Sashe 271
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* Dedicated To Hauwa A Usman Jiddar YA HAKAM THE MAKER OF IMMUTABLE JUDGEMENTS page 85 ........Ahankali Musty ya zaresa ajikinsa yana dubansa, yayi matukar mamakin irin ramar dayaga Ak din ya sakeyi koma yace ya k'ara lalacewa kamar wanda yayi jinya a d'an kwanakin dayayi bai sanyashi acikin idanunsa ba. " wani irin dad'in farin ciki ke d'awainiya da ruhinsa ya dinga jin kamar ya narke agurin saboda yadda yake ji ajikinsa, wasu hawayen murna yacigaba da zubarwa "me zaicewa Musty arayuwa? "Musty ya gama masa komai arayuwarsa tunda yasamo masa labarin inda bugun zuciyarsa take. ya dinga kallon fuskar Musty yana tsantsar murna a hankali kuma ya dinga murmushi yana hawaye duk atare Musty ya kalleshi yana murmushi, shima farin ciki yake damuwa abokinsa tazo k'arshe zai dawo tamkar yadda yasanshi ada. hannunsa yakamo suka nufi inda zasu shiga jirgi suna magana k'asa k'asa Musty yace "kayi addua friend Allah yasa ba'ayi dogon fushi da kai ba akan abubuwan da suka faru. "Addu'a kullun cikin yinta nake a tun sanda lamarin nan ya faru,in sha Allahu bazatayi fushi da mijinta ba, tasan mijinta na tsananin sonta,tasan da ina cikin haiyacina bazan yi abubuwan duk da akace nayi ba, "nasan zata min uziri bisa ga kyawawan halaiyenta yak'a rasa fadar haka yana cizan lip's dinsa na kasa shi kad'ai yasan yadda yake jin zuciyarsa akanta. Acikin jirgin ma kasa boye murnarsa yayi duk da wasi wasin da zuciyarsa ke yi,sai dai ya karfafa zuciyarsa da zai yi nasara akanta domin wani lokacin idan abubuwa suka daure masa, cikin sauki kuma zasu warware, Allah Allah ya dingayi jirgin ya sauka ya d'aura idanunsa akanta. A natse yake takowa daga matattakalar benen jirgin yana jin wani irin farinciki from know where yana ziyarar ilahirin jikinsa ,koda bai d'aura kwayar idanunsa akanta ba,amman ruhinsa ya samu salama ,saboda jinsa a kasar da bugun zuciyarsa take zaune ciki , ahankali suka soma fitowa daga cikin jirgin har suka karasa saukowa gaba d'aya . kai tsaye inda jerin motocin haya dake jire suka nufa batare da b'ata lokaci ba suka shiga motar direban yajasu. "tafiyar minti talatin ce takawo su unguwar, Ahankali ya fito daga cikin motar bayan direban yagama daidaita parking a k'ofar gidan. yayi shiru yana kallon yanayin tsarin ginin gidan ko ba'a gaya masa ba yasan gidan wani hamshakin me arziki ne, juyowa yayi yana tambayar direban daya kawosu "ka tabbatar da addrees d'in da muka baka kayi amfani dashi? cikin harshensa turancinsa da bai gama k'warewa ba yace "nan ne gidan Alhaji Mahmud tsohon minister al'qallar kasuwanci da gine gine ta kasar Cotonou ............ kai kawai Ak ya jinjina yacigaba kallon tsarin gidan,yayinda Musty ya juya yana sallamar direban "kana mamakin ganin tushen su'ad ko? cewan "Musty Ak yayi shiru yak'i cewa komai sai cizan lip's dinsa na kasa yake yi yana cigaba da kallon gidan ko shugaban k'asa albarka, Musty yaci gaba da magana "a wasu lokuta haka al'marin ubangiji yake ni kaina nayi mamaki ganin muhallinsu koda yake ai biri yayi kama da mutun dan yanayin Umman Su'ad d'in bai nuna daga gidan babu ta fito ba. "rayuwa ce tazo mata a haka tunda Musty yasoma magana baice masa komai ba shima Musty yasan bazai ce komai d'in ba a irin wannan yanayin . kai tsaye gurin securities din bakin get d'in suka nufa suka nemi ayi musu ison shiga cikin gidan cikin minti goma akabawa me gadi umarnin yashigo dasu. A hadadden parlour'n mamma akayi musu masauki cike da girmamawa da mutuntaka ta tar'besu sukayi saurin durkushewa k'asa gabanta suka kwashi gaisuwa dan ko ba'a gaya musu matsayinta agidan ba sun sa itace tsohuwar gidan sakamakon tsantsar kamanninta da Umman su'ad ,domin babu abinda yarabasu sai yanayin girma ,ta amsa gaisuwarsu tana faman tsokanarsu "duk sai naga fuskarku a k'asa acikinku waye angon nawa? Ak wanda har lokacin yake durkushe cikin tsantsar tsoro ko d'agowa ya kasayi a k'arshe ma ya sakeyin k'asa da kansa sosai cike da fargaba,sai dai zuciyarsa dake tsananin bugawa domin son ganin abincin ruhinsa. Gaba d'aya zuciyarsa tak'i samun sukuni da natsuwa babu abinda take muradin gani tamkar matarsa . Musty yayi murmushi sannan ya nuna mata Ak da yatsan hannusa "ga angon naki nan durkushe watakilla ya manta ba'a durkusawa mata ne. atare sukayi murmushi amman banda AK dake kalle kallen ta inda zaiga fitowar sahibarsa.. "lallai kam da ala'mun mantuwa yayi masha Allah da mijin nawa ,na iya zaben miji nagani na fad'a, kodayake nima ba baya ba gurin kyau,watakilla ma shima abinda ya hango kenan ko ango na?? "maza tashi ka zauna kaji kar kafafunka suyi maka ciwo, ka saki jikinka tamkar kana gida, dan naga ala'mun kamar ka tsorata da ganina suka sake yin wata dariyar suna dubansa. shi dai Ak still bai ce dasu komai ba baya ga shafan bayan keyarsa dayayi ala'mun jin kunya. Musty ya d'an saci kallonsa "wannan itace rana ta farko dayaga wannan tsigar tajin kunya atattare dashi ,sam shi mutun ne mara kunya mara jin tsoro me dakakkiyar zuciya akan komai. " lallai mamma tasamu darajar me girma da diyarta ta kasa samu agurin sirikin nata. Ahankali ma'aikatan gidan suka shiga kai kawo a tsakanin kitchen da cikin parlour'n ,an shirya dining table d'in dake can gefe guda nau'in abinci da abin sha ne iri iri wanda daman ka idar gidan kenan, basa yin abinci kala daya sannan basa yin abinci kad'an saboda basu rabo da baki. mik'ewa tsaye mamma tayi ahankali tare da cewa kuci abinci yanzu zan turo muku ita, Ak yayi saurin cewa" uhm dan Allah karki ce mata mune, Mamma ta dakata da tafiyar data soma tare da yin murmushi irin nasu na manya kana tace "saboda me? yayi raurau da idanu sannan ya marairaice muryar tamkar wani maraya " idan tasan nine may be bazata fito ba.............. ta d'aga masa hannu tare da cewa "karka damu zata fito sannan ta juya taci gaba da tafiya ta nufi b'angaren da su'ad d'in take. tunda mamma tabar gurin ya kasa samun sukuni da natsuwar zuciya ,zuciyarsa cike take fal da fargaba " bazai iya cin komai ba ahalin yanzu, duk da tarin yunwar dayake tare da ita har sai ya daura idanunsa akanta, ita kadai zuciyarsa ke buk'atar da kwad'ayin son gani. idar da sallarta kenan ta mik'e tsaye tana ninke pray mat mamma tashigo d'akin bakinta dauke da sallama ta amsa tana me fad'ad'a fara'arta tare da cewa "yar tsohuwar nan ba kya tsufa wallahi kullun sai k'ara kyau kike ta fadi hakan ne sakamakon shigar dake jikin tsohuwar doguwar riga ce har k'asa sai dai ta nad'e kanta da bakin mayafin jallabiyar, d'an tsufa mamma ta tsufa sai dai tsabar jin dadin datake samu daga ya'yanta ya hana tsufan bayyana. "kema kiyi adduar samun irin tsufana ko ma fiyye dana nawa, tsufa irin wannan yana da matukar wuyar samu a wannan lokacin amman idan mutun yana bukatar tsufansa yayi kyau abu na farko shine rike ibada tare da kiyaye hakokin ubangiji da yiwa miji da iyaye biyayya a ganiyar kuruciya shi ke sa tsufan mutun yayi kyau.. "kin idar da sallar ne ko kuwa Yanzu zakiyi? "na idar Mamma wani abun zan miki? "babu abinda zaki min muje parlour'n kinyi baki daga nigeria, a matuk'ar tsorace su'ad tace "nayi baki fa kikace mamma? mamma tace "eh " su'ad tayi shiru tana tunani bak'in da tayi dan gaba d'aya bata kawowa zuciyarta mijinta ne yazo gurinta ba, tunda tun zuwansu ammi jikinta yaba ya dade dasanin in datake ,zuwa ne dai bazai yi yaga halin datake ciki ba. ta tsurawa mamma ido jikinta a matukar sanyaye tace " dan Allah mamma ki gayan min su waye sukazo? "dan bakiji yadda zuciyata ta d'auki rawa ba.. a zuciyar mamma tace "dole jikinki ya sauya zuciyarki ta d'auki rawa, makusancin rayuwarki ne yazo gareki amman azahirance cewa tayi "muje kiga ko su waye, atare suka shigo parlour'n, tsoro taji sosai har gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa da ganin mutanen da batayi especting ganinsu ba, a daidai wannan lokacin . aranta tace "gaskiya mamma ta shamaceni dayawa dan wallahi datasan shine yaxo bazata fito ba. sai dai ta wani bangaren take zuciyarta tashiga murna da oyoyon ganin burin ranta uban ya'yanta zuciyarta ce ta tsanata bugawa tsabar fargaba domin batasan dame yazo mata ba "Tsaye tayi aguri kamar wace aka dasata tsabar tashin hankali yayinda wasu hawayen murna da tashin hankali sukayi nasarar biyo fuskarta, tana k'ok'ari sharesu,abubuwa guda uku suka had'e mata alokaci d'aya, Ak ya tsura mata mayatattu idanunsa kyam yana kallonta kyawun data k'ara ya wuce yadda ya dinga kiyastawa aransa,sakamakon yanayin gidan dayaga tana rayuwa aciki. "komai ya canza atare da ita har yar k'iba tayi, me yiwuwa ko dan albarkan cikin jikinta ne yasa takara kyau na musamman ya fad'i haka aransa. ita kuwa su'ad gaba d'aya ta rikice tarasa halin datake ciki ,ahankali ta d'auke kanta daga garesu Musty ne yasoma magana yace "su'ad ki zauna mana kinyi tsaye shiru ga abokina yazo taka nas domin yabada hak'urin abinda ya faru sannan ayi sulhu da juna. mamma tace "jaira kuka me kikayi hk kmr wace aka aikowa da mutuwa byn murna yakamata kiyi? "In kuma kinfasa aura ne ni inso sai inbishi mutafi can muyi zaman mu ke kuma sai ki zauna da tsohu dan nakula kinfi sonshi, gaba d'aya akasa dariya, sannan ta bar falon domin basu guri. dan girma Allah su'ad ki tausaya ki zauna ba'a son mace me juna biyu na doguwar tsayuwa irin hk ,ki taimaka idan wani abu yasameki abokina zai shiga damuwa.. sai lokacin ta d'ago fararen ta kalli Musty amman Ak taki yarda su sake had'a idanu dashi cigaba da tsayuwarta tayi tare da goge hawayenta shi kuwa Ak ya kasa kwakwarar motsi agurin duk wani hali data tsinci kanta ciki a yanzu ya rigada ya gane yana jin tamkar yakarasa gareta ya durkusa bisa gwiwowinsa ya tausasa muryasa yabata hak'uri tare da kalmomi da zasu kwantar mata da hankali. Musty ya lura sosai da halin rudanin da zuciyar amininsa take ciki akan matarsa,sai dai ya share batare daya sake karanbanin furta wata kalmaba dan ya lura gbdy haushin amininsa ya shafeshi. ya mik'e