← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 289

Sashe 127

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aje azo mata dani zata amshi cikin jikina wayyohhly Allah ..meyasa na hanashi auren muradin ransa..? gashi yanzu na rasa d'ana da jikokina da diyata yanxu bani da komai sai cikin jikin yarinyar nan dana hanashi aurenta . dan Allah kuje kuzo min daita ina son cikin jikinta "kuje ku amso min jinin d'ana taufeek hk ta dinga sabatu tana kuka ranar kwana sukayi a hospital sbd rikicewar datayi. yace min yaso gaya musu inda nake amman yace sai ya nemi izinina kafin yasanar musu da komai . yana kai wa karshen mgnrsa . "nace kar ya kuskura yasanar musu da inda nake sbd su'ad diyace ni kaidai bata da wani dangin uwa balle uba nice komai nata a duniya da lahira. "yace meyasa zan fadi hk? "nace masa bisa abubuwa dayawa amman bari kaji kadan daga cikin dalilaina. " duk mutumin dayace bai sonka baxai taba sonka ba har duniya ta nade , sannan yanzu rashin d'anta da jikokinta datayi ne yasa take bukatarmu arayuwarta . lyace salema kiyi hkr ki tausaya rayuwar hjy kodan kada duniya ta sheganta min yarinya , ki bar yarinya ta taso cikin danginta. "ni ko nace sam bazan taba mikaki ba duk runtse duk wuya ina tare dake. babu yadda doctor rak bai so yayi comfuse dina ba amman naki yarda duk ta inda biyo nima sai na bullo masa da nawa dalilin, daga karshe yace na zauna nayi nazari sosai akan mgnr. sannan yacigaba da bani labarin" salemat ki godewa Allah masoyinki yasamu sheidar arxiki takowani bangare mahaifiyarsa da danginsa har ma mutane gari abin sai yabaki mamaki . wajen zaman makoki ma hk jama'a sukai ta zuwa wani mutun yazo yana kuka yace asirinsa ya tuno shekaru sama da biyar kenan taufeek ne ke dauke da cinsa dana ya'yansa da nauyin karatun ya'yansa. hk ma wani mutun shima yazo ya kawo kudi kimanin dubu dari yace taufeek ne yabashi jari ya dinga juyawa yasamu abin ciyar da family dinsa. koda aka duba diray dinsa aka ga sunan mutumin amman shi kyauta yabasa hk makarantu islamiya da masallatai suka dinga fadar irin taimakon dayake musu abin ni kaina sai da yabani mamaki sbd bai taba sanar min ba. kuka nake sosai lokacin dayake sanar min amman km naji dadin aikin alkhari dayayi arayuwarsa. watana daya cif a hospital din Doctor rak aka sallamomu muka dawo gida, duk a karkashin kulawar dr rak duk wani abun amfani dana bukata ya tsiya mana. "sosai yake bamu kulawa tare da bata lokacinasa tare dake wani lokacin yayi kuka wani lokacin km naga yana kallonki yana murmushi. airin tashin hankali da hjy ta riski kanta ciki, ciwon zuciya yayi nasarar kamata yayinda hawan jininta ya tashi zanga zanga sugar'nta ya hau sosai babu abinda take furtawa sai kuzo min da yarinyar da taufeek yayiwa ciki wallahi ina son cikin da yarinyar zata haifa . ku taimaka ku kawo min ita tun ban mutu ba ,nan fa likitoci suka ce ayi mata abinda take so idan ba hk ba za'a iya rasata. nan fa hankalin yan'uwa yayi mugun tashi aka baza nemana duk kasar da taufeek ya rubuta acikin diary dinsa muje tare dashi, babu wanda basu je nemana ba amman basu samu nasarar ganina ba . daga karshe har kasata Cotonou sukaje da taimako address din gidanmu dake rubuce acikin diary dinsa . nan ma sabon tashin hankali suka riska domin an tabbatar musu da banzo ba, hk suka dawo jiki a sanyaye. ko lokacin sai da doctor rak ya tasani gaba da magiyar na taimakawa rayuwar hjy kar ta mutu nabari ya bayyana ni garesu ,na saka masa kuka wiwi "nace bai kaunata bai jin tausayina na sake tabbatar masa koda taufeek din ne zai dawo duniya bazan bashi diyata ya kaiwa hjy ba, ballantana baya raye, ka manta lokacin da nake kuka da idanuna ina tokonta akan ta tausaya min tabari d'anta ya aureni ,amman taki babu abinda taufeek baiyi ba dan ganin ta amince da aurenmu ta zubawa zuciyarta rashin imani amman shine yanzu zaka dinga son tillasa zuciyata akan nata muradin. "wallahi wallahi doctor rak ko duk duniyar nan gatan hjy ne ko sama da kasa zasu hade ko mutuwa hjy zatayi sai da ta mutu amman ina tabbatar maka idanunta bazasu taba ganin diyata su'ad ba ,nasan su'ad jinin d'anta ce amman ta haramta gareta . "banki idan su'ad din ce taso ganin danginta ba. shima ina tabbatar maka sai na kawar da tunaninta akansu. jikin hjy yayi tsamari sosai zuwa lokacin zuciyar har tasoma kunbura idanunta sun kunbura sai an kwantar sai an tayar, hnklin yan'uwa dana diyarta data rage mata a duniya ,ya sake tashi babu abinda take iya cewa sai akawo min saleema da cikin jikinta ..... dan girman ku kawo min cikin jikin salema ina son.. wallahi matsawar banganta ba mutuwa zanyi, zan mutu, karku bari na mutu banga salema ba da cikin jikinta ba. dr rak kuwa tunda ya damka min documents din gidajen da taufeek ya siya da sunana ,na gujeshi sbd lura danayi yana son tillastani akan kaiwa hjy ke, alhalin bazan iya ba dake ba . dan hk na baro wancan tsohon gidan namu na dawo nan nacigaba da rayuwata ina baki kulawar data dace sauran gidajen na zuba yan haya da taimakon lawyer sa, domin amfanin da kudin gurin taimakawa rayuwarmu ni dake. lokacin da taufeek ya kai shekara 4 cif da rasuwa itama hjy tace ga garinku byn doguwar jinyar datayi agida da hospital ,ta rasu batare da burinta na ganina da abinda na haifa ba . lokacin da kika shekara biyar na hadu da hasan a kasuwar oshodi ,naje yi miki tsiyar kayan sallah, ban ganshi ba sai shi ne ya fara ganeni . naji dadi sake ganinsa danayi, shine fa na kawosa gidana yaga inda nake ko alokacin sai daya tmbyi taufeek nagaya masa komai har labarina, yayi mugun tausaya min dan har kuka yayi, daga nan wannan lokacin mukashiga zumunci dashi . har wata rana dayazo nake nace masa yayi aure man zama hk babu dadi . "yace min ai yana da mata agarinsu har da yara guda biyu ,amman dai yana son yin aure anan amman tunanin kudin haya yake yi. dan bashi da karfin kama haya. take nace masa kar ya damu da gurin zama idan yasamu mata yayi aurensa ga flat nan abaya yazo ya tare da amaryarsa yaji dadi sosai yashiga yi min godiya . nan fa yayi aurensa tun daman akwai wace yake so iyayenta sun dameshi da zance aure rashin gurin zama ne yasa yaki meida hankali. da dabara na tura hasan zuwa garinmu domin binciko min yadda dangina suke rayuwa byn babu ni . watansa biyu acikin kasar cotonou ya dawo min da labari iri iri wani naji dadin faruwarsa wani km kuka yasani sosai. "mkr labarin mutuwar hjy babba dana dangina wayanda suka cigaba da rayuwarsu suka manta dani. har number gaddafi yayana hasan yazo min dashi, wai ana yawan turosa Nigeria aiki a medical hospital din dake cikin sam . abinda yasani jin dadi km labarin hjy harira da take tsaka da hauka tuburan acikin garin zugu har da tsince tsince abula tana tonawa kanta asirin abinda ta aikata , wanda hkn ne yayi sanadiyar yayyena duka ukun suka saki jikokinta, sannan dayawa daga cikin ya'yanta dake gidan miji aka sako mata su . zaman mu lfy da hasan da matarsa wad'anda ke tsananin mu biyayya, "wani lokaci Hasan yake bani shawarar nayi aure, amman nace masa babu mgnr aure araina . shi kuwa wani sabon auren ya kara ,tarewar amaryar bai fi da wata uku ba akayi wani mummunar hatsarin kwantaina akan bridge din oju elaigba. kwntaina ta fado akan motocin dake kasan titi har da mutane yayinda hasan yakasance daya daga cikinsu .hk aka zomana da gawar hasan jina jina,domin ko wanka bayi masa ba sallah kawai akayi masa aka kaisa makwancinsa. wayan nan matan guda biyu na cikin flat din baya duk matan hasan ne shiyasa duk lokacin da kikace a koresu daga gidan nan suna zaginki suna miki habaici nake sharewa da zance bawai dan zagin da suke miki bai damuna ba. sbd suna cin darajar abu daya hasan ..sannan tun tasowarki kin bude ido kingansu ne acikin gidan nan, shi kasan hasan kun shaku dashi sosai fiyye da tunaninki yana sonki yana baki kulawa. ,kin taso cikin kulawa da farinciki, uwa uba natsuwa da hankali duk wanda yaganki yana sonki da son mu'amula dake, har lokacin dakika gama secondry school dinki. shigarki jami'a da shekara daya komai naki yasoma dagulewa daga karshe naga kin dawo min wani iri. tun daga wannan lokacin na riski rayuwarki cikin shaye shaye da fadace fadade da jama'a wanda ada bakya yi. "km tun a wannan lokaci nayi bankwana da farinciki har zuwa yanxu danake baki labari.... lokacin da ummun su'ad takawo karshen labarinta ita kuka su'ad kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani cikin uwa da "ya" su'ad ta mike tsaye jikinta a matukar sanyaye tana cigaba da kukanta har da shesheka. kenan zargin mutane unguwarsu akanta ya tabbata gsky ne ita din shegiyace yar gaba da fatiha .... abinda tafi tsana da kyamata kenan arayuwata ,shi akayi akasameni . wayyohlly Allah nah... ta fadi hk a bayyane tare da daura hannuta duka bisa kanta wani irin kuka me taba zuciya ta saki. umma ta karaso gareta itama kuka take ta rungumeta kiyi hkr diyata karki dajeni dan kinji abinda muka aikata da mahaifinki, babanki mutumin kirki ne kaddara ce tasa muka same miki ta hanyar da batadace ba, ba dan zuciyarmu yaso hkn ba . "ki tausayi min diyata karki juya min baya, kece duniyata, rungume umna su'ad tayi ajikinta sosai muryarta na rawa "tace ba zan taba gudunki ba umma ,duk duniya banida kmrki kice kika samar dani duk da bata hanyar dace ba amman bazan iya gudunki ba sbd kaddarar data fada miki ni kaina na tausaya miki ummana ,labarinki ya taba min zuciya sosai . "da najin labarinki kafin zuwan wannan lokacin da banyi riskin din rayuwata ba. umma da ban saka kaina cikin wannan mummunar rayuwar dana tsinci kaina ciki ba. "naji taikaicin naji bakincikin ta hanyar danaxo duniya amman bai kai tsanar
Chapter 127 · 0% Book details