Sashe 94
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH _alhamdullahi zuciyar bagudo hauwa A usman jiddarh ina matukar farinciki tayaki murnar kammala wannan mashahurin kayataccen daddaden labarin naki me suna gadar zare...... gadar zare labari ne zai ilimantar fadakarta ya wazantar da ul'uma sannan ya nishadarta, hakika kinyi namijin kokari sosai acikin wannan labarin naki sannan kin taka wargani domin kin xo da wani salon rubutu wanda ba duk writer ce zata iya kawo abubuwan masu mahimmanci da kika tattara acikin wannan labari me cike da darasi iri iri ,na jin jinamiki zuciyata na sake jin jinamiki zuciyar bagudo you are besty writer of the year ,Allah ya kara baseera da karfin ido _ _qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam: la tabagaduw, wala takhasaduw,wala tadabaruw, wala taqatha'u ,wa kunu ibadallahi ikwanan_ _Allah Messenger saw :said do not harbour grudge against one another nor jealousy nor enmity and not show ur backs to one another and become as fellow brothers_ page 36 adduar ake takoina sbd yadda abubuwan suke sake tabarbarewa. amman babu wani sausauci acikin lamarin. kullun abun sai gaba yake. yana sake tabarbarewa duk abinda suka taba matsawar da hannusu ne take zai narke ya lallace. idan business suka soma yanzu ne kudin zai narke a nema komai arasa . a wani zuwa ne da mahaifina yayi garin yaga yadda suka koma abin tausayi, yasa aka budewa abbakar katanfarin commpines wanda za'a dinga yin kayan masarufi shi km aliyu companies cement shi da sani,. duk wani abinda dayakamata a aiwatar dangin mayan injina an zubashi a ma'aikatun duka ,har an soma neman work's. acikin sati biyu da kammala komai na company . aka samu matsala domin atsakar daren ranar talata wacce tayi daidai da sati uku da bude companies din . wata iska tazagaye kanfanunnunka daga baya sai gobara ta kama da duk wani kayan da'aka xuba ciki . dun sun kone kumarsu. wani irin ci wutan take ta ban mamaki kmr ba wutan duniya ba duk yawan mutane dake kokarin ganin wutar ta mutu amman hkn yaki yiwuwa hatta masu kashe wuta kasa kasheta suka dole hk aka zubawa gurin idanu. sannan hk wutar ta dinga ci har byn kwana biyu sannan ta mutu dan kanta. idan kudi ne ma hk zai tsiyace ya lalace ya tanbade ahannunsu batare da sunyi abun arziki ba har sai sun dawo suna karya murya tmkr yadda masu ma'ula kanyi ko mabarata. abinda ke ciwa hjy babba tuwa akwarya kenan. na wannan iftila'in daya samun ya'yanta ,wani lokacin hk zata zauna da tsufanta ta tasa ya'yan agaba tana kuka tana rokon Allah yakawo mata saukin lamarin . tunda yanzu har takai takawo abinda za'a ci ma agidajensu babu. tallafawarsu gabadaya ta koma kan dawood da sauran matan wanda wani lokacin idan hjy babba na kuka suke rarrashinta da kwantar mata da hknli.wanda dole tasa kullun suna kan hanyar gidan domin kwantar mata da hnkl. yayinda duk wannan bakin asirin da harira ke bankawa bai shafi mahaifina ba dan shi kmr ma kara bunkasa dikiyarsa ake dan hk koda yaushe acikin taimawa yan'uwansa yake tun kafin su tmbayeshi zai basu hk kawan abinci yadda ake ajiyewa agidansa hk yake aika musu ,wannan abun ke sa hjy babba dan rage damuwar dake damunta tayi sanya masa albarka. byn shekara uku asarin da harira tayiwa yan dakin hjy babba yasoma karyewa yana komawa kanta . domin dukiyar datayi asirin akansu duk sunkare tasss babu abinda ya saura . sai yakasancewa an soma taba nata dukiyar data ya'yanta dake gidan miji . nan fa hknlinta yayi mugun tashi. domin sauran yaranta ma data aurar byn mutuwar marigayi haka dinga sakosu acewar mazajensu masu kafar tsiya ne dan tunda suka auresu suke asarar dukiya kasancewar guda uku daga cikin ya'yan data aurar duk masu mata suka aura nan jama'a suka soma rade radin a gari ai dukiyar da akabar musu ce take konewa killa ma alhj yasif uba na madugu ba kudin Allah da annabi bane kudinsa dan yawan dukiyarsa ace ace abin didiginta, hk dai maganganu mutane sukayita yawo acikin gari. kowa da abinda yake cewa akan lamarin. wasu suce ba hk bane ba kudin jini bane jarabawa ce yayinda wasu marasa fahimata da imani suce sam kudin jini ne . rayuwa fa tasoma sauyawa hjy harira duk abinda ta shuka daki daki suka dinga dawowa kanta da ya'yanta ,tashiga cikin matsanancin maseefa fiyye wanda hjy babba tashiga abaya . tayi bakinciki wannan maseefar data sameta .. tayi kuka tayi juyi da ihu duk ita kadai adakinta babu wanda zata zauna dashi ta tautauna damuwarta dan ko ya'yanta tasanawar da abinda tayi yasa suka tsinci kansu cikin wannan hali tsine mata zasuyi. dan gbdy ya'yan hjy yusif uba na madugu kansu ahade yake kowane bai son laifin dan uwansa . rayuwa kenan wani sakamakon tun aduniya akeyinsa duk dukiyar da take bin bokaye akansu babu hk kazalika nata ma babu sai dai dan abunda bazarasa ba rayuwa tayiwa harira tsananin ga km halin damuwar da yaranta mata ke ciki tarasa mafuta abun yana matukar damunta fiyye da tunanin duk wani mahaluki. tana daga kwance akan kujera tunani barkatai sai zuwa mata suke cikin zuciyarta ta rasa lalubo mafuta. bata ankara ba sai taji saukar hawaye daga cikin gurbin idanuwanta, tabbas wannan shine kaikayi koma kam mashekiya, tayi abu yaxo yasha mata kai . da tasani keya ce inji hausawa. byn hannuta ta sanya tana goge hawayenta dake fitowa daga cikin kwarnin idanunta. faruwan hk yayi daidai da shigowar daya daga cikin yaranta cikin parlour tana hango hawayen dake fita daga cikin idanun mahaifiyarsu tayi wani tsalle takaraso gun datake kwance akan kujera tayi durkuso agabanta ta kamo hannayenta a rude take mata mgn hjy hjy meke faruwa dake hk duk kwanakin nan hk nake ganin cikin damuwa da tashin hankali idan ma wani abu ne yakamata ki sanarmana ba wai ki zauna kina asarar hawayenki ba . tayi mata mgnr da harshen yaren Cotonou wato agumanci ,hjy harira ta kalli diyarta dake zaune agida yanzu tana zawarci ga yaron ciki, tace babu komai jannat . jannat tayi saurin girgiza kai tare da cewa ban yarda ba wlh akwai dai abinda kike boye mana. babu yadda za'ayi ki dinga zama kina kuka kullun idan ma wannan maseefar data afko mana ce ai ba mu kadai bane kina kallo su yaya tsawon shekaru uku sukayi suna cikin wannan jarabawar me sukayi baya ga hkr . har gashi sannu ahankali sun soma dawowa daidai . hjy harira tai shiru tana zance zuci duk lokacin data kallesu suna bala'i bata tausayin... jannat ta katse uwar ta hanyar cewa ko bakijin dadi ne a sanarwa yaya dawood ? hjy harira tayi shiru still taki cewa komai jannat ta bala'i rudewa sakamakon rashin yi mata mgn datayi ..bata ankara ba sai ga hawaye suna fita daga cikin idanunta . da sauri hjy harira ta tmbyeta kukan me kike yi ? ya zama dole nayi kuka sakamakon halin danaga kin tsinci kanki acikin kinki fada mana abinda ke damunki muna matukar kaunarki a raye bama son rasaki. hjy harira ta dan yi murmushin karfin hali tare da girgiza kai tace kada wannan abun ya dameki bana jin dadin zuciyata ne . amman yanzu komai ya wuce diyarta. jannat tayi murmushi tare da cewa wai har naji dadi ta km yi mata murmshi tace kije ki dauki abinciki gaya can kici yana kitchen . tana fita daga dakin harira ta mike ta fara zariya acikin dakin ta kai gwaro ta kai mari. tasanya hannuta na hagu tana dan dukan goshinta dashi ,tabbas na tafka babban kuskuren ni ko me janyo min nayi yayan mijina asiri hk ? ya zama dole na koma gun boka domin akarya min wannan asirin. gashi nazo nayi abinda ya daneni inda asirin zai tsaya iya kansu ne ai da sauki . take anan tayi niyyar komawa gurin boka gobe goben nan domin akarya asirin dataiwa ya'yan mijinta dan ko ya'yanta bata son suji abinda tayi wallahi tasan a yadda suke ji da yan'uwansu sai sun gujeta . da wannan shawarar da zuciyarta tabata washegari da misalin karfe goma na safiya tayi shiri bata zame koina ba sai kauyen da boka yake amman abin tashin hankali koda ta isa ta iske boka ya mutu harira najin abinda wata tsohuwa ke sanar mata cewar boka ya mutu ai bata san sanda ta salale akan gwiwowinta ba ta daura hannuta duka a saman kanta ta rusa wani giggitaccen kuka. wayyohhly ni harari naga ta kaina ya zanyi da wannan bala'i boka ya mutu ya barni cikin bala'i. nan dai taci kukanta tagaji ,ganin kukan bazai mata ba yasanta tashi tabar gurin ta nufo hanyar dawowa gida. duk jikinta a mace tmkr wacce bata da laka gbdy cikin kwana biyun nan tai zuru zuru hk ma duka ya'yanta tasasu atashin hnkli har na gidan miji da zawarawan da suka fito .duk sun fita haiyacinsu ganin halin da mahaifiyarmu ke ciki. kuka suka zauna suna mata hkn ke sanya itama ta zauna tana kukan nadama. ta km yin wata shawarar data sake zuwa gurin wani bokan domin taga ko za'adace hkn kuwa tai shirin xuwa gurin wani hatsabibin boka dataji labarinsa cewar aikinsa sha yanxu magani yanzu. hjy harira zaune gaban boka tana koro masa bayani abinda take son yayi mata. bokan da kanshi ya jinjina wannan lamarin mugunta irin nata . yace gsky al'amarin da akwai wuya acikinsa, domin ko cikin dayan biyu nan, ayi daya, koki dauki yaranki uku ki jefasu cikin ruwa me gudana ko km acikin tsohowar rijiya da km kanki zaki aikata hkn sannan asirin ya karye. matukar ba hk kikayi ba keda arziki sai dai a lahira .. hjy harira nagama jin abinda boka ya fada ta fashe da kukan munfarci tana rokonsa ya taimaka da wani sihirin amman banda wannan dan bazata iya jefa danta daya cikin rijiya ba balle har uku. take boka yace matsalar baki aikata hkn ba ina tabbacin wannan sihirin ba zai taba karyewa ba. dole sai kinje kin jefa yaranki uku acikin rijiya ko rafi. hk hjy harira ta koma gida tana kuka hk dai abin duniya ya dameta . yayinda cikin ikon Allah da karfin adduar da hjy babba keyi