Sashe 136
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hatsarin dake tattare da aikin ... jikina na rawa na bar gurin malamin tafiyar awa ukuce ta kawo cikin garin lagos ,kai tsaye hospital din da aka kwantar dashi na nufa cikin matsanancin sauri . ina isa hospital daidai step muka ci karo da yarinyar jiya zata sauko muka gaisa daita, tana sake min godiya . "muryata a sanyaye nace mata babu komai ya jikin yaya faisal din? tayi murmushi tare da cewa da sauki amman ba sunansa faisal ba abdulkabir sunansa ..... ohhhh ai jiya ne naji kmr kina ihun kiran sunan faisal da sunan mahaifiyarku da mahaifinku uhmmm.. me naji kince? na daga idanuna sama ala'mun son tunawa can nace yauwa asiya da mahruf na fadi hk tare da saurin waskewa. yarinyar data tsinci kaina cikin jin faduwar gaba sakamakon jin sautin muryarta ,tayi zugun tana kallona ,nasan tunani take akan nacika tmby. "dan hk nayi saurin katse mata tunaninta ta hanyar cewa kiyi hkr na cika tmby ko? murmushi sake yi sannan tace "no babu komai, wato hk na gigice jiya ina ta zuba sambatu gsky rudewa ce kawai amman duk ba hk sunan iyayenmu suke ba, mahaifiyarmu sunanta baraka wace muke kira da ammi ,mahaifinmu km adam sunansa muna kiransa da dady. "ayya gsky jiya kin gigice dayawa kina fadar abubuwa ni zan wuce ki gaida dady da ammi har da yaya abdulkabir, Allah ya bashi lfy. "tace ameen cikin hanzari na juya zan wuce naji sautin muryarta bazaki leka kiga yadda jikinsa yayi ba? na juya ahankali nace "sauri nake wallahi amman zan dawo wani lokaci na duba jikinsa , ok idan badamuwa muje na rage miki hanya . tare muka jero har zuwa bakin motar jiya da muka kawo shi hospital ta bude motar tashiga ta zauna, nima na bude dayan bangaren nashiga na zauna ,har tayiwa motar key wayarta ta dauki kara, ta dauka tayi mgn "tare da cewa ok gani nan xuwa ,ta dube gefen inda nake zaune zugun tace dan Allah kiyi hkr ana kirana,amman yanzu zan dawo . "kaiki damu ta fita ta barni cikin motar tare da kunna min AC 'n motar. fitarta ke da wuya kmr ance na juya bayan motar, idanuna ya sauka akan littafin dana gani shekaran jiya , hanuna na rawa na kai na dauka ina kallonsa kmr ranar farko dana soma ganinsa ahankali na bude cikin littafin wanda naga a shafin farko an rubuta littafin sirri ....... na meida murfin littafin na rufe ina duban ainihin bangon litttafin, rubutun jiki na kurawa ido sosai amman bangane abinda ke rubuce ba kasancewar ba da harshen turanci aka rubuta ba, ba km da French ba, ina tunanin ko da wani irin yare ne wannan akayi rubutun dashi, na hango tahowar yarinyar nayi saurin tura littafin cikin hijabina na boye na sake tattaro natsuwa na sanyawa jikina, dan karta gane wani abu, tana gama karasowa ta bude ta shigo cikin motar "tace yi hakuri dan Allah na barki zaune ke kadai ? "nayi murmushi tare da cewa babu komai ai ,ta tada motar muka bar harabar hospital . muna kaiwa *fadeyi* kafin mu karasa *o'nipan* nace anan zan sauka taja burki gefen titi tayi parking na sauka tana sake min godiya, sunanta nake son tmbyrta amman karta ga kmr nacika tmby yasa na share ,na rufe mata murfin motar taja tayi gaba, ni km nakarasa inda zan samu motar me zuwa unguwarmu. washegari ma haka na shirya da niyyar zuwa school na wuce *idiroko* byn na isa gidan alhj tapa na gaya masa sunansa dana iyayensa sannan yayi duba cikin fara kasar dake gabansa ya tabbatar da sunan ne nagaya masa ,sannan yasoma min bayani kmr hk za'a yi aiki amman me karfi ,cikin biyu ki zabi daya zaki tare anan tsawon wata daya dodon tsafi zai dinga kwana dake, ko km me a miki tsafi sannan wannan ciwon zai bar jikinsa. byn ya warke sai ya aureki .. kafin ayi aiki na biyu akwai sharadin me karfi ,matsawar bai aureki ba ciwon zai iya dawowa jikinki . "sannan ko kin aure wani bazaki taba haihuwa dashi arayuwarki ba matsawar bashi wannan abdulkabir din kika aura ba. "sannan duk ranar da kika kuskura kika gayawa wani wannan sirri kece silar nemo masa mgn , shima ciwon zai iya dawo kanki . "akwai tukunyar tsafin da zanbaki wanda zaki dauka akanki idan dare ya raba,sai ki samu hanyar data rabu gida uku ki ajiye wannan tukunyar tsafin, byn kin ambaci sunansa dana iyayensa sai ki saka wannan maganin a tsakiyar bakinki, ki juyawa tukunyar tsafin baya. " karki kuskura ki juya bayanki idan kin ajiye tukunyar tsafin sannan karki kuskura kiyi kowa magana ,duk wanda yayi miki mgn karki tanka masa domin akwai matsala idan kika amsa kowace irin murya ce zaki sallawantar da rayuwarki. "sbd amsawarki tana daidai da rugewar rayuwarki gbdy domin zaki dawo wata bake ba zaki dawo rikakkiyar yar daba me shaye shaye duk abinda ya danganci maye sai kin sha shi, banda fashi da makama. nayi shr kawai ina kallonsa sbd narasa abinda zance masa yayinda tsoro da firgice suka farmami xuciyata da ilahirin jikina, naji araina bazan iya wannan kasadar ba.. mutumin da zanyi wannan aikin sai da rai akansa bai san ni ba bai san koni wacece ba yanzu idan nazo nagama taimakawa rayuwarsa yace bazai aureni ba meye makomar rayuwata? nayiwa kaina tmbyr take zuciyata tayi rauni magangun ore suka dinga xuwa min 1 byn 1 ahankali hawaye suka cicciko idanuna na sake tsare alhj tapa da idanuna sannan na motsa labbana nasoma mgn cikin sanyi murya, "gsky aikin nan akwai hatsarin bazan iya sai da raina ba ....... "a she kuwa zaki yawo tsira ra ai duk wanda yaji yanayin tsarin aikinmu da ka'idarsa dole yayi ko km ya koma tsince tsince a bola... nayi saurin zaro idanuna waje daidai da hawayen idanuna sun samu nasarar gangarowa bisa kuncina . muryata a matukar tsorace "nace hauka kake nufin zanyi matsawar ban yarda ba? "tubaran kuwa domin sai kin zama mahaukaciya karfi da yaji me yaga kayan jikinta tana yawo tsirara haihuwar uwarta .. hankalinsa ya kai kololuwar gurin tashi jikina ya dauki rawa dan hk ina gama jin bayaninsa nacigaba da kukana ina dana sanin shigar da kaina cikin tashin hankali danayi. ganin bani da wata mafita ko dabara yasa na amince da zabi na biyu wato daukar tukunyar tsafi dan bazan iya bari mutumin yasadu dani ba. ina zauna ya hada min ruwan magani nasoma wanka dashi tun agindansa sannan yabani wata yar karamar tukunya dake cike makil da kayan tsafi an tsiyaya manja acikin tunkuyar. ahankali ya sake min bayani duk yadda zanyi na amsa na nufo gida. tun a hanya zuciyata tabani shawarar nayi wa mahaifiya amfani da maganin bacci ta yadda zn samu damar fita cikin dare,take na amince da shawarar da xuciyata ta bani. na tsaya wani pharmacy na siyi panador night . ina shiga gidanmu nasamu waje karkashin step na boye tukunyar maganin sannan nashiga part dinmu inda na iske ummana zaune tana kallon TV nayi mata sannu da gida sannan nakarasa uwar daka nayi wanka na kimtsa zuciyata na wani irin bugu. dadare byn nagama girki na hadawa ummana cucumber just na saka mata maganin baccin ciki na kawo mata abinci da cucumber just din dana hadata mata. gama cin abincinta ke da wuya bacci yayi gaba daita akan kujerar datake zaune akai. ni km ganin tayi bacci yasa na tasheta xuwa uwar daka ta kwanta nima kwanciyar nayi zuciyata cike da tunani iri iri da fargaba.. misalin karfe biyun dare na tashi dan dama banyi bacci ba, na sauya kaya zuwa doguwar riga da dan guntun hijabina na dauki takalmina sadaf sadaf zan fita har na kai bakin kofar fita, na tsaya ina jin yadda kirjina ke tsananta bugawa.na dawo da baya ahankali na isa inda ummana ke kwance kmr ta mutu na dan duka nayi kissing dinta sannan na sake juyawa na bar gidan gbdy. a matukar firgice nake tafiya cikin wannan daren sbd rashin sabo domin ban taba tsintar rayuwata acikin wannan yanayin ba, byn school da islamiyya bana zuwa koina da zarar na dawo gida bana sake fita sai wata goben . sannu ahankali na kawo hanyar data rabu gida uku na ajiye tukunyar tsafin ,na tsuguna gaban tukunyar tsafin nayi kirarin sunan abdulkabir dana iyayensa sosai kmr yadda alhj tapa ya koyar dani ,sannan na juyo nasoma tafiya zuwa hanyar komawata gida cikin rashin sa'a har naci rabin tafiya nasoma jin sautin muryar mutane ana ihu tare da sautin gudu ,a she police ne suka biyo barayi wani irin mahaukacin tsoro da firgice ne ya mamaye ilahirin jikina. take km jikina yasoma rawa naki juyawa nacigaba da tafiya cike da dauriyar xuciya, cikin hk naga barayin sun kwaso aguje sai gashi munci karo dasu gbdy na rude na gigice sbd jin yadda suke harbi ,police na meida musu da martani . "a matukar tsorace nasoma neman hanyar tsira batare dana juya ba amman hkn yaki samuwa sbd jin sautin police danayi ta bayana suna futar you are under'arest ,all of you drop your gun nan fa na sake gigicewa da shiga matsanancin tashin hankali ,jikina ya sake daukar rawa nayi saurin fita ciki barayin zuwa gefe guda na tsaya jikina nacigaba da kirrma. inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi nashiga furtawa ina sake maimaitawa ,da bindiga naga wani police yana min nuni na koma cikinsu . "bakina na rawa nace ai batare muke dasu ba, ban ma sansu ba yau shine rana ta farko dana taba ganinsu ni nazo kawo... short up police ya buga min tsawa nan fa na sake rudewa na daura hannuna bisa kaina ina kuka ina cewa wallahi batare muke dasu ba. ganin hk yasa daya daga cikin barayin kwashewa da wata uwar dry sannan yacewa police din yasani tare muke fitar dare dasu. aiko ina jin hk nan na zube kasa bisa gwiwowina na kara sautin kukana ina rantsuwa akan bana cikinsu ,amman hk police suka hadeni dasu muka koma zuwa hanyar dana ajiye tukunyar tsafin, wanda sai lokacin na tuna da sharadin da alhj tapa yace min . kuka nake sosai har sanda muka isa (area g) police station aka