← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 264 OF 289

Sashe 264

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kuka kamar me daga karshe muka fawwalawa Allah komai mukacigaba da rayuwarmu. yayana habib yacigaba da bani kulawa da kuma abinda yashafi fannin kasuwamcin mahaifinmu domin a yanzu shine kan gaba a komai wanda zuwa wannan lokacin arzikin mahaifinmu ya zarta yadda ka tsinci naka arzikin lokacin da kayi lossing momery dinka. a lokacin Allah Allah na dinga yi na kammala karatuna domin na samun damar taimakawa d'anuwa na wanda kullun yake nuna min bazan iya komai acikin lamarin , ni kuma sai na dinga nuna masa zan iya ai duk abinda namiji yayi mace zata iya yin feyye da haka duk lokacin dana fadi haka sai dai yayi murmushi kawai yace "sai dai nayi aure mu taru dani dashi da mijina mu tallafawa dukiyarmu.. nima nace yayi aure domin yafini bukatar haka yaya Habib kyakkyawa ne ajin farko dan har ya zartani a komai hakan yasa yan'mata ke yawon kawo masa farmaki amman sai yaki .. haka na dinga yiwa Habib nacin aure shima yana min naci nayi aure mijina ya tallafawa dukiyata sai dai nayi murmushin nace nafi son shi ya fara a haka har Allah yasa nagama karatuna nasoma taimaka masa . a shekaru uku darasa iyayenmu da mukayi abubuwa dayawa sun faru ciki har da soyayyyar da mukeyi da wani daga cikin ma'aikacin company dinmu wanda hakan yasa muka dan samu matsala da Habib saboda rashin amincewarsa a cewarsa basona yake tsakanin da Allah ba na canza wani nace masa kawai naji . cikin haka na fuskanci habib na tare da matsala saboda alokacin ya rame tsotsai ga yawon tunani da yawon ciwo wanda wani lokacin idan yana tari har aman jini yake nan fa hankalina yatashi mukaje yaga likintasa doctor bai yi min bayanin komai ba yayi adminting dinsa akacigaba da bashi kulawa da daurashi akan magani wanda duk daren duniya nice ke bashi magani kafin na kwanta gaba d'aya na tattara dukkanin hankalina garesa domin bana son narasa shi. "lokaci zuwa lokaci ciwon natashi kuma duk lokacin daya tashi ya dinga tari kenan da aman jini, a wata safiya ne Habib ya tashi da rashin lafiya me karfi wanda yafi duk sauran rashin lafiyar dayake dan wannan karon har da gudaji gudajin aman jini yake. muka isa ga likita dake dubashi akasoma bashi taimako gaugauwa ranar dai na tsare likinta kan lallai sai yayi min bayanin cutar dake damun dan'uwana dayake aman jini cikin bayanan likita dayake min ne naji wai d'an'uwana na dauke da cutar blood cance wanda yanzu cutar takai matakin da sai an zuke jinin jikinsa an sa masa wani sannan zai samu lafiya yacigaba da lallabata rayuwarsa datayi saura dan a halin yanzu bazai wuce shekara daya araye ba zai mutu .... hankalina yayi mugu mugun tashi nayi kuka awa raina zai fita dan lokacin gani nake shikenan ma na rasa d'an'uwa na dinga zagin likinta ina cewa shine zai mutu kafin shekara daya, haka na dawo masa tamakar mahaukaciya sabuwar kamu da kyar aka samu aka shawo kaina da taimakon likitoci komai ya daidaita aka d'aura shi akan sabon magani da zai dinga rage tasirin ciwon ajikinsa "lokacin na nemi likintan dake kula da lafiyarsa akan kar yasanar masa da yana d'auke da ciwon. inda likitan ya tabbatar min da ai ya dade da sani yana d'auke da ciwon dan yana taimakawa kansa sosai gurin zuwa duba lafiyarsa yanzu abinda yasa kikasani dan ciwon ya girmama ajikinsa ne dabazaki sani ba... lokacin da doctor ke mini bayanin yadda rayuwarsa zatakasance ni nake kuka amman shi ko dingon hawaye bai zubar ba "Allah ya sanya masa dauriya d'aukar kaddarar datasameshi acikin ganiyar kuruciyarsa. gashi babu uwa babu uba babu dangin mahaifi sai na uwa suma ba wasu masu yawa ba..... a kullun tsakanina da Habib kar na aure husein nasamu wani ko bayan ransa na aura haka ina jin son husein araina na daina sauraronsa nafi maida hankalina gurin kula da lfyrsa. tashin farkon abinda yazowa zuciyar Habib bai wuce yadda zamuyi da tarin dukiyar da muke da ba, saboda shi oready yasanyawa rayuwarsa yana daf da kabari , abu na farko da muka soma dashi muraba dukiyar mu gida uku kashi daya muyi taimako dashi zuwa kasashen duniya amman mu fara da kasar haihuwar mahaifinmu duk da bamusan asalin daga wani jahar ya fito ba amman muka zabi somawa da kasar kano..... alokacin idan ba ance maka Habib na dauke da cutar cance ba bazaka taba yarda ba, dan irin kulawar danake bashi da taimakon likita yasa cutar kin nunawa a jikinsa kamar farkon kamuwa da ciwon sai dai idan ciwon ya tashi ne zaka tausaya masa sammakon fita haiyacinsa dayake zai ta aman jini gudaji gudaji ni kuma haka zan shiga tashin hankali nayi ta kuka ina masa karatun alqurni me girma har zuwa sanda zai samu lafiya.. yaje kasashen duniya da dama da lalurar ciwon jikinsa sannan ya shirya tafiya Nigeria inda kwarai naso binsa kasar haihuwar mahaifinmu amman ya hanani dole tasa na hakura domin alokacin bana kuskuren sa'bawa umarninsa duk abinda yace haka za'a yi tashin farko daya isa Nigeria a jahar kano jirginsa ya sauka dan haka yasoma abinda ya kaishi ta fanni taimakawa marasa lafiya da marasa galihu da marayu. yaje state ya kai ashirin a yadda yasanar min daga karshe ya zo jahar lagos inda nan ya iskeka rai hannun Allah bakasan inda kanka yake ba ganin farko da Habib yayi maka yaji kashiga ransa ya dade sosai akanka yana kare maka kallo cike da tausayawa alokacin yace bai san sanda ya dinga zubar maka da hawaye ba gashi daganinka an ga mutun me kima da dattako sannan siffarka batayi kama da mutumin daya fito daga gidan banza ba, yasamu likinta kwakwalwar dake kula da kai domin son jin dalilin shigarka wannan halin anan likitan yake gaya masa "kasamu matsalar kwakwalwa momery dinka ce ta ta'bu wanda dole sai an fitar da kai kasar waje sannan zaka iya dawowa daidai idan anyi dace. gashi basu san kowa naka ba tunda aka kawoka babu wani wanda yazo naka take Habib yaji zai d'auki nauyinka amman yasa a sanar a kafafan yad'a labarai domin son binciko danginka. kusan kwanaki goma ana yad'a labarai da hotonka a halin dakake ciki amman ba asamu wanda yasan wani naka ba. "dan haka habib yasanya hannu da taimakon likita ya taho koria da kai inda kai tsaye hospital aka nufa da kai akashiga baka taimakon gaugauwa anan likitoci suka tabbatar mana da kayi lossing memory dinka wanda har ya wuce fahimtarsu amman may be idan ka hadu da abinda zuciyarka tafi bukatar arayuwa ko fuskar wanda zuciyarka take matsananci so zaka iya dawowa tunaninka.. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 264 · 0% Book details