Sashe 220
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
bai runsaba haka su'ad duk inda yayi tana binsa tana kuka da kokarin kamoshi jikinta . Hankalinta yayi k'ololuwa tashi takoma kamar wata zararra hawayen majina duk sun wanke mata fuska gashin kanta ya watse ya baje cikin k'ank'anin lokaci tafita haiyacinta koma kamar wata mahaukaciya. Kuka take wiwi tana bin AK duk inda yasa k'afa tana faman cewa. "Abdul " meke damunka ? "dan Allah kagaya min idan wani abu nayi maka nabaka hakuri sbd banason ganinka cikin damuwa takai hannu zata tab'a shi yayi saurin buge hannunta ya sake wurin zama sam baya k'aunar tarabe shi . a halin yanzu idan AK na k'aunar mutuwan shi to yana k'aunar su'ad tarabe shi. Daf da asuba AK zaune abakin gado ya zuba uban tagumi Zee kawai yake tunani hade da buk'atar son ganinta. A hankali su'ad ta lallabo tafad'a saman k'irjin shi a matuk'ar zabure AK ya mik'e yayi cilli da su'ad jikake k'ummmm muryarsa cike da hargagi yace "kina hauka ne ko kin sha wani abu ne? jikinta na rawa ta sauko daga kan gadon ta durkusa gabansa ta kamo kafafnsa "dan Allah mijina farincikina duniyata karka tsiro min da abinda zuciyata bazata iya dauka ba idan ka nemi nisanta kanka dani komai na iya faruwa dani.. ko bi takanta AK beyi ba, su'ad wace ta buga goshinta a jikin gado zunbur ta mik'e dafe da goshi domin tabugu sosai har wurin yatashi amma bata bi ta jinkita ba taci gaba da bin AK sukaci gaba da zagaye d'akin. Haka suka kwana babu wanda ya runtsa shida ita har gari yawaye. Gari nawayewa AK ya hau shirya kayansa tsab ya dauko passport dinsu yasoma shirya musu tafiya zuwa gida nageria. acikin jirgi kuwa zama ne akayi shi babu ruwan wani da wani tmkr wasu kurame suka dawo sabanin lokacin da zasu baro Nigeria suna manne da juna tare da nuna tsantsar kulawa . yanzu kam kallo daya zakawa fuskokinsu kagane cewar suna cikin damuwa me tattare da tashin hankali kowanensu da abunda ke damun zuciyarsa sai dai damuwar su'ad ta ninka ta AK dan tun da suka baro kasar spain kuka take har sanda jirginsu ya lula samarin samaniyya shi kuwa ko ajikinsa asalima toshe kunnuwansa yayi da earpiece. misalin karfe shida daidai na safiyar laraba jirginsu ya sauka a murtala international airport . mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE