkanin ilahirin gabobin jikinta .bashiri ta zame hanuta da sauri ,tare da cewa my life kadawo lfy ..?ya hade Rai sosai yana kallon cikin kwayar idanunta kana muRyarsa a sanayaye yace irin tarbar Da zansamu kenan daga gareki ..? 2yrs Rabonmu da juna shine har zan rike hannunki ki kwace bansan wace iRin mata nake shirin aura ba...... kwata kwata bansa randa zaki waye ba zainab ,gaki nan kmr jinshi mutanen fako . sai randa ka aureni zan waye tayi mgn tana me turo masa baki tare da kafe shi da idanunta tana kallonsa wani irin sihirtacce kyau yayi me tattare da fitina ,Ya dai da wannan kallo kmr zaki cinye ..gara na kalli fuskar rayuwata Bakasan yadda nake jin kaina ba yanzu takarasa mgnr tana murmush ganin yadda ya karkace yana kallonta cike da shaukinta ko ba gayamata tasan abdulkabeer nata ne ita kadai . take suka shiga bayyanawa juna sirrin zuciya da zuciya . basu sukar juna ba har sai lokacin kwanciyya . Sannu ahankali asirin da boka na kan dutse yayiwa ak yasoma barin jikinsa amman ba duka ba. sakamakon adduar da ammi keyi masa babu dare babu rana . har saka manyan malamai tayi suyiwa gudan jininta addua . daman km shi sihiri baya daurewa sai dai kadingayi kana tisawa ,yanzu baya wani nuna rawar kai da zakewa akan zeey lamuran gabansa kawai yakeyi. shiyasa lokacin da ammi ta dameshi akan zance aurensa da zeey ya fututtuke shi ba yanzu ba sai nan gaba matsawar tana sonshi tajirasa zuwa na wani lokaci dan shi yanzu bai tashi yin aure ba . ammi ta rude ta gigice da Jin abinda yace, har da kukanta ina ganin abdul kmr bakada lfy as age dinka yanzu yakamata ace kayi aure . zo yarona zo ka zauna kusa dani kasanarwa amminka idan bakada lfy ne natashi tsaye gurin neman maka mgn ,murmushi yayi kawai sbd ya fuskanci inda mgnrta ta dosa . "take kunyarta ta kamashi ya soso keyarsa yana barin gurin . zainab dake zaune ta kasa kwarkwarar motsi JKinta ya sake yayi sanyi tarasa meke mata dadi ta lura duk kwanakin nan iskanci yake mata . ya daina sonta da rawar jiki akanta . da alamun sai ta sake kaiwa bokanta ziyara . gannin yanayin data shiga yasa ammi saurin matsowa kusa daita tasoma bata hkr .murmushin yake zeey tayi tana me sunkiyar da kanta kasa alamun kunya tasoma wasa da yatsun hannuta kana tace hb ammi ai babu komai . duk lokacin daya tashi duk daidai ne. yauwa diyata diyar albarka shiyasa nake kara sonki akwai hankali
Chapter 59 · 0% Book details