Sashe 241
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
za'a jimu dake .. "Bama za'ajimu ba wannan cin da kamin yau kamar zaka kasheni ai dole nayi takatsantsan da gidan dadinka tabashi amsa da hakan sannan suka rabu . suna rabuwa da akil, taja tsaki d'an iska kawai ai baka isa ka hanani abinda nagadama ba, jikina kuwa yanzu nasoma rabawa gayu su mora nima na moresu, haka kawai zaka takura rayuwarta, ko ba dan abinda boka yace ba zan bawa duk wanda nasan zanji dadi jikina ya mora, tana tuki take wannan surutan sannan kuma tana kokarin neman number sadik bayan ya dauka ta tmbyeshi "yana ina yanzu"yace shi ai tunda takirasa ya bar ma'aiikata" tace ka dawo yanxu ina son ganinka daxu bakai zan kira ba mistake n .. katseta yayi "kinga madam bafa zan sake dawo da kaina cikin halaka ba, alhalin nasan abinda ni dake muke a ikatawa yasa'bawa shari'a muslinci," tunda kin furta haka da bakinki gara kowa yakama gabansa ,gara ko iskancin zanyi naje nayi da wace ba matar aure ba, yana kaiwa nan yakatse kiran ta sake neman layinsa cike da matsanancin mamaki ita yake gayawa haka ko giyar kudin datake tura masa ne ya fara haukatashi ,har manta da wace yake magana. yana d'auka tace " kai dan ubanka kazo yanzu office kasameni. ,"wannan kuma umarnin zance da ne," Zainab yakira sunanta naga fa kina neman takurawa rayuwa idan baki barni sali'n alin ba zan fallasaki kowa yasan abinda kikeyi yakarasa fadar hk yana kashe wayarsa gbdy ma ya zare laying ya wurgar akan titi yacigaba tafiyarsa yana jan tsaki. zuciyarta ta girgiza kwarai akan magangun yaron ,dan hk bata sake yunkurin nemansa ba tacigaba diriving duk da ta damu dashi sosai. dan yana matukar d'ebe mata kewa a office duk lokacin da bukatarta ta motsa, to yanzu yata iya ai dole tabarshi kamar yadda yace karya fallasawa duniya ita. tunda tasan tana da masu maye mata gurbinsa ko a yanzu tagadamar samun madadinsa huda goma tasan zatasamu dan haka tasharesa tacigaba da abubuwanta kullun tana tare da akill dinta ko Williams idan kuma taga wanda ya biya mata rai koda tsomon Lipton ne zai mata zata bashi kanta ya dai yi kar asirinta akan abdul yayi sanyi . ******** zaune su'ad take akan gadon ammi tana cin farar kasa eiman tashigo dakin, ta zauna kusa daita tare da cewa "sammin tunda kika fara cin abin nan take biya min yau dai sai naji yadda take, su'ad ta mika mata gutun dayayi saura a hannuta, eimn ta amsa tana murmushin sannan ta saka cikin bakinta taji gardin gishiri gishiri "tace kai kece abun fa yana dadi sosai. su'ad ta ta'be baki "ina wani dadi a nan . "ai kuwa da dadi may be ma ita ce ta sake gyara miki jiki ,su'ad ta d'an kalleta batare da tace komai ba. "eh mana matar yaya kalli fa yadda kika dawo kinga kyaun da kikayi kuwa kamar ba me laulayin ciki ba sai dan ramar itama nasan rashin yayana ne a kusa koda yaushe ,su'ad tayi murmushin karfin hali batare da tace mata komai ba har sanda tagama tsokanar ta ajiye sauran farar kasar data kasa cinyewa ta fita sakamakon kiranta da ammi tayi. "kamar ba me laulayi ba ta furta abinda eiman tace cikin ranta ,ina eiman bazaki fahimta ba ni kadai nasan yadda nake ji ajikinta. kamar yadda sir mahbub yace zaizo yaga jikin su'ad hakan ce takasance yanzu haka zaune yake abayan motarsa direbansa na jansa ahankali ,gaba da bayansa duk motacin escort dinsa ke biye dashi. kafin su iso unguwar yasoma kokarin neman layin AK wanda lokacin yake zaune makale da zeey ita kuma sai faman zuba masa shagwaba take iri iri tana narkemasa tare da ta'ba masa inda tasan yafi saurin hawa network, kira sir mahbub yashigo wayarsa wannan shine karo na sau ba adadi da'ake kiran wayar da kyar yasamu ya zame zeey ajikinsa ya d'auki wayar yana dubawa ganin sunan dayaga yana yawo a screen din wayar ne ya d'an sashi sosa keyarsa ,sannan ya d'auka cike da girmamawa bangare sir mahbub kuwa yana jin ya dvauka yace" gani a hanyar gidanku ,kana kusa dai ko? "ok ganin nan zuwa yanzu sannan ya ajiye wayar tare da cewa "my zeey zan d'an fita amman yanzu zan dawo. "ina zaka kuma da yammanci nan? kiyi hkr ya sunkuyo tare da kissing din wuyarta "sir mahbub ne ke son ganina yanzu ,kawai ya tsinci kanshi da kin gaya mata gaskiya ,zamewa tayi daga jikinsa tana kissing din kirjinsa sannan ya bar gidan . yana fita takira william's sakamakon jinta datayi cikin wani yanayi batare da bata lokaci ba yashigo har cikin kuryar dakinta tana ganinsa ta taso da sauri ta rungumeshi ajikinta tana kissing dinsa shima bayi sanya a gwiwa ba yashiga meida mata da martani nan suka shiga shashacinsu. ******** can kuwa gidansu ammi zaune suke har umman su'ad data kawo musu ziyara. su'ad na kwance tana fama da kanta dan har lokacin laulayi take komai tace sai ta mayar dashi baya zama acikinta gashi duk nesan abu matsawar takafa ranta shi zataci idan bataci ba sai taji kamar duk cutar duniya kanta ta dawo kuma zuwa wani lokaci bata iya cin komai ba gashi laulayin ya hade mata da tinani mijinta hakan yasa ta dashe ta rame sai fari da dagon hanci idan kuwa ta fara kakarin amai kamar zata mutu dan har hawayen tausayi ammi ke zubar mata tashi tayi zaune daga kwanciyar datayi sakamakon wani abincin yan ghana dataji ya biya mata rai . batayi magana ba suka da cigaba da hira da mahaifiyarta har gurin biyar ta mike zata wuce su'ad dake zaune gefen ammi tace"ummana .... "ya'akayi diyar ummanta? su'ad tayi murmushn jin dadi wanda yaushe rabon datayi irinsa. "ummana ina son naci *banku* banku abincin mutane ghana ne sai dai mafi akasarin mutanen conotou togo lumay da sauran kasashensu can suka ficinsa ,sabani akasarmu ta hausa fulani ,asalinsa da rogo akeyinsa. "umman su'ad tayi murmushi sannan tace "karki damu yanzu zanje na siyo miki na kuma dawo da kaina nayi miki. "yauwa ummana nagode sosai ta juya zata fita a daidai lokacin da motocin sir mahbub suka tsaya kai kofar gidansu ak. ammi takirata "salema yanzu ina zakije neman *mori* ? "ana siyarwa a wacan jection din can da zaka fadeyi "ok idan haka ne bari na tura hannuta taje ta tsiyo yanzu ta dawo ke kuma kije ki daura ruwa daza'ayi amfani dashi . murmushi umma tayi sannan tace "ai ba'a daura ruwa , asalin molin ake damawa tare da agulma, sai azuba masa ruwa a d'aura akan wuta ayita juya shi har sai yayi danko. ammi tace " to... ikon Allah amman abincin kasarku ne ko? "dan banta'ba jin sunansa ba sai yau abakinku, suka sa dariya gbdynsu har su'ad. " to gashi kinji sunansa yau kuma jikanki ne zai ci inji cewar eiman . "aiko nagodewa Allah ai nafiso yasaka diyata cin abinci sosai su'ad najin haka ta mike tsam tashige dakin ta kwanta tabarsu suka cigaba tautaunawa akan yadda ake sarrafa moli yazama banku har sanda taji dawowar hannutu haka kawai su'ad dake kwance a daki taji gabanta na faduwa haka ummanta kirjinta ke dokawa sai dai ta'ajiye hakan amatsayin abinda tasaba ji akoda yaushe dan wani lokacin haka zataji gabanta na faduwa . shigowar hannutu da kmr minti biyu sannan ak yakaraso kofar gidan ya fito cikin sauri ya isa motar dayasan sir mahbub yake ciki escout dinsa dake tsaye jikin kofar yayi saurin bude murfin motar inda sir mahbub ya ziro kafafunsa ya fito suka jera zuwa cikin gidan suna magana kasa kasa har suka sanyo kai da niyyar shiga part din ammi shima sir mahbub haka ya tsinci kanshi da jin mummunar faduwar gaba, adaidai wannan lokacin umman su'ad ta amshe bakar ledar hannu hannutu tasoma kokarin shiga kitchen suna gama shigowa cikin parlour'n umman su'ad na karasa shigewa... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE