Sashe 74
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
niyyar nocking sai ta dauke. , da kyar dai tasamu ta sanyawa jikinta jarumta tayi nocking kmr batasonyi... me gadin gidan ne ya mike tsaye tare da budewa yana dubanta. , ina wuni baba. lfy lau yarinya ,ya amsa mata cikin sakin fuska, dan Allah baba ko abdulkabir na gida? eh yana gida. idan da hali dan Allah baba inason nashigo akwai abinda yakawoni gurinsa . yasan da zuwan naki ne? tayi Shiru tana tunanin abinda zatace ,har sai da baba ya sake maimaita tmbyrsa ,sannan tace eh yasan da zuwana . baba me gadi yakarasa bude mata get tare da bata hanya shigowa. kalle Kallen farfajiyar gidan take. ahankali tasoma tunani ta inda zata soma ganinsa batasan inda zata dosa ba . ganin yadda take zare idanuwa yasa baba me gadi yace ta biyo shi har bakin kofar part dinsa ya kaita yana nuna mata kofar shiga . sannan ya juya zuwa bakin aikinsa. ahankali ta kai hannu jikin kofar zatayi nocking sai km wani tunani yazo mata . ta murda handle din kofar taji kofar ta bude sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, sannan tasanya kanta ciki hadadden parlour'n wanda yakawatu da kayan more rayuwar duniya, wani irin kamashi airfreshiner ne yasoma kaiwa hancinta ziyara ,wanda kadan ya rage naumfashin bai tsaya ba. , ga sanyi ac dake ratsa gbdy ilahirin jikinta . komai na parlour me kyau ne kmr yadda mammalakin keda tsananin kyau. kallon parlour take kirjinta na dukan uku uku zuciyarta na harbawa da sauri sauri. ahankali tasamu guri ta zauna akan kujera dake parlour tana fargaban haduwarta dashi. kwance yake ruf da ciki acikin akan makeken bed dinsa , daga shi sai gajeren wando short niker iya cinya da whit singlet yana opereting system . hk kawai ya tsinci kanshi da jin mummunar faduwar gaba...... sakamakon wani sauyi dayaji ajikinsa da hancinsa . gbdy ji yayi cent din gidan ya sauya masa. wani irin kamshi yake ji wanda yakasa tantancewa. dan hk , ahankali ya ture system din dake gabansa gefe tare da saukowa daga kan bed .yana mike hade da salati ala'mun gajiya. ahankali ya bude kofar bedroom dinsa ..kmr a mafarki yaganta zaune ta daura kafarta daya kan daya tana jijigawa ahankali ahankali idanunta akan wani tangamemen hotonsa dake manne da bango parlour'n . jikinta ne yabata duk inda akayi yana gurin ,dan hk ahankali tasoma jiyo da fuskarta har ta sauke fararen idanunta akan kyakkyawan fuskarsa, me dauke da annurin kyau. , atare gabansu ya fadi suna kallon juna kafin daga bisani ta mike tsaye a firgice tana cigaba da kallonsa, tundaga sama har kasa. kyakkwa ne ajin farko na bugawa ajarida, me tattare da siffar karfi ,duk inda ka kalla ajinsa kwance yake luf luf da kwantaccen gashi . wanda ke sake bayyanar da tsansar kyawun surar jikin da Allah yayi masa. hatta zara zaran yatsun kafarsa dana hannuwansa kwance suke luf da gashi . shi din irin mazajan nan ne abin bukata da muradin kowace mace . sannan samun irinsu ke da matukar wahala,gbdy shock ya hanasa motsawa daga inda yake tsaye, jiyake tmkr an shafe masa ganinsa ne abubuwanta sun daina daure masa kai, sun koma bashi tsoro yarinya tmkr aljana duk inda yayi tana like, ganin irin kallon kurrila datake masa ne yasanyashi saurin kallon jikinsa, sannan ya meida mayattun idanunsa akanta yana watsa mata wani matsiyacin kallo me hade da harara... muryarsa a matukar harzuke yace me yakawoki km... ?meyasa jakanci da rashin zuciya yayi miki yawa ? yama akayi kika shigo gidan nan .. ? kayi hkr na kasa jure rashin ganinka ne akalla yau kwana biyu kenan bansaka cikin idanuna ba, duk hanyar dana san zanga ka kulleta abdulkabir .. yaya kake son nayi da rayuwata ..? Kayarda Dani wallahi ni masoyiyarkace . wace yarda zanyi dake, yarda dake ko abin kunya Allah yakiyayeni da yarda da mace irinki ,yan kwanaki ne yarage a daura min aure da natsatsiya mata kamilalliya, wace tasan kima daraja da mutuncin kanta ba irinki ba taxi ...... ya janyo hannuta afusace yayi hanyar waje daita ,tare da ingizata harabar gidan ya juya da sauri yashige ciki part dinsa ya danno kofar da karfin grammmmmm kake ji yasanya key ,tare da jinginar da bayansa da jikin kofar yana sauke numfashi sama sama. da mugun gudu su'ad takaraso jikin kofar tana bugawa da karfi hade ihun kiran sunansa abdulkabir..... abdulkabir...... Please open the door for me don't do this to me ... Nocking take da iyakacin karfinta tana ihun kiran sunansa Amman yayi mata banza. wani irin juyi tayi tare da Tabaro jikin kofar tana surutai wallah Banza yarda ba kajawota mata maseefa da bala'i me tsanani agurina . sai na azabtar da ma kowacece zatayi gangancin aurenka da azaba mafi tsanani. wlh baka isa ka aure wata kabarni ba matsawar ina numfashi. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE